Garin Dadi 26

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Garin Dadi 26


©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
_(Home of experts & perfect Writers)_

 

*GARIN DAÆŠI…..!*

 

*_NA_*

_*UMMI A’ISHA*_

PAID BOOK #500

*Wattpad:ummishatu*

 

26

*Ina kuke manyan mata Æ´an Æ™walisa ma’abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haÉ—aÉ—É—un Lagos lace wanda zaku iya samun É—inkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaÉ“inki, gefe É—aya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUÆŠI GIDA…..*

~~~Abu kamar wasa shirye shiryen biki sun kankama gadan gadan a gidan mu kuma sai lokacin na fara jin fargabar auren da za ayi min, ada bani da magana ko buri sai na in ganni a gidan Samz amma yanzu da zarar na tuna sai inji gabana ya faɗi sannan ga wata irin kewa da nake ji ta ƴan gidanmu gaba ɗaya tun kafin in bar gidan sai dai duk da fargabar da nake ciki hakan bai hanani yin kumari ba saboda yanzu bani da wata sauran damuwa ko matsala, kullum muna tare da shi awaya duk da tun zuwanshi bikin Yaya Abdul Hakim bai ƙara dawowa ba sai dai ta waya wannan kam yakan ɓata lokutansa da dukiyarsa wurin hira dani, lokacinsa yake bani sosai kamar bai da sauran wani abu mai muhimmanci a rayuwar sa sama dani, duk wani abu da ya shige masa duhu dangane da addini ni yake fara tambaya ni kuma in bashi amsa gwargwadon sanina da fahimtata wanda kuma ilmi na bai kai ba sai in tambayi Abba, sosai ya dage wurin neman ilmin addini dan duk bayan sallar magriba yake zuwa wurin wani alaramma ɗaukar karatu, ni dai a lokuta da dama ina zama in yi shiru in yi ta tunani dan har yau ban san kowa nashi ba duk da ya sanar dani yana da ƙanne Hadiza, Maryam da Abdallah saboda mahaifinsu dama can sunan musulmai yake saka musu duk da mommy bata so,

A yanda na fahimta samz yana tare da damuwa duk da bai fito fili ya sanar dani ba ya barwa ransa domin damuwar tana da nasaba da mahaifiiyarsa dan gaba É—aya ta fita sabgarsa ko gaisuwarsa bata amsawa tun daga ranar da yaje mata da maganar yana son zai musulunta, tun daga lokacin idan yayi mata waya bata É—auka idan ya kira Æ™annenshi sun bata wayar bata karÉ“a fushi take yi dashi sosai kuma wannan abun shine yafi komai damunsa ahalin yanzu, duk da tana fushi dashi hakan bai hana shi sake shiryawa ba ya nufi Kaduna ranar Juma’a, saida yayi mata tsaraba da kayan fruits domin tana mutuwar son kankana da gwanda da abarba da kuma apple, duk ya siya mata harda Æ™arin ayaba da lemo, bayan sallar la’asar ya shiga gidan sanye da farin yadi riÆ™e da kayan da ya siya, tana zaune tsakar gida tare da Æ™anwarshi Mary tana yi mata kitso, Mary ce kaÉ—ai tayi masa magana ta hanyar gaida shi amma ita mommy yi tayi kamar bata san dashi ba a wurin,

“Mommy…. Zuwa nayi in baki haÆ™uri akan abin da nayi miki, pls forgive me mommy….. Dan Allah ki daina fushi dani, fushinki zai iya cutar da rsyuwata”

“Ai Samuel baka ga komai ba, ba dai kace ni zaka watsawa Æ™asa a ido ba? Ni da na haife ka na reneka na kula da rayuwar ka ni kayiwa haka ko? To hanya É—aya ce kuma ita kaÉ—ai zata sa in daina fushi da kai, kayi gaggawar barin wannan addinin ka dawo kiristanci ”

” Mommy kiyi haÆ™uri ”

” ka tashi kaje na gama magana ”

Tashi yayi bayan ya ajiye mata kayan duk da baida tabbacin zata ci, bedroom É—insa ya shiga ya ajiye jakar laptop É—in shi sannan ya kwanta kan gadonshi, gaba É—aya ya rasa abin da yake yi masa daÉ—i, shi dai ya san ba zai iya barin musulunci ba ahalin yanzu haka kuma baya son fushin da mommy keyi dashi, wayar shi ya ciro daga aljihun gaban rigarsa ya lalubo no beloved ya kira,

Ina falon mama ina kallon wani Indian series a tashar zee world naga kiran sa, kallon na kashe na miƙe na koma cikin ɗakina na zauna bakin gado ina yi masa sallama,

“Baby yakike…….”

“lafiya lau Honey… Ya juma’a”

“Lafiya lau”

“Lafiya kuwa? Naji kamar akwai abin da yake damunka” na faÉ—a ina kishingiÉ—a a jikin gado na, shiru yayi na É—an wani lokaci yana sake jinjina kulawa ta a gareshi domin ina saurin gane yanayinsa na farin ciki ko baÆ™in ciki koda kuwa iya muryarsa naji,

“Babu abin da ke damuna kawai na kwanta ne kaina na ciwo kaÉ—an”

“ayya sorry ko dai fargabar aurence?” na faÉ—a cikin tsokana, dariya naji yayi kamar yadda na tsammata,

“Fargaba kamar wata ke…. Ni da nake alla alla lokacin yazo in samu abokiyar hirar dare… Kamar in janyo lokacin fa haka nake ji”

“Wacece abokiyar hirar daren taka? Ai na faÉ—a maka ni bacci zan yi in barka”

“Haba baby….. Ba zaki tausaya min ba”

“Ka san me Æ™awalli tace kwanaki?”

“a’a… Me tace?”

“wai in fara koya maka baccin tun daga yanzu, dan haka har baccin rana zaka rinÆ™a yi”

“zan so haka nima…. May be dama rashinki ne yasa nake kasa baccin amma idan kina nan na san zanyi”

“ai dolenka ma ka koyi bacci….”

“Haba baby….” ya sake faÉ—a yana murmushi,

“Ehh, da bacci da abinci zan rinÆ™a baka da yawa”

“kina son na Æ™ara Æ™iba kenan”

“ohh yeah”

“OK babu problem amma ni bana son nayi Æ™iba baby….. Haka ya isa”

“amma shine ni kake so in yi” na faÉ—a cikin shagwaÉ“a,

“kema kaÉ—an nake so kiyi amma idan kin yi da yawa babu matsala ina sonki a duk yanda kike”

“thank you Dear, I love you”

“I love you too”

A taÆ™aice dai mun jima muna hira sannan muka yi sallama. Har Samz ya gama weekend É—inshi ya koma mommy bata saurare shi ba sai Daddynshi ke kwantar masa da hankali cewar wata rana zata sauko shi dai kawai ya cigaba da yi mata biyayya, ya san zai yi wuya ta sauko musamman ma idan ta ji maganar aurenshi da ni wanda har yanzu ba a faÉ—a mata ba, sai da aka gama haÉ—a komai sannan Daddy ke sanar da ita wai next month bikin Muhammad Mu’allim, suma ne kawai bata yi ba nan ta shiga zage zage da yiwa daddy Allah ya isa wai ya raba ta da yaronta kuma ita É—anta bazai auri musulmi ba,

Kwana tayi tana bala’i ta hana Daddy bacci sai masifa take,

“yaro na… My beloved son shine yau zai auri Muslim ehhhhhh…… Over my dead body…… Samz zai auri Muslim ya fasa auren Felicia…. Impossible… This will not be possible… Allah ya isa tsakanina da ku….. An yiwa yaro na asiri”

Duk maganganun da take yi daddy yana jin ta amma ya rabu da ita da yake shi mutum ne mai haƙurin gaske sai dai ka cuce shi ba dai ya cuce ka ba, har asuba bata yi bacci ba gari yana wayewa ta shirya ta fita duk a tunaninsa church ta tafi, gidan aminiyarta mahaifiyar Felicia ta tafi wato madam comfort, tana zuwa ta fashe da kuka tana zayyana mata abunda ke faruwa,

“Maman Mary inada solution…. Dole na san ba a banza Samz ya zama haka ba, dan haka shawara ta shine muje inda za a raba shi da tsafin da aka yi masa a juya tunaninsa da Æ™waÆ™walwarsa ya manta da kowacce mace sai Felicia, nan da next month É—in sai ayi wedding ceremony É—insu ” na’am maman Mary tayi da shawarar madam comfort nan suka bazama suka rankaya suka tafi wurin bokansu wanda saida suka yi doguwar tafiya dan sai da suka manta da barin cikin gari tun suna wuce Æ´an Æ™auyuka da gidaje tsilla tsilla har ya zamana sai sai jeji, tun wayewar gari suke tafiya akan babur amma basu isa ga wannan boka ba sai la’asar sakaliya,

Madam comfort ce ta fara shiga cikin Æ´ar bukkar bayan ta jima tana yi wa boka bayani ta fito ta kira Maman Mary, tambayar ta boka yayi,

“Duk naji matsalolinki da damuwarki dama dalilin zuwanki nan…. Yanzu me kike so ayi masa?”

“Yawwa boka so nake a juya tunanin sa ya bar wannan sabon addinin da ya shiga ya dawo namu…. Sannan akwai wata yarinya da yake so zai aura amma ni ban san ta ba itama ina so a nisanta ta dashi a mantar dashi ita gaba É—aya yaji ta fita a ransa ya daina tunawa da ita ya dawo ya auri Æ´ar aminiyata Felicia……. ”

Wata ƙara boka yayi da kuwwa mai tsoratarwa ya shafa ƙoƙon dake gaban sa cike da ruwan tsafi sai ga hoton samz nan ya bayyana raɗau,

” Wannan ne? ”

” Ehh shine ” inji Madam comfort,

” To angama” boka ya basu tabbaci,

“Boka kar a cutar dashi kawai iya abin da na faÉ—a maka za ayi masa”, “babu matsala zuwa cikin dare zamu gama aikin mu lokacin aiki yafi tafiya daidai” kuÉ—i ta ajiye masa suka tashi suka sake kama hanyar gida.

Nidai yau tunda na tashi nake faÉ—uwar gaba barin ma lokacin sallar azahar amma koda na gayawa Anty wadda ta zo gida bayan ta haihu sai take cemin wai dama in dai biki ya kusa haka kowacce mace ke ji kawai dai in tsananta addu’a, addu’ar naketa yi acikin zuciya ta kome nake ina yin wannan addu’ar har magriba inda Samz ya kirani video call ganin sa nayi kamar marar lafiya shima yana zaune gefen titi………✍

*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*

*_Ummi Shatu_*

Post a Comment

0 Comments