Garin Dadi 27

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Garin Dadi 27


©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*GARIN DAÆŠI…..!*
PAID BOOK #500

_*NA*_

_*UMMI A’ISHA*_

*Wattpad:ummishatu*

 

27

*Ina kuke manyan mata Æ´an Æ™walisa ma’abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haÉ—aÉ—É—un Lagos lace wanda zaku iya samun É—inkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaÉ“inki, gefe É—aya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUÆŠI GIDA…..*

~~~Ƙurawa juna ido muka yi kamar yau ne muka fara ganin juna sai dai amma ni ba cikin idanuwansa nake kallo ba kunya bata barina in iya saka nawa idon cikin nasa,

“Mr man….. Ya kake?” na faÉ—a cikin tsokana,

“Baby….. Lafiya lau nake, kefa?” ya buÆ™ata yana sake kallo na,

“nima lafiya nake”

“ok naji daÉ—in jin hakan…. Yau saura kwana nawa ma bikinmu?”

“ni ban san saura kwana nawa ba, bana counting” na faÉ—a cikin shagwaÉ“ata da na saba yi masa ina turo baki,

“ni ina counting É—in ai, sai anyi magana kice kina sona bayan gashi nan bama kya É—okin zuwa kusa dani” shima ya faÉ—a cikin shagwaÉ“ar, dariya na Æ™yalÆ™yale da ita kafin nace,

“ashe dai kaima É—in shagwaÉ“aÉ“É“e ne ban sani ba….”

“Ehh kin koya min” ya faÉ—a yana lumshe idanuwansa,

“ni É—in na iya shagwaÉ“a ne?” na buÆ™ata nima ina gyara kwanciya ta a gefen gado na,

“Baby ai kin iya shagwaÉ“a….. Yanzu ki bani labarin yau me kika yi dan ban ganki ba throughout sai yanzu…….”

“yau babu abin da nayi sannan babu inda naje kawai kusan a kwance na wuni”

“Baki da lafiya?” ya buÆ™ata yana kallona,

“lafiya ta Lau kawai dai bana jin hayaniya ne yau É—innan….”

“same here my dear….. Nima yau É—innan ina jin jikina very weak….. I don’t know what’s happening to me…”

“Sorry….”

“Amma baby meyasa gaba É—aya ni dake muke jin yanayi iri É—aya?” jin tambayar da yayi min naji gabana ya tsinke ya faÉ—i domin nima abin da ke kai kawo araina kenan dan kamar ya shiga zuciya ta ya gani,duk da haka ban nuna masa ba sai nayi murmushin jan hankali nace,

” ni da kai ai abu É—ayane ko ka manta ne? Hatta jinin dake gudana ajikinmu iri É—aya ne, haka zuciyar dake bugawa a Æ™irjina kai ma itace ke bugawa a naka Æ™irjin… Kaga kuwa idan haka ne to ya zama dole mu rinÆ™a tsintar kanmu cikin yanayi guda” murmushi naga yayi tare da lumshe idanuwansa, a hankali naji ya furta,

“my clever baby….. You know what? Am eager naga munyi aure ina ganin ki kusa dani kina yimin irin waÉ—annan sweet sweet words É—in”

Rufe fuska ta nayi da hannuna guda É—aya cike da kunya,

“Yaushe zaka zo?” na tambaye shi bayan na buÉ—e fuskar tawa,

“kina nemana ne?”

“Ehh mana”

“to yaushe kike son ganina?” ya sake tambayata bayan ya miÆ™e daga zaunen da yake yana tafiya gefen titi,

“ko gobe ma….”

ÆŠan shiru yayi alamar tunani zuwa caan naji yace,

“banda gobe….. I have a lot of things da zanyi gobe but insha Allah next tomorrow zan zo Kano….”

“Me zan dafa maka?”

“komai ma baby….”

“zaka sake zuwa idan ka tafi?”

“no, sai munyi aure sannan zan zo”

“baka da zance sai na aure….. Aure dai aure dai”

“to me kike so in ambata wanda ya wuce wannan? Shine a raina yanzu”

Har ya ƙarasa masallacin unguwar su muna hira kuma wani abun mamaki yau gaba ɗaya daga ni har shi kamar bama son yin sallama da juna dan sai munyi sallama sai mu sake ɗauko wata sabuwar hirar, da haka har aka kira sallar isha nan ya shiga salla, nima tashi nayi nai sallar har lokacin jikina a wani sanyaye yake kamar an aiko min da saƙon mutuwa,

Sake kirana yayi misalin Æ™arfe 9 na dare yana sanar da ni ciwon kan dake damunsa addu’ar samun lafiya nayi masa sannan na Æ™ara da,

“wannan Hisnul Muslim É—in da na faÉ—a maka wanda ka É—auko a Play store ka duba shi da kyau duk wata addu’a da kake buÆ™ata insha Allah zaka samu aciki….”

“Baby ai ban iyaba…. Ki koya min”

“Babu matsala bari mu fara tun daga addu’ar farko…”

Hannu nasa na buÉ—e bed drawer É—ina na ciro littafin Hisnul Muslim É—ina na buÉ—e muka fara tun daga addu’ar farko, ina faÉ—a yana faÉ—a sannan kowacce addu’a sai nayi masa cikakken bayani akanta, har 12 muka kai sannan nace yayi bacci haka ya É—an huta, sallama muka yi yace zai yi baccin wai amma idan 3 tayi na tashe shi tunda nace ni ba bacci zanyi ba karatu zanyi, saida na fara yin salloli na nayi raka’a takwas sannan na fara karatun littafi mai tsarki, har 3 na kai idona biyu bayan na idar ina shirin kwanciya sai ga kiran Samz,

“Yanzu nake shirin kiran ka fa”

“Na tashi….. Nayi wani mafarki ne”

“Kayi addu’a?”

“Nayi”

“Allah yasa ya zama alkhairi”

Baccina na kwanta na shaÆ™a cikin kwanciyar hankali shi kuma samz ya kwana yana salla har asuba, washe gari da matsanancin zazzabi ya tashi da ciwon kai, tun yana iya amsa waya har yazo baya iyawa, ai hankali na idan yayi dubu sai da ya tashi, ji nayi kamar in yi tsuntsuwa in tafi Abuja in je in kula dashi, sai yau naji da ace zan iya janyo ranar bikin mu da na janyota ko dan in bashi cikakkiyar kulawa domin tun ina iya samun wayar tashi har ta kai ta kawo idan na kira sai injita akashe, sai zuwa dare sannan naji ta shiga kuma nan É—inma ba shine ya É—aga wayar ba wani friend É—in shi ne Ahmad wanda suke yin aiki tare, shine yake yimin bayanin wai dama Samz É—in yana da typhoid soo yanzun ma typhoid É—in nasa ne ya tashi, nidai ban samu jin muryarsa ba sai da gari ya waye har lokacin yana asibiti ba a sallameshi ba, babu abin da ya sauya ko ya canja daga kulawar da muke baiwa junanmu sai dai zuwa Kanon da bai yi ba kenan kamar yadda yaci buri rashin lafiya yayi ta yi har tsawon wasu kwanaki, a É“angare É—aya kuma ya ware maÆ™udan kuÉ—i ya bawa matar uncle É—insa wadda ita ce ke haÉ—a lefe na ba lefe kaÉ—ai ba kusan duk wani shirye shirye ma wanda ya shafi bikinmu a gidan uncle É—insa ake yi dan hatta gidan da zamu zauna ma uncle É—insa ya bawa wakilci akan ya samo mana gida mai daraja a Kano acikin manyan unguwanni wai tunda nace a Kano zan zauna, cikin lokaci Æ™anÆ™ani aka samu wani lafiyayyen gida a unguwar hotoro, gidane flat mai mutuÆ™ar kyau da aji sabo fil ban san adadin miliyoyin da ya salwantar ba wurin mallakar gidan amma bai sanar dani ba har yanzu saboda yana cikin hali na rashin lafiya, ganin rashin lafiyar tasa ta tsananta ya sanya mahaifinsu da Æ™annenshi tafiya wurinsa amma banda mommy wadda tace ko mutuwa zai yi yaje yaita mutuwar ita babu ruwanta, nima na so in je in duba shi amma Æ´an gidanmu basu barni ba sai iya su kaÉ—ai ne suka je, anty kuwa kullum daga gidan ta ake kai musu abinci asibitin da suke, ga biki nata Æ™aratowa ga ango na kwance yana fama da kansa, ni kaina ni É—inma bani da maraba da marar lafiyar domin kullum cikin damuwa da tunani nake gashi kullum addu’a ta kar Allah yasa in yi mafarki da ya warke saboda ance idan kayi mafarki marar lafiya ya warke to mutuwa yayi, duk abin da baka so sau da yawa shine yake faruwa, ina cikin bacci wanda ya É—auke ni mintuna kaÉ—an da suka wuce nayi mafarki wai Samz ya rasu ai a wani hargitse na tashi hankalina a dugunzume, fuskata sharkaf hawaye sakamakon kukan da nasha cikin mafarkin, wayata na É—auka jikina na rawa na soma kiran wayarsa……..✍

 

*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*

_*Ummi Shatu*_

Post a Comment

0 Comments