Garin Dadi 22

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Garin Dadi 22


©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
_(Home of expert & perfect Writers)_

 

*GARIN DAÆŠI……!*

 

*_NA_*

_*UMMI A’ISHA*_

PAID BOOK

*Wattpad:ummishatu*

22

*Ina kuke manyan mata Æ´an Æ™walisa ma’abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haÉ—aÉ—É—un Lagos lace wanda zaku iya samun É—inkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaÉ“inki, gefe É—aya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUÆŠI GIDA…..*

~~~Daren ranar gaba É—aya bacci Æ™auracewa idona yayi damuwa cunkushe fal raina, zuciya ta tana ta saÆ™a min abubuwa da dama game da tarayya ta da Samz musamman ma idan na tuno irin maganganun da Ƙawalli ta faÉ—a, tabbas nima nasan duk abubuwan da ta faÉ—a babu ja ko Æ™arya acikin su sai dai amma shi so ba kaine kake zaÉ“awa kanka wanda zaka so ba zuciyar ka ce ke da wannan ikon, ganin wankin hula na shirin kaini dare ya sani tashi na shiga toilet na É—auro alwala na fito na zo na fara sallar nafila, na jima kuma na daÉ—e goshina a Æ™asa inata addu’a akan neman zaÉ“in Allah dangane da lamarina da Samz, addu’a ta bata wuce idan har shigowarsa rayuwata babu alkhairi to Allah yayi gaggawar cire shi araina kuma ya kawo min musulmi É—an uwana wanda zai soni tsakani da Allah, idan kuma akwai alkhairi a tarayyarmu dashi ubangiji Allah ya sauÆ™aÆ™a lamarin ya cika mana burinmu,

Saida nayi karatun littafi mai tsarki na karanta suratul Qasas sannan na kwanta lokacin misalin ƙarfe uku da yan mintuna na dare, ina kwanciya babu jimawa bacci ya ɗaukeni zuciya ta fess babu sauran damuwa, duk wannan ɓacin ran ya gushe sakamakon ayoyin Allah da na karanta a wannan dare, abin da ban sani ba shine shima samz cikin damuwar yake saboda ya saba da duk daren duniya sai munyi hira amma yau wayata a kashe tun bayan da Ƙawalli ta bar gidanmu, haka ya kwana cikin damuwa da rashin sanin takamaimai abin da ya faru da har yasa na kashe waya ya kasa samu na, shi dama ba baccin dare yake yiba shiyasa haka ya kwana cikin damuwa.

Nikam yau da farin ciki na tashi kamar anyi min albishir kuma wani abin mamaki ji nayi ina É—okin jin muryar samz kamar irin na shekara ban ji shi É—innan ba, shiyasa tun ina kan gadona na kunna wayata na kira shi ko wanka banyi ba brush kaÉ—ai nayi, katse kiran nawa naga yayi sai gashi ya kirani video call, murmushi nayi na kalli jikina na tabbatar da babu matsala domin sanye nake da riga da wando na bacci peach masu É—an kauri sai pink É—in hula akaina,

“Baby….. What happened?? “

Murmushi nayi na sunkuyar da kaina ƙasa ina mutsuttsuka ido,

” Good morning…… ” na faÉ—a ina lumshe idona,

” Ba zan amsa ba É—ago idonki in ganki first…. ”

ÆŠagowa nayi na kalleshi shima yana kallo na,

” kin yi bacci jiya?” kai na É—aga masa,

“OK, me yasa kika kashe wayarki?”

“Ban jin dadi, kaina ke ciwo amma yanzu ya daina da na samu bacci”

“OK sorry…… Kin yi breakfast?”

“A’a, yanzu na tashi ai”

“ok kiyi breakfast ina kallon ki….. Idan kin gama zan kwanta in yi bacci”

“OK bani 2 minutes”

Wayar na ajiye akan gado na nafi ta zuwa kitchen, ruwan zafi na zuba a cup na saka lipton da sugar sannan na zuba É—umamen tuwo na koma É—aki, har lokacin yana kan waya bai kashe ba sai dai ya ajiye ta shima yana wani abu a system É—insa,

“Am back Darling…..”

“Me zaki ci?”

“tuwo, ka san nayi missing É—umame, a Lagos bakwa ba mu tuwo na dawo gidan anty itama babu tuwo…..”

“Baby rigima…. Ok bari in zauna in kalli laumarki….”

Dariya nayi na fara cin tuwo na ina ce masa ai tawa ƙarama ce akan tasa,ina ci muna hira da haka har na cinye sai lokacin muka yi sallama dan zai kwanta yayi bacci, ni kuma wanka nayi na shirya na fita wurin su mama naje muka sha hira nayi ta basu labarin Lagos da Abuja, wurin ƙarfe 12 na nufi gidan su ƙawalli,

A tsakar gida na sameta tana gyaran ɗanyen zogale wanda zata yi dambu, mayafi na nacire na lanƙaye a sama sannan na ɗauko bokitin ƙarfe na zauna,

“Yan mata…. Umma fa?” na faÉ—a ina gyara zamana,

“Ta je asibitin malam….” ta bani amsa batare da ta É—agoba,

“waye bai da lafiya? “

” wani aminin mahaifi su ne, shi ne taje duba shi ”

” ayya Allah ya bashi lafiya ”

” amin”

“Baki tambayi Samz ba” na fada cikin sigar jan magana”

Dakatawa tayi daga abin da take yi ta Kalleni,

“au baki hakura da maganar samz É—innan ba ko widat? Wai widat kin kuwa san halin da kike Æ™okarin jefa kanki? Soyayya da arne?”

“Ƙawalli kenan abin da nake nuna miki daban abin da kike kallo daban, kin kasa fahimtata”

“ai bazan taÉ“a fahimtar ki ba indai akan wannan maganar ne Æ™awalli na faÉ—a miki wannan guy É—in wallahi yaudararki zai yi, kawai zai yi amfani da son da kike yi masa ne idan ya tabbatar kin gama kamuwa, Allah tun wuri kiyi nesa dashi”

“bazan iya ba Æ™awalli, wallahi ba zan iya rabuwa dashi ba, ke bana ma jin zan iya rayuwa batare da shi ba, rabuwa dashi kamar rabuwa da numfashi na ne…..”

“TirÆ™ashi….. Lallai kin yi nisa, to yanzu idan akace ya fito kuyi aure sai ayi yaya? Kin dai san babu yadda za ayi kuyi aure a haka ko? Dole acikin biyu ayi É—aya ko dai ya musulunta ko kuma ku rabu, ke ni bama na jin zai iya musulunta kuma koda ya musulunta É—in akwai wata a Æ™asa wallahi da sauran rina a kaba….. ”

” wai dan Allah me yasa kike negative thinking akan samz, nifa jikina yana bani alkhairi ne haÉ—uwa ta dashi, sannan tun farko ni na fara sonshi har shima ya kamu da so na, kuma bai taÉ“a yimin maganar addininsa ba ko tallarsa…. Wallahi Maryam ba zan É“oye miki ba ina yi masa wani irin mahaukacin so wanda ban taÉ“a yi wa wani É—a namiji ba ”

Cike da tsananin mamaki take kallo na har saida na dasa aya,

” Ikon Allah…. Gaskiya Æ™awalli ba dan nayi miki kyakkyawan sani ba kuma na san irin tarbiyar da kika samu daga gidan da kika fito haka na san abin da zaki iya aikatawa da wanda ba za ki iya ba da nace wani abu…..” murmushi nayi nace, “faÉ—i duk abin da ke ranki sai in wayar miki da kai idan ba haka bane”

“wallahi wallahi ba dan nayi miki farin saniba zance ko kun É—anÉ—ana juna shiyasa kuka mayincewa juna…..” ko kaÉ—an ban ji haushin kalamanta ba madadin haka ma dariya suka sani sai da nayi mai isata sannan na bata amsa,

“Dama na san hakan zata faru Æ™awalli, bake kaÉ—ai ba kusan duk wanda zai ji muna soyayya da Samz abinda zai fara zuwa ransa kenan…. Sai dai wallahi ba haka bane, nida shi mun yi wa junanmu alÆ™awarin insha Allah baza muyi koda kiss ba sai bayan munyi aure bare har mu aikata alfasha…. Wallahi Æ™awalli samz yana da nutsuwa kuma i trust him 100%, ni nasan baya shan giya kuma baya neman mata, bayan ya faÉ—a min da bakin sa saida na sake bincikawa da kaina ba tare da ya sani ba kuma har yau bai sani ba…. Har É—akin da ya sauka a hotel lokacin da muna training naje dan in duba shi amma har na dubashi na fito bai ko yi yinÆ™urin kama hannu na ba, bayan na fito sai da naje wurin masu kula da hotel É—in da shige da ficen mutane muka yi magana dasu na yi musu tambayoyi akan shi amma duk amsar É—aya ce babu macen da ta taÉ“a zuwa wurin sa sai ni kuma bai taÉ“a yin order É—in giya ba….. Kinga tunda abubuwan nasa basu wani Æ™azanta ba ni ina ji ajikina nan gaba zai iya karÉ“ar shahada, ni kaina ban taÉ“a zaton zan samu kaina dumu dumu cikin soyayyar wanda ba musulmi ba dan sanin kanki ne nafi kowa Æ™yamatarsu da tsanarsu dan komai daÉ—in abu indai ya fito daga hannun su wallahi nabar abin kenan har abada kuma indai naci to sai nayi amai idan daga baya akace min sun taÉ“a, nidai kawai na É—auki wannan a matsayin jarrabawa dan haka addu’a kawai nake buÆ™ata…… ” ajiyar zuciya ta sauke jikin ta duk yayi sanyi da maganganu na,

” Tabbas kam jarrabawa ce, Ubangiji Allah ya baki ikon ci, muga pics dinsa dan Allah ”

Wayata na miƙa mata bayan na fito mata da pics ɗinsa,

” Wayyo ni Allah, GARIN DAÆŠI NA NESA, irin wannan haÉ—aÉ—É—en guy haka Æ™awata… Ina ma musulmi ne, dole ki ruÉ—e ashe ba a banza ba ”

Murmushi nayi dan har ga Allah a karon farko nidai ba kyawunsa ne yaja ni na faɗa sonshi ba haka kawai naji yayi min, hira sosai muka yi da Ƙawalli dan har saida ta kammala dambun nan muka ci sannan nayi mata sallama na koma gida. Soyayyar mu muka cigaba da yi nida samz, bayan dawowa ta da sati ɗaya yamin waya wai zai zo kano ya ganni, duk atunina da wasa yake yi shiyasa nayi dariya nace ina jira, zuwa yamma sai ya sake kirana wai gashi a kano ya sauka a wani guests palace in bashi address ɗin gidanmu zai zo, ai babu shiri na tashi daga kwancen da nake ina hutawa,

“Wai dagaske ka zo?” na faÉ—a idanuwana awaje,

“yeah am serious baby….”. Ya bani amsa, rasa abin cewa nayi dan ni dai ko giyar wake nake sha bazan bari Samz yazo gidanmu ba dan masifar Yaya Abdul Hakim ma kaÉ—ai ta isheni kafin azo kansu mama wanda kullum maganar su kar mu zubar musu da mutunci a idon duniya,

” Baby baki ce komai ba….” jin maganar sa yasa na dawo hayyacina,

“Cutie….. Dan Allah ka fahimce ni, wallahi ban san dagaske kake yiba da bazan barka ka zo ba saboda zuwanka gidanmu zai haifar min da matsaloli masu tarin yawa….”

“to yanzu ya za ayi? Nidai dole ina son ganin ki, bazan iya hakura in tafi ban ganki ba…. Tunda baki son in zo gidanku to a ina zamu haÉ—u, zaki zo Guest house É—in da na sauka?”

“No cutie, nanfa Kano ne, Baban mu da brothers É—ina an san su sosai, idan na zo hotel wurin ka za asamu matsalar da tafi wacce za a samu idan ka zo gida…”

“OK yanzu kina nufin bazan ganki ba gaba É—aya? Nace zan zo gidanku kin Æ™i, nace ke ki zo nan ma kin Æ™i…” ya faÉ—a cike da damuwa ni kaina acikin damuwar nake da kuma tarin ruÉ—ani gaba É—aya ban san menene mafita ba, jin ya kashe wayar ya tabbatar min da cewa wataÆ™ila fushi yayi ko dai wani abu me kama da haka, hijabi na É—auka, sai da na tabbatar babu wanda ya ganni sannan na sulale na bar gidan, gidan su Æ™awalli na shiga inata cin uban sauri, ina shiga ummansu tace wai ban haÉ—u da ita ba dan itama wai yanzun nan ta fita unguwa, sake juyawa nayi cikin damuwa na fita, ina fitowa muka yi kiciÉ“us da ita,

“yan mata lafiya kuwa, saurin me kike yi haka?” ta faÉ—a tana kama hannuna, abin da ya fito dani na kwashe na faÉ—a mata na Æ™are maganar da cewa,

“Ni yanzu ban san yanda zanyi in ganshi ba wallahi dan bani da wata dabara”

“Karki damu, kije gida ki shirya gani nan zuwa, Allah yayi zamu haÉ—u dan har na tari napep zamu tafi na duba handbag É—ina naga ashe ban É—auki kuÉ—in ba, kije ina zuwa”

Cikin farin ciki na juya na koma gida ina zuwa na hau shiri cikin wata lafiyayyar stones grown nasha turare kamar wadda zan je gasar sarauniyar Æ™amshi, ban wani É“atawa kaina lokaci ba wurin yin doguwar kwalliya na É—auki wayata da side bag É—ina ina jiran Æ™arasowarta………..✍

 

*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*

 

*_Ummi Shatu_*

Post a Comment

0 Comments