Garin Dadi 19

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Garin Dadi 19


©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
_(Home of expert & perfect Writers)_

 

*GARIN DAÆŠI………!*

 

_*NA*_

*_UMMI A’ISHA_*

 

*Wattpad:ummishatu*

 

19

*Ina kuke manyan mata Æ´an Æ™walisa ma’abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haÉ—aÉ—É—un Lagos lace wanda zaku iya samun É—inkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaÉ“inki, gefe É—aya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUÆŠI GIDA…..*

~~~Jin abinda nace yasa shi yin murmushi kafin ya É—auke idonsa daga kaina yana kallon wani wuri, zuba masa ido nayi ina kallonsa, sai yanzu na san inda asalin kyau yake, ada ina yiwa Hashim kallon kyakkyawa sai yanzu na gane ashe nayi kuskure a baya domin ga inda asalin kyawun yake wurin samz dan hatta Æ™wayar idonsa kaÉ—ai mai mutuÆ™ar É—aukar hankali ce, idanuwan nasa gaba É—aya kuwa sexy eyes gareshi ma’abota kyau da sanya shauÆ™i, shi dai ba fari bane haka kuma ba za asa shi sahun baÆ™aÆ™e ba, ganin zai juyo gare ni yasa ni saurin É—auke idona daga kansa,

“Mommy na ke son in auri Felicia….. Duk da a karon farko ni na ganta ina so amma daga baya sai na ji ta fita daga raina…. Amma ita mahaifiyata har gobe tana son in aure ta nikuma na faÉ—a mata ba zan iya auren ta ba….” sai lokacin na É—aga idona na kalle shi jin abin da yace,

” To amma me yasa ka fara sonta a karon farko daga baya kuma ka sauya ra’ayinka?”

” Da farko tabbas nine na ganta ina sonta kuma har na faÉ—a mata muka fara soyayya na kai ta gidanmu na gabatar da ita sai daga baya na gane ba matar aure na bace….”

“Me yasa ta zama ba matar aurenka ba?” na sake tambayarsa har lokacin idona na kansa,

“Lesbian ce….”

“Ya aka yi ka sani?”

Murmushi naga yayi sannan ya sunkuyar da kansa ƙasa ya ɗago yana kallo na,

“baby kin san wani abu? Zaki yi kyau da Barrister” murmushi nayi nima na bashi amsa da,

“to ai brothers É—ina gaba É—aya da elder sister É—ina lawyers ne…… Mu 3 ne kaÉ—ai muka saki layi”

“ke ai computer guru ce…”

“ka fini iyawa ai…. Baka bani amsar tambaya ta ba”

“uhmmmmm…… Muna tare da ita sai na fara noticing wasu abubuwa atare da ita…. Sai inga pics na mata a phone É—inta daga Æ™arshe bakina da nata ta faÉ—a min tana yi kuma wai gaskiya bata jin zata daina sai dai muyi aure a haka…. Har fa wani state É—in take tafiya yawo wurin mace, ba zan iya auren macen da take aikata irin wannan abun ba ”

Nidai har ga Allah ban taɓa sanin akwai masu hankali a addinin su samz ba kamar haka,

” Wannan shi ne dalilin da yasa ka rabu da ita? ”

” Shine kaÉ—ai dalili…… Bana son mace mai bin maza ko mata ”

” Kai baka yi? ” na tambaye shi dan kore zargi domin inata wasi wasin ko yana neman mata ko baya yi ko yana shan giya ko ba yayi,

“What?” Shima ya buÆ™ata,

“Dan Allah kar ka É—auki magana ta da wata manufa…. Kana shan giya ko baka sha sannan kana kula mata ko baka yi?”

Shiru naga yayi ya zuba min ido wanda har sai da naji ina ma banyi masa tambayar ba araina dan ta yuyu ko ta É“ata masa rai,

“kayi haÆ™uri idan har tambayata ta É“ata maka rai….”

“No baby….. Baki É“ata min rai ba kawai dai ina farin cikin samun kamilar mace ne…. Ban taÉ“a kula matan banza ba kuma ba na shan giya….”

Ajiyar zuciya na sauke jin amsar da ta fito daga bakin sa, hannunshi na kalla da har lokacin ke rike da nawa,

“ka sakar min hannu mana….”

“am sorry…..” ya fada ba tare da ya saki É—in ba,

“I want to kiss you…….” wani mugun kallo na yi nasa sannan na fincike hannuwana na miÆ™e ina gyara mayafin kaina, afusace na kai hannu zan É—auki handbag É—ina amma yayi saurin riÆ™eta,

“Haba baby me nayi? Kiyi haÆ™uri”

“ohh tambaya ta ma kake yi abin da kayi? Ai ban san wannan shi ne dalilin da yasa ka É—auko ni ka kawoni nan ba, yanzun nan ka gama faÉ—a min wai kai baka bin matan banza ashe you are a professional liar”

“am very sorry….. Ba abin da nake nufi ba kenan”

“Ka bani handbag É—ina zan tafi”

“am sorry baby, ki zauna mu Æ™arasa magana….. Ba zan sake ba pls forgive me, i won’t misbehave again i beg” ya Æ™arasa maganar yana haÉ—e hannuwansa wuri guda alamar roÆ™o da neman afuwa, tsaye nayi kawai ni ban tafi ba kuma ban zauna ba, miÆ™ewa tsaye shima yayi yana kallo na, ni kam nabi na haÉ—e rai na tamke girar sama da Æ™asa kamar ban taÉ“a dariya ba,

“am soo sorry baby…..” ya sake faÉ—a yana riÆ™o hannuna, zama nayi ba tare da na kalleshi ba,

“pls smile…. Ki daina fushi haka”

Shiru ne ya É—an ratsa kamar na minti biyu kafin naji yace,

“baby how old are you?” É—an kallonsa nayi muka haÉ—a ido dan shi É—inma ni yake kallo,

“kai zaka fara faÉ—ar naka….”

“amma ai ni na fara tambaya”

“uhmmmm” na É—aga masa kai,

“ok, well…. Am 34 going to 35 nan da 4 months”

“ashe ma ka tsufa” na faÉ—a cikin tsokana amma sai na fuske kamar maganar ba daga bakina ta fito ba,

“dagaske na tsufa? Zan so mu raba tsufan tare” ya faÉ—a yana murmushi,nima murmushin nayi,

“Daga nan idan angama training ina zaki tafi? Kano?”

“no, Abuja zan koma ta can zan wuce Kano”

“Ok, zan ganki a Abuja É—in before ki tafi”

“babu problem”

“amma idan kika koma gida zan rinÆ™a samun ganin ki? Ba zan iya 2 weeks ban ganki ba” ya faÉ—a cikin langaÉ“ar da kai alamun ban tausayi kuma dagaske ya ban tausayin dan na fahimci da gasken gaske yake sona ssÉ“anin ni da nake son sa sama sama amma shi son da yake yimin irin na do or die ne,

“Karka damu zaka rinÆ™a ganina duk lokacin da ka so….”

“Naji daÉ—in haka…”

Mun jima sosai muna hira yana bani labarai daban daban wadanda wasu sun shafi rayuwarsa, har ɗan bakin ruwan nan ya rakani za ayi min hoto, takalma na na cire na sa ƙafa ta guda ɗaya tamkar wadda aka jonawa lantarki haka naji an fisgoni ga wani uban shock dake neman jana cikin ruwan ai babu shiri na riƙoshi bama ƙaramar riƙewa ba dan ƙanƙameshi nayi na rufe idona gam ni kaina ban san ina tsoron ruwa ba har haka sai yau dan har kaina ya soma juyawa ina jin jiri yana ɗaukana kamar zan faɗi kawai hango girma da yawan ruwan nake yi, ashe daga nesa ne yake burge ni yanzu kuma da na zo kusa dashi sai naji ya tada min da hankali, kasa tafiya nayi sai rawa da jikina ke yi kamar ana kaɗa min mazari idanuwa na a rufe gam, ganin kamar bana cikin hayyacina ya sashi sunkuyawa ya ɗaukeni kamar wata baby zuwa gefen ruwan, ni kam ban ma san ya ɗaukenin ba sai ƙara ƙanƙameshi da nayi kamar rayuwa ta tana manne dashi, tsawon mintuna biyar ban dawo cikin hayyacina ba, a hankali na fara buɗe idanuwa na ina salati har na buɗesu gaba ɗaya akanshi dake durƙushe yana riƙe dani,

“Am sorry baby na kawoki wurin da bakya so”

Girgiza kai nayi ina Æ™okarin raba jikina da nasa, “Karka damu ina son wurin… Kawai dai ban taÉ“a shiga ruwa bane”

“Kar ki damu next time idan mun dawo zaki shiga kuma ba zaki ji tsoro ba….. Ni ina son ruwa sosai dan har swimming nake yi”

Zaro ido nayi ina kallonsa kafin na miÆ™e “nikam duk ranar da na shiga ina jin mutuwa zanyi dan tsoro nake….”

“Babu abin da zai sameki ai tare zamu shiga and i will stay by your side….” duk da ya faÉ—i haka ji nake kamar ba zan iya ba nikam, fara tafiya nayi na barshi nan durÆ™ushe yana kallo na Æ™afa ta babu takalmi, wurin da takalman mu suke na nufa na saka nawa na rataya handbag É—ina ina jiran sa yazo mu tafi, sai da ya gama É—aukata a hotuna ni ban san yana yi ba sannan ya taso yasa takalminsa tare da riÆ™o hannu na, kallonsa nayi alamar tuhuma amma sai ya É—auke kai ya fara tafiya yana jana nan nabi bayan sa, da yake magrib ta yi saura Æ™iris shiyasa wurin yayi wahalar abun hawa dan bamu samu drop ba sai taxi É—in da ta cika babu space sai na mutum É—aya lallai sai yau na san na zo Lagos dan yawancin yan matan da suka zo wurin da samarin su kan cinyar samarin suka hau muma kuma hakan ake so muyi araina nace ashe zan kwana anan, sanin da samz yayi na ni ba zan iya hakan ba sai yace in shiga in tafi shi zai taho, girgiza kai nayi nace nidai nafi son mu tafi tare dole muna ji muna gani wannan taxi É—in ta tafi bayan wasu sun shiga, a Æ™afa muka fara tafiya jin ya sake kama min hannu ya sani fincikewa cigaba da tafiya muka yi amma ganin babu haza ni da kaina na kama hannun sa na riÆ™e da hannu biyu murmushi yayi yace,

“Ba dai bakya jin magana ba, waye ya faÉ—a miki nan Kano ne, you must hold my hand whether you like it or not…..” baki na turo masa ina kallonsa,

“what eva….” ya faÉ—a yana kallo na bayan ya É—aga kafaÉ—a, sai da muka yi Æ´ar tafiya sannan muka samu taxi itanma kuma a cike cewa yayi kawai in shiga gaba in tafi ni É—aya amma na maÆ™ale kafaÉ—a,

“mu tafi tare…” na faÉ—a ina kalle kalle dan tsoro nake ji in shiga wannan motar cike da maza da mata ba su fi biyu ba ni É—aya kar aje a sace ni,

“ok muje….”

Shi ya fara shiga kafin ni, zaman dai duk a takure dan abin da bana so ɗin dai babu yadda na iya dole sai da jikina ya mannu da nashi,ni jina nake kamar akan ƙaya amma shi ya ciro wayar shi yana kallon ball alamar ma abin ko a jikinshi, har masaukinmu ya kai ni sannan ya wuce, ina shiga anty Salma tace yanzu take shirin kirana ta jini shiru ga magriba tayi, zama nayi na fara bata labarin ruwan da ya tsorata ni yau, dariya ta rinƙa yi tana cewa anya kuwa za a kai ni ƙasar Turai honey moon.

Mun jima muna hira da anty Salma yau dan har wurin 10 muka kai, shirin bacci nayi na janyo wayata da yake tana silent miss calls ɗin samz na gani sai na yaya Abdul Rashid duk ciki babu wanda nabi dan naga dare ya fara yi, kashe wayar nayi na kwanta, abubuwan da suka faru ɗazu sune suka fara dawo min, hirarmu da samz da lokutan da muka ɗebe tare, dan so kam ina sonshi har cikin raina fiye da yadda naso kowanne saurayi a baya asali ma sonshi ne ya mantar dani son kowanne namiji sai shi ɗaya, begen sa da tunanin sa fal raina nayi bacci. Shirye shiryen tafiya muke ta yi dan mun gama training sai aiki da za mu kama bayan mun koma gida munyi hutun sati biyu, kasuwa muka shiga nida anty Salma muka sha siyayyar tsaraba, Mama, Annie, ƙawalli dasu Islam yaran anty duk babu wanda ban yi wa tsaraba ba ita kuma anty na siya mata dogayen riguna na shan iska wanda zata yi renon cikinta dashi agajiye lis muka dawo dan ba ƙaramin yawo muka yi ba, rabona da samz kuwa tun shekaran jiya da aka gama training dan jiya da yau duk mun fita nida Anty Salma wadda keta alla alla agama training mu tafi taje taga yaranta dan bata da aiki sai kallon hotonsu da yin waya dasu ta rinƙa tambayarsu ɗaya bayan ɗaya yau me da me suka yi, wani lokacin zama kawai nake yi inyita kallon ta idan tana waya dasu araina ina cewa watakila nima wata rana haka zanyi, koda wa zanyi auren har in haihu Allah kaɗai masanin gaibu, wataƙila da samz, duk lokacin da na tuna hakan sai in yi murmushi araina ince da zan samu beautiful kids in dai samz ne ubansu waɗannan idanuwan sune ke shagaltar dani idan ina kallonsa, zan so in haifi yara masu da kama dashi idan har Allah ya ƙaddara tarayyarmu matsayin miji da mata, washe gari zamu tafi amma jirgin ƙarfe hudun yamma zamu bi, bayan na gama shiryawa misalin 11 yazo muka fita inata faɗa masa nidai kar ya kai ni wurin ruwan nan dan bana so, dariya yake yimin wai yau zai koya min ruwa daga yau na daina tsoron ruwa, kama ni yayi muka shiga cikin jirgin ruwan matuƙin ya tashe shi muka fara tafiya a hankali, hannaye na cikin nashi yana faɗa min irin girman son da yake yimin har ga Allah ban san mun zo tsakiyar ruwan ba domin kalaman da samz ke sanar dani masu zaƙi fiye da zaƙin zuma, ina kallon gefena naganmu a tsakiyar ruwa falala sake maƙale hannun sa nayi ina ƙokarin matsawa kusa dashi, duk da a tsorace nake haka na daure muka je ƙarshen ruwan muka sake dawowa,

“Dan Allah kar ki braking heart É—ina baby…. Idan kin tafi karki manta dani, zamu haÉ—u a Abuja, but pls don’t brake my heart” sallama muka yi ya rakoni har masauki yana tafiya naga alert na 200k daga gareshi wai kuÉ—in flight, text na tura masa na godiya araina ina tunanin ina yasamu account details É—ina daga Æ™arshe na tuna ai mun rubuta jikin attendance,muna dab da tafiya naga massage É—inshi,

_I love you._ shine abin da ya turo reply na mai da masa ina jin kewarsa acikin raina…………✍

*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*

 

*_Ummi Shatu_*

Post a Comment

0 Comments