Garin Dadi 20

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Garin Dadi 20


©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
_(Home of expert & perfect Writers)_

 

*GARIN DAÆŠI…….!*

 

*_NA_*

*_UMMI A’ISHA_*

*Wattpad:ummishatu*

_If an egg is broken by outside force, life ends, if broken by inside force, life begins. Great things always begin from inside_

 

20

*Ina kuke manyan mata Æ´an Æ™walisa ma’abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haÉ—aÉ—É—un Lagos lace wanda zaku iya samun É—inkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaÉ“inki, gefe É—aya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUÆŠI GIDA…..*

~~~Ni kaina inada yaƙinin cewa zanyi missing Samz duba da irin yadda zuciyata ta shaƙu dashi ƙwarai dagaske, duk da baida yawan hayaniya amma ni idan yana tare dani mai surutu yake zama tare da barkwanci dan haka zai yi ta tsokana ta yana zolaya ta, da tunaninsa a ƙoƙon raina muka sauka garin Abuja, Anty da kanta itace ta ɗauko ni zuwa gidanta,

“Widat da alama Lagos É—in nan ta karÉ“eki…..” Anty ta faÉ—a cikin wasa akan hanyar mu ta zuwa gidanta fuskarta Æ™unshe da fara’a, juyawa nayi na kalle ta,

“Anty me kika gani?” na buÆ™ata ina kallonta,

“Na ganine ai kin narka uwar Æ™iba…” ta bani amsa idanuwanta na kan titi,

“wai dagaske Anty?”

“Allah dagaske kin yi Æ™iba Widat, babu wanda ya faÉ—a miki? Salma bata faÉ—a miki ba?”

“Ƙawalli ta faÉ—a min kuma…..” shiru nayi ban Æ™arasa ba dan naso in yi suÉ“utar baki ince Samz ma yace nayi Æ™iba akan tsoffin pics É—in da na tura masa wanda na É—auka lokacin da na zo Abuja before mu tafi Lagos,

” To kinga ashe ba ma ni kaÉ—ai na gani ba…… ”

Murmushi kawai nayi a raina ina sake tuna shi, na san ta dalilinshi ne na samu tarin farin ciki da kwanciyar hankalin da har nake iya cin abinci in ƙoshi wanda har ya sani ƙiba, haka kuma ta dslilinsa ne farin cikin da na rasa ya dawo, ban taɓa sanin na kamu da sonshi har haka ba sai yanzu da na ɗan yi nesa dashi dan bana cikakken mintuna uku sai na tuna shi a cikin raina. Lokacin da muka ƙarasa gidan Anty salla nayi na zauna muna ta hira da ita inata bata labarin Lagos da abubuwan da suka faffaru wurin training,

“Baki bani labarinsa ba shi kuma”

“Waye kuma Anty?”

Dariya tayi kafin tace “Shi Æ™anin nawa mana”

“Anty waye ya faÉ—a miki?”

“Sai an faÉ—a min? Ai da ganin yanda hankalinki ya kwanta na gane kin samu wani wanda ya iya kula da ke kuma…..”

Tashi nayi na gudu bedroom ina ce mata zan bata labarinsa amma ba yanzu ba, sai da nayi wanka na gama shirin bacci sannan na kunna wayata, ina buÉ—eta massages É—in Samz suka fara tururuwar shigowa, tun kafin na gama karantawa kuma kiran shi ya shigo,

” Hello Darling….” na faÉ—a murya ta can Æ™asa,

“Yes Sweetie….. Sai yanzu ake samun ki?”

“Yi haÆ™uri wallahi kana raina…”

“Ya kike? Kin je gida lafiya?”

“Lafiya Lau….”

“I miss you baby…… Kinci abinci?”

“I miss you more….. Na ci É—an kaÉ—an”

“why? Bana son kina cin abinci kaÉ—an baby”

“Kafi son in ci da yawa in yi Æ™iba sosai…. Kana ji Anty ta fara cewa nayi Æ™iba sosai”

“Nima ai na faÉ—a miki….. Amma idan kin Æ™ara kaÉ—an ki barta haka….. Idan kika yi nauyi da yawa ba zan rinka É—aukar ki ba….” tun kafin ya Æ™arasa na shagwaÉ“e fuska cikin shagwaÉ“a kamar zanyi kuka nace,

“Ba zaka rinÆ™a É—auka na ba?” na faÉ—a kamar zanyi kuka,

“Ehh mana, idan kina so in rinÆ™a É—aukar ki kar kiyi nauyi da yawa”

“uhmm uhmmm…. Ni dai a’a” ni kaina bana sanin na iya shagwaÉ“a sai idan ina tare da Samz ban san dalili ba sai in yi ta masa shagwaÉ“a shi kuma yana biye min yana rarrashi na kamar wata baby koda yake da babyn ma yake kirana,

“ok is alright….. Zan rinÆ™a É—aukar ki, har goyaki zan rinÆ™a yi, ko abinci a baki zan rinÆ™a baki, ni zan rinÆ™a yi miki wanka ina shirya ki” jin ya ambaci wanka ya sani faÉ—in,

“uhmm uhmmm” cikin shagwaÉ“a,

“Kina jin kunya ko, karki damu kwana É—aya za muyi tare zaki ji kin daina jin kunya ta”

“uhmmm” na sake faÉ—i cikin shagwaÉ“a,

“Hmmmmm baby kenan….” ya faÉ—a cikin harshen Hausa abin da yayi mutuÆ™ar bani mamaki dan kwata kwata ban san ya iya ba saboda ban taÉ“a jin sa yayi ba,

“Baby….. Ya za ayi in ganki gobe?” ya sake tambaya ta da hausa,

“Wai dama kana jin hausa?”

Dariya naji yayi kafin ya bani amsa da “Uhumm”

“Ohh Allah shine baka taÉ“a nuna min ka iya ba…. Allah ya soni ban taÉ“a gulmarka agabanka ba da hausa”

“Da kin yi ma da sai inji in yi shiru kamar ban ji ba”

“Gobe da yaushe zaka dawo?”

“Ƙarfe 9 na safe”

“ok zuwa yamma dai, za muyi waya duk yadda ake ciki za ka jini”

“ok baby….. Kina jin bacci?”

Kafaɗa na maƙale kamar yana gabana yana kallo na,

“Ni ban gaji da jin muryarka ba….”

“Nima ban gaji da jin taki muryar ba kawai dai bana son in takura miki gashi kin gaji ko…”

“Gajiyar training ce da kuka rinÆ™a tara mana ita a zaune…”

Dariya naji yayi sannan yace, “Kinga masu miji sun huta yanzu suna can ana rage musu gajiya….. Kema da matata ce da tuni na rage miki ita”

“ka Æ™ara min wata dai” na faÉ—a acikin raina a fili kuma ce masa nayi “Dama ana rage gajiya ne? Ta yaya?”

Murmushi yayi “zan gwada miki amma ba yanzu ba, sai mun zama abu guda”

“to shikenan, zan jira”

“kiyi bacci ki huta, oya close your eyes….” a hankali na lumshe idanuwa na ina sauraren kalaman da yake faÉ—a min ban san lokacin da bacci ya kwashe ni ba ko addu’a sai da na farka misalin Æ™arfe 2:30 nayi fitsari nayi alwala sannan nai addu’ar na sake kwanciya babu É“ata lokaci wani baccin yayi gaba dani ban sake tashi ba sai bayan asubah, 6 na safe ina tuÆ™unÆ™une amma ba bacci nake yi ba naga kiransa, tsokana ta ya fara yi wai jiya bacci babu sallama, baki na turo masa da yake video call ne yana ganina ina ganinsa,

“Ba Kaine ba ka sani baccin dole….” dariya yayi ya shafa sumar kan shi ya kalleni da wannan shanyanyun idanuwan nasa masu É—aukar hankali,

“ke ki godewa Allah ma kina iya bacci da zarar kin kwanta, ni duk abin da zanyi bana iya bacci sai after 2 wani lokacin ma har 4 idona biyu”

“me yasa?”

“kawai na riga da na saba ne tunda jimawa” kwanciya ta na gyara na kalleshi sosai,

“to me kake yi?”

“just Games, watching movies etc” ya faÉ—a yana yimin murmushi araina nace daÉ—in musulunci kenan da ace musulmi ne ya samu wannan damar da sai yaita sallolinsa da karatun Alqur’ani tunda har asuba yake kaiwa wani lokacin baiyi bacci ba,

“Amma kuma kaje asibiti kaga Dr?”

“yeah naje, babu wani problem fa lafiya ta Æ™alau”

“Ai kuwa akwai matsala, yanzu da kana da mata ya kenan?”

“Babu baccin dare, zaki yita tayani hira har lokacin baccina yayi sai muyi baccin tare…”

“uhmm… Uhmm…. Nidai baccina zanyi in barka”

“ai kuwa baki isaba…. Kema hana ki bacci zan yi”

“Za mu gani ai”

“ki dai shirya dan babu baccin dare sai baccin safe”

“wai kai dan baka yi shikenan kowa ma ba zai yi ba? Ni zanyi bacci na kai kuma zaka yita games É—inka da kallon films har lokacin baccinka yayi”

“No, wannan ai lokacin da nake ni É—aya ne babu abokin hira, amma idan muka yi aure ai kinga na samu abin da yafi Games da Films É—ebe kewa”

“nidai a’a”

“To shikenan na yarda zaki yi bacci tun 8… Ba zan hanaki ba”

“yawwa ehh”

Dariya yayi yace wai zanyi bayani, har 8 muka kai muna hira kafin muka yi sallama na sake komawa bacci, sai after 10 na tashi nayi wanka na shirya na san yanzu Samz ya sauka, text massage na tura masa ina tambayarsa ko ya sauka, reply ya dawo min dashi yace ehh bai kirani bane dan baya son ya tasheni a bacci, murmushi nayi na zauna dan yin breakfast wadda mai aikin Anty ta haÉ—a saboda ita yanzu cikinta ya fara girma ba kowanne aiki take yiba. Tun Æ™arfe 3 nake tunanin ta yadda zan tunkari Anty da maganar fita dan munyi da Samz cewa zamu haÉ—u around 4 o’clock sai dai ban san ta yadda zan faÉ—awa Anty ba dan nasan a yanzu dai ba kowane zai fahimce ni ba duk wadda yaji ina soyayya dashi a matsayinsa na wadda ba musulmi ba fassara É—aya za ayi mana cewa iskanci muke kawai wannan fassarar na daÉ—e da saninta acikin Æ™abilar Hausa Fulani duk lokacin da saurayi musulmi ke soyayya da yarinyar da ba musulma ba kallon É—an iska ake yi masa to nima na san duk wanda ya ji kallon da zai yi min kenan kaÉ—anne zasu yi wa lamarin kyakkyawar fahimta shiyasa da ya nemi da in bashi address É—in gidan Anty akan wai shi zai zo har gidan naÆ™i nace mu haÉ—u kawai a inda yace da farko,

Bedroom ɗin Anty na shiga duk da ban san ƙaryar da zanyi mata ba domin ba halina bane kuma ban saba ba, tana kwance tana duba wani kundi (Nigerian constitution), zama nayi gefen gadonta,

“Anty sannu da hutawa”

Ajiye littafin tayi ta kalleni fuskar ta ƙunshe da murmushi,

“Yawwa Widat, ya akayi?”

“Anty ina so ne zan fita….”

“Ina zaki je?”

“Dama Anty wani ne da muka haÉ—u dashi a wurin training É—in nan to wai yana son yazo wurina ni kuma bana son yazo yanzu shine sai nace masa zan je saloon dama yau to za mu haÉ—u acan….”

“Widat kenan…. Ai darajar budurwa saurayi ya taka Æ™afa da Æ™afa yaje gidan su ba wai su rinÆ™a haÉ—uwa a waje ba amma ku Æ´anmatan yanzu ban san menene matsalar ku ba bakwa son hira a gida sai dai wuraren shaÆ™atawa….. Shikenan tunda É“oye mana shi akeyi wata rana dai dole mu ganshi idan auren ya taso”

Dariya nayi na tashi na fita naje na sake shiryawa na fito nayiwa Anty sallama na fita bayan tayi min jan kunne da gargaÉ—i akan in kula kuma in dawo before 6,saloon na fara zuwa aka wanke min kaina aka gyara tun lokacin da aka fara yimin gyaran gashin muke chaten da Samz ina faÉ—a masa shagon yace yasan wurin, alert na gani na 50k da nayi masa magana sai cewa yayi wai kuÉ—in saloon É—inne, gyara rolling É—ina nayi na fita daga shagon bayan angama min, ina fita na ganshi tsaye daga gefe ya sha p cap yana latsa wayar shi na ganshi sarai amma sai nayi kamar ban ganshi ba na wuce,

“Hey baby….” ya faÉ—a tare da biyo bayana, ban kula shi ba nayi gaba na cigaba da tafiya ta dan har ga Allah banji daÉ—in kuÉ—in nan da ya sake turo min ba me hakan yake nufi? Dab dani yazo muka jera amma ban ko kalleshi ba, a Æ™afa muke tafiya har muka Æ™arasa wani É—an Æ™aramin wurin hutawa, ganin inata fushi na Æ™i kula shi ya sa shi niyyar sake tsokanata, yarinyar da ta kawo mana drinks da snacks É—in da yayi order yake yiwa magana wai kitsonta yayi masa kyau, harara nake aika musu daga shi har ita kamar idona zai fito waje, hannuna naji ya riÆ™o bayan ta tafi,

“Am sorry baby…..” ya faÉ—a yana murza Æ´an yatsuna, wata hararar na sake aika masa amma duk da haka bai saki hannun nawa ba saima sake damÆ™eshi da yayi wanda hakan yayi daidai da shigowar…………

 

*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*

 

_*Ummi Shatu*_

Post a Comment

0 Comments