Garin Dadi 25

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Garin Dadi 25


©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATIONS*
_(Home of experts & perfect Writers)_

 

*GARIN DAÆŠI….!*

 

*_NA_*

*_UMMI A’ISHA_*

PAID BOOK 500

*Wattpad:ummishatu*

 

25

*Ina kuke manyan mata Æ´an Æ™walisa ma’abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haÉ—aÉ—É—un Lagos lace wanda zaku iya samun É—inkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaÉ“inki, gefe É—aya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUÆŠI GIDA…..*

~~~Tabbas shi ɗinne nake gani kamar a mafarki yayi kyau har ya gaji cikin milk colour ɗin yadi na maza ɗinkin half jamfa kansa sanye da hula ya ɗaura agogon azurfa a hannunsa, sam babu abin da ya canja na daga halittarsa yana nan kamar yadda na san shi sai ma kyau da kwarjini da ya ƙara,

Zumbur na miƙe tsaye ina sake kallonshi fuskata ɗauke da mamaki sannan ga tsantsar farin ciki wanda ya taru ya haɗu da mamakin da nake ciki, shima tsayen ya miƙe yana kallona fuskarshi ɗauke da murmushi, ai ban san lokacin da na kwasa a guje ba na tafi gareshi, ina zuwa ya buɗe min hannuwansa sai kuma na tsaya turus sake buɗe min hannuwan nashi yayi, saida na rufe fuska ta da hannaye na sannan na iya ƙarasawa na shige jikinsa, rungumeni yayi yana dariya, nima rungume shi nayi tsantsam kamar ina tsoron kada ya sake tafiya ya barni.

Mun jima tsaye rungume da juna ina cikin ƙirjinsa ina shaƙar ƙamshin turaren da ke fita daga jikinsa gaba ɗaya ma na manta da cewa a falon Abba muke, sai da na tuna sannan na shiga kiciniyar raba jikina da nashi, duk da haka bai sake ni gaba ɗaya ba yana riƙe da hannuwana duka guda biyu muna zaune a kujera ɗaya sai kallon juna muke kamar zamu cinye junanmu,

“Baby….. Why all this silent? Yanzu kin kyauta kenan? You broke my heart….”

Murmushi nayi na sunkuyar da kaina ƙasa ina tunanin amsar da ya dace in bashi,

“Ba kaine ba ka tafi ka barni….” na faÉ—a cikin shagwaÉ“a ina turo masa baki,

“Am sorry baby…”

“ni ban haÆ™ura ba, sai kayi min alÆ™awari guda É—aya”

“FaÉ—a min ko menene am ready to do it….”

“Sai kayi min alÆ™awarin ba zaka sake tafiya ka barni ba”

Murmushi naga yayi kafin ya ɗauke idonsa daga kan ƙunshin hannuna ya kalleni,

“OK i promise you bazan sake tafiya in barki ba and i have a good news da zan faÉ—a miki”

“Gist me please” na faÉ—a ina kallonsa,

“well…. Am a Muslim now”

Ai jin maganar tasa nayi kamar cikin mafarki, rasa abin da zan yi nayi sai kawai na sake rungume shi ina jin ƙwallar farin ciki tana ƙokarin zubowa daga idanuwa na,

“Samz are you kidding me?” na buÆ™ata cikin zaÆ™uwa,

“no am not….. Am serious baby”

“Thank you Cutie, thank you for saving my life……”

Ɗago fuskata yayi yana kallona kallo sosai irin na ƙurulla,

“baby naga kin canja, kin yi rashin lafiya ne?”

Kai na É—aga masa ina murmushi,

“ayya sorry, kin samu sauÆ™i yanzu”

“Ehh na samu sauÆ™i, ya aka yi ka musulunta? Gidanku basu hana ka ba?”

Murmushi naga yayi idanuwansa akan hannuwana,

“Daddy na musulmi ne…..”

“wai dagaske? Wow”

“seriously…… Shida uncle É—ina duk musulmai ne, mommy na ce Christian…. Amma shi Dad É—inmu asali Christian ne sai daga baya ya musulunta shi kuma uncle É—ina tun asali dama musulmi ne….”

“Amma naji daÉ—in wannan labarin, soo what’s your name now?”

Murmushi yayi ya sunkuyar da kai kafin ya É—ago ya kalleni,

“Guess it….”

ÆŠan shiru nayi alamar tunani tsawon minti É—aya nace,

“Muhammad…”

“uhmm kin kusa dai…. My dad is used to call me Muhammad but akwai inkiya”

“Wow….. I love you” na faÉ—a ina É“oye fuskata,

“I love you too baby….. Kin rame amma kin fi kyau a haka”

Kallon jikina nayi dan ni kaina na san na rame amma maganar ma nafi kyau a haka bata taso ba sai dai shi ban san me ya gani ba, a haka anty ta shigo ta same mu tana ɗauke da babban tire na silva da kanta, fruits ne da abinci da juice da ruwa, bayan anty ta fita ina ƙasa ina zuba masa abinci naji yace,

“Ai lokacin da na zo naga mutane har gabana ya faÉ—i nayi zaton ko ke za ayi wa aure”

Sai da na É—an dara sannan nace, “to da ni É—in ce da ya zaka yi?”

“Allah da ba zan yarda ba, zan tada riot har sai an bani matata”

Dariya na sake yi bayan na gama zuba masa abincin nace,

“Ta ina na zama matarka?”

“matata ce mana, nan da 2 months”

“Ohh harma kayi fixing date shine ban sani ba”

Biye min yayi naci gaba da tsokanar shi har ya ci abincin ya gama, ni dai yau jina nake kamar ba ni ba dan tamkar a mafarki, mun jima muna hira dan har magrib saida yayi sallar magriba sannan ya tafi, a daren ranar Abba ya kirani yake tambaya ta wai ina son Muhammad zan aure shi? Shiru nayi na kasa bada amsa dan shine kaɗai namijin da nake so a halin yanzu daga ƙarshe Abba yace to in tashi inje amma zai ɗauki shiruna a matsayin ehh,

Ina komawa ɗaki na ɗauko wayata daga cikin drawer ɗin madubina wadda ke ajiye wata da watanni nan na kunnata ina kunnuwa massages suka yi ta shigowa wanda mafi yawa na samz ne, daren ranar kuwa kusan kwana muka yi muna waya dashi, washe gari ya koma Abuja ni kuma ranar muka fara bikin gidanmu dan ranar ne kamu, nida amarya wurin kwalliya muka je aka cancaremu aka fito mana da ainihin kyawun mu tun a wurin nayi pics na turawa abin ƙaunata, ita kuma ƙawalli sai tsokanata take wai in yi ingama nima nan da 2 months ne ni duk ban ɗauki maganar ta wani serious ba kamar yadda bana ɗaukar ta Samz serious idan yace saura namu nan da 2 months, cikin farin da annashuwa muka yi kamu muka gama, Ƙarshen gajiya na gaji dan ko Samz yau ba muyi doguwar hira ba,

Ranar ɗaurin aure sai gashi ya zo, ya sha farar shaddarshi ƙal dama can shi gwanin saka manyan kaya ne kuma suna yi masa kyau, a ranar ya koma bayan mun sha hira na kai masa abinci yaci, washe gari aka yi yini kuma a ranar aka raka amarya gidanta dake unguwar Kwandila, nikam bayan bikin nan sai da nafi sati ɗaya ina baccin gajiya sakamakon gajiyar da na kwasa, ƴan biki kuwa tuni sun baje sai ƴan gida sune basu tattafi ba,sai bayan bikin sannan nake jin ana maganar bikina wai nan da wata biyu anty harda cewa wai dan Allah in dai daure in yi ƙiba kafin bikin kuma zata haɗo min wani haɗi mai kamar garin kunu in rinƙa damawa ina sha,sai ranar na tabbatar da dagaske nima anfara lissafin aure na, washe gari da naje gidan ƙawalli muke ƙara maganar danni sai naga kamar ansa lokacin yayi kusa sosai maimakon ma ace irin wata huɗun nan ko biyar zuwa shida, dariya ƙawalli tayi tace,

“Keda wannan samz É—in naki ai gara dai ayi ayi a miÆ™aku É—akinku tun kafin haÆ™urinku ya Æ™are”

“me kike nufi?” na faÉ—a ina harararta,

“Ni babu abin da nake nufi kawai gaskiya na faÉ—a”

Ban bata amsa ba na ɗauki wayata na yi gefe ina amsa kiran da Samz keyi min, har dare ina gidan ƙawalli sai da nayi sallar ishah sannan yaya Abdul hakim ya maida ni gida, yanzu kam kusan kwana muke yi muna waya yau ma tun 9 muke waya yana bani labarin ta yadda yasan gidanmu har suka zo shida uncle ɗinsa wai gidan anty yaje dayake lokacin da ina Abuja ya taɓa rakani yaga gidan, itace ta bashi phone no ɗin Abba kuma tayi masa kwatancen gidanmu a Kano kuma tun kafin su zo uncle ɗinsa ya sanar da Abba buƙatarsu ta ayi bikin kwana kusa, cikin bargo na shige sosai sannan nace,

“Amma dai kasan bana son barin Kano ko?”

“kina nufin in barki a Kano?”

“Ehh mana”

“OK babu problem zan barki a Kano, duk lokacin da kike son zama dani sai ki zo Abuja lokacin da kika ji bakya son ganina kuma sai ki dawo gidanki na Kano”

“dagaske zaka barni a Kano?”

“Dagaske Allah, zan sama miki gida anan”

“Nagode sweetheart”

“Don’t mention it dear”

Kusan kwana muka yi muna hira a waya yana bani labarin irin tanadin da yayi min idan munyi aure nima ina faÉ—a masa nawa da haka har bacci ya kwashe ni na barshi nan kan waya yana magana shi daya saida yaji shirun yayi yawa babu amsa sannan ya farga………✍

*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*

 

_*Ummi Shatu*_

Post a Comment

0 Comments