Garin Dadi 2

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Garin Dadi 2

©️ HASKE WRITERS ASSOCIATION.
_(Home of expert & perpect writers)_

 


*GARIN DAÆŠI…….!*

*_NA_*

*_UMMI A’ISHA_*

*Wattpad:ummishatu*

 

*2*

 

~~~Ganin na zurfafa wurin tunanin da baida wani alfanu ya sanya Maryam zungurata tare da faÉ—in,

“tunanin me kike yi ne kuma? Wai dan Allah menene damuwarki Æ™awalli?”

Numfashi na ajiye ahankali kafin na kalleta ina sake gyara zamana bayan na jingina bayana da jikin gadona,

“kawai mamakin kalamanki nake ta faman yi, ta yaya ma zaki kwatanta zuciya ta da misalin mutanen da basa jin Æ™amshi ko wari? Ni dai ina ji acikin raina kawai dan yaya faisal ba type É—ina bane shiyasa bana jin sonshi acikin zuciya ta”

“dan girman Allah kibar maganar nan Æ™awalli, kawai muyi maganar abinda yadace muyi wurin karÉ“arsa, me kike ganin za mu shirya masa?”

Na san dan kawai abar maganar yasa ta faÉ—in haka, share maganar nima nayi nai tsam da raina sannan na bata amsa da cewa,

” nifa da snacks ma kaÉ—ai zan haÉ—a masa ai ya isheshi kuma bamu wahalar da kanmu ba ”

Hararata tayi tare da jan ɗan ƙaramin tsaki,

“mtswww kina da damuwa wallahi, ta yaya zamu bashi snacks kaÉ—ai? Gaskiya koda zamu bashi snacks É—in to ya zama dole mu yi masa girki”

“nifa gaskiya agajiye nake kema kin sani, dama weekend ne kaÉ—ai ranar hutuna to shima weekend É—in gashi yazo min babu hutu”

“wallahi ko zakiyi me sai mun yi masa girkin nan, mutum zai taso tun gari igari ya Abuja yazo takanas saboda ke kice wai iya snacks za a bashi? Wannan ma ba zai yuyu ba”

“to naji, yanzu ke aganinki me da me yadace muyi masa?”

“yawwa yanzu kika yi magana, fried rice ma kaÉ—ai ta isa da É—an pepe chicken É—insa sai cream cocumber and apple salad inyaso sai ayi snacks É—in da lemon kwakwa”

“shikenan to babu matsala zuwa goben da safe sai muyi”

“haka nake son ji, ko kefa, bari in tashi in je gida sai goben”

Mayafina na É—auka na bi bayanta domin yi mata rakiya, muna tafe muna sake tattaunawa har muka zo daidai sashen samarin gidan mu wanda a halin yanzu iya yaya Abdul hakim ne kaÉ—ai aciki domin yaya Abdallah yayi aure shi kuma yaya Abdurrahman ya tafi bauchi wani aiki, muryar yaya Abdul hakim muka tsinkayo yana cewa,

“idan kika sake kika fita ahaka sai jikin ki ya faÉ—a miki….”

Jikina na shiga dubawa amma banga aibun shigata ba sam domin kuwa riga da wandone ajikina masu taushi sai mayafi da na yafa,haushin hakanne yasani juyawa na koma ban Æ™ara bi ta kan Maryam ba dake tsaye suna gaisawa dashi, ina komawa É—akina nayi salla bayan na idar na sake komawa wurin su Annie waÉ—anda ke zaune cikin wata runfa dake cikin farfajiyar gidan mu, zama nima nayi bayan na zubo abinci, nan na É“ata lokaci har zuwa lokacin da Abba ya shigo nan kuma muka rankaya muka bishi sashensa, Abba yana mutuÆ™ar ji dani domin sunan mahaifiyarsa gareni haka kuma shine da kansa ya saka min sunan da ake yi min alkunya dashi wato widat. Ganin Æ™arfe goma saura ya sani yi wa su Abba sallama na wuce É—akina, miss called nagani guda biyu na yaya faisal, shirin bacci nayi ina tsaka da addu’a naji wani kiran yana shigowa, É—auka nayi bayan na kwanta na nutsu ina saurarensa,

“Ko gimbiyar ta fara bacci ne na tasheta? Ni É—inne akwai ni da rashin haÆ™uri in dai akanki ne….”

Danne abinda nake ji nayi na ƙirƙiro murmushin dole nayi wanda har shi saida ya jiyo sautin fitarsa, sau da yawa bana jin daɗin hirar da yake yi min kawai dai ina daurewa ne in danne in saurareshi amma ba wai dan yana burgeni ba,

” ba bacci nayi ba, ina wurin Abba ne kuma na bar wayar a É—aki sai yanzu na shigo”

“Æ´ar gatan Abba, ai najima da sanin dama Abba ya naji dake, duk gidan nan babu wanda ya kai mu gata”

“har da kai a tsokanar?”

“a’a ba tsokana bace, na san bacci kike ji kin dawo daga aiki kin gaji, dan haka bari na barki kiyi bacci kafin mu haÉ—u gobe”

“shikenan nagode”

“kiyi bacci lafiya, bye bye”

Kashe wayar nayi na turata can ƙasan ɗaya pillow na dake gefen kaina domin dama baccin nake ji kamar ya sani shiyasa lokaci ƙanƙani bacci yayi awon gaba dani. Misalin ƙarfe 11 saura na tashi daga baccin da na koma bayan sallar asuba ganin yanda lokaci ya tafi ya sani zaro ido a raina ina cewa,

“har yanzu Æ™awalli bata zo mun É—ora girkin nan ba”

Brush kaɗai nayi na fita amma sai dai me? Tun bayan fitowata nake jiyo wani lafiyayyen ƙamshi wanda ya tsinkar min da yawu, kitchen ɗin mama na shiga wanda daga can ne nake jiyo tashin ƙamshin, ina shiga na iske ƙawalli tanata cin uban aiki kuma ita kaɗai, ta sauke fried rice tana kwashewa cikin warmer sannan ga samosa tana soyawa gefe ɗaya kuma tana yin chicken pepe, sakin baki kawai nayi na tsaya ina kallonta gaba ɗaya ma na rasa abinda zan furta,

“yan mata sai yanzu aka tashi? Barka da fitowa”

“haba dan Allah Æ™awalli, yanzu maimakon ki tasheni muyi aikin tare sai ki zo kiyi ta wahala ke É—aya? Oya tashi in Æ™arasa”

Murmushi tayi sannan ta miƙa hannu ta ɗauko plate guda ɗaya na tangaran ta soma zuba fried rice ɗin aciki,

“na san kina jin yunwa to ga taÉ“i kije kici idan kin gama kiyi wanka ki shirya dan babu mamaki ya taho…. Ki duba cikin fridge salad É—in da na haÉ—a na ciki sai ki É—an É—ibi kaÉ—an dan na baÆ™o ne kawai dai na sanmiki ne….”

“dan Allah kibar shi in Æ™arasa kema kije ki huta” na faÉ—a ina marairaicewa,

“zancen kike so, nifa na gama aikina malama, idan ma zaki karÉ“a kije kici gara ki karÉ“a idan kuma baki karÉ“a in mayar abuna in juye dama albarkacin yaya faisal kika ci….”

Murmushi nayi na karɓa ina harararta,

“har wani ma albarkacin sa naci? Shi awa”

Bata kulani ba ta maida hankali wurin soye soyen da take yi ganin haka ya sani wucewa falon mama na É—ebi salad É—in kamar yadda tace sannan na zauna na fara ci ina sake jinjina halacci da mutunci irin na Maryam duk da na san nima É—in idan nice zanyi mata fiye da haka to amma a Æ™awayen yanzu a wannan zamanin ba lallai asamu waÉ—anda suke Æ™awance tsakani da Allah kamar yadda muke yi ba, ina ci ina duba lokaci ta agogon bangon dake kafe cikin falon ahaka na kammala na wuce É—akina, saida na buÉ—e wayata sannan na fara shirin shiga wanka, massage É—in yaya faisal ne ya shigo nan na buÉ—e naga yace min ya taho yana hanya harma ya wuce Kaduna, reply na mayar masa cewa Allah ya kawo shi lafiya, daga nan na shiga wanka a raina ina cewa gara inyi inyi in fito dan nasan yanzu zan ganshi ya Æ™araso saboda bala’in gudu gareshi a mota sam bai iya driving a hankali ba. Bayan na fito daga wanka ina shiryawa Æ™awalli ta shigo riÆ™e da plate tana cin fried rice,

“sannu da aiki, nagode madalla Allah ya bar zumunci…”

“wannan yarinyar…. Kina abu kamar wata tsohuwa wadda ta shekara É—ari a duniya, shegen manyance”

“daga godiya shine manyance? Ai shikenan, ya kusa Æ™arasowa”

“Allah ya kawoshi lafiya…”

“amin” na amsa ina Æ™oÆ™arin ciro wata doguwar riga ta wani yadin material milk colour dama kusan irin shigar da nafi yi kenan doguwar riga dan zai yi wahala ka ganni da riga da skirt ko zani, daga doguwar riga sai riga da wando, turaren Arabian oud nayi amfani dasu sannan na saka kayan na yafa baÆ™in sirrin gyale, ina zaune kusa da Maryam muna hira naga kiran yaya faisal ya shigo,

“Kinga har ya Æ™araso ba” na faÉ—a ina É—aga wayar ai kuwa ina karata a kunnena naji yace “madam gani na zo”

“ok to ina zuwa” na bashi amsa kafin na cire wayar daga kunnena na miÆ™e tsaye ina sake duba fuskata a mirror, ni na fara yin gaba ita kuma Æ™awalli zata biyoni daga baya.

Kamar koda yaushe a sashen su yaya Abdurrahman na iskeshi É—akin yaya Abdul hakim, ya sha gayunsa cikin wani sabon lallausan yadi fari kansa sanye da hula, ganina na shigo yasashi yin murmushi yana kallona,

Zama nayi É—an nesa dashi na fara gaidashi fuskata a sake duk da saida nayi namijin gaske kafin hakan ta kasance. Muna zaune muna É—an taÉ“a hira wacce mafi yawanta ta aikina ce Æ™awalli ta shigo hannunta É—auke da babban faranti wanda ta ajiye agabansa itama suka shiga gaisawa, ta É—an jima sannan ta fita ta tafi, nikam har saida lokacin sallar azahar yayi sannan na samu na fito na nufi sashen mama tun daga nan ban sake komawa wurin sa ba har sai bayan da aka yi sallar magrib duk da massage É—in da naga ya tutturo min akan wai in zo in É—auki kayana da ya kawo min, sai da na bari Æ™awalli ta dawo sannan muka je tare bayan na sake caÉ“a ado cikin wata doguwar riga Æ´ar kanti mai santsi, nan ta kwashi kayan ta fita dasu ta kai cikin gida, tare dashi muka shiga gidan suka gaggaisa dasu mama sannan ya shiga wurin Abba, tun daga nan nikam nayi sallama dashi na wuce É—akina, kayan da yaya faisal ya kawo min nagani saman gadona Æ™awalli ta ajiye min su nan na zauna na soma dubawa, turaruka ne yan ubansu designers sai kayan ciye ciye su chocolate kala daban daban sannan sai kwalin sabuwar waya Æ´ar yayi mai shegen tsada. Kinkimar kayan nayi na nufi wurin mama dasu domin nuna musu amma koda naje sai naji tace ai tuni Maryam ta kawo musu sun gani dan itace ma ta umarceta da ta kai min kayan É—akina suma ga irin tsarabar da ya kawo musu, fruits nagani kaya guda tun daga kan lemo, ayaba, abarba da apple, apple É—in na É—auka guda É—aya na wuce É—akina na ajiye kayan na soma shirin bacci bayan na gabatar da sallar ishah lokacin misalin Æ™arfe tara da rabi (9:30) na dare, kishingida nayi akan gado na na É—auki apple É—in da na shigo dashi na fara gutsira ina ci, wayata na hannuna ina duba posting É—in da aka yi a Instagram dan yau gaba É—aya ban hauba sai yanzu, kiran da ya shigo cikin wayar tawa ne ya katse min kallon da nake yi, “yanzu zai katse min jin daÉ—i” na ayyana hakan acikin raina ina Æ™oÆ™arin É—aga kiran,

“albishirinki….. Abba yace in turo magabata na……” iya abinda na iya ji kenan sakamakon silmiyewar da wayar tayi ta faÉ—i………………. ✍

 

 

*_Ummi Shatu_*

Post a Comment

0 Comments