Garin Dadi 29

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Garin Dadi 29


©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
_(Home of expert & perfect Writers)_

 

*GARIN DAÆŠI…..!*

 

*_NA_*

_*UMMI A’ISHA*_

PAID BOOK #500

*Wattpad:ummishatu*

29

*Ina kuke manyan mata Æ´an Æ™walisa ma’abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haÉ—aÉ—É—un Lagos lace wanda zaku iya samun É—inkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaÉ“inki, gefe É—aya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUÆŠI GIDA…..*

~~~Cikin farin ciki da ɗoki nake shaƙar iskar garina kuma tushena wato Kanon dabo tarin Allah, sai murna nake yi wadda ban san ko ta mecece ba amma ni dai na san ba murnar aure bace,

Lokacin da naje gida tun daga ƙofar gida na san anyi gyara na musamman a gidan domin gashi nan ya sha sabon fenti ko ina an gyareshi tsaf, ƙawalli tana gidan dan haka rungume juna muka yi muna tsalle yaya Abdul Hakim da fitowarsa kenan daga sashen Annie ya bimu da harara wadda ba mu san ma yana yi ba, sakina tayi tana ƙare min kallo sakamakon canjawar da nayi nai ƙiba da haske saboda supplements din da Anty ke bani na gyaran jiki da sauran abubuwa ita kanta bata san yawan kuɗin da ta kashe ba wurin gyara ni tun daga kan su dilke, magungunan infection, na gyara fata da dai sauran su,

“Tabdijam…… Samz zai kwashi lagwada….” ta faÉ—a a hankali ta yadda wani ba zai jiyo ta ba, harararta nayi nace “ya ranki”

“WataÆ™ila daren ranar da aka kaiki ki samu ciki Æ™awalli…..”

“Ta Allah ba taki ba Æ™awalli……insha Allah sai bayan shekara biyu zan haihu”

“a wannan samz É—in naki zaki kai shekara biyu baki haihu ba?”

Kallon yanda ta riÆ™e haÉ“a kamar wata tsohuwa nayi dariya nayi nai gaba abina ta biyo baya na, gani nayi gaba É—aya Æ´an gidanmu sun zama busy dan ban samu mama agida ba wai sun fita kasuwa ita da Anty Salaha sai iya Annie kaÉ—ai da sauran abokan arziÆ™i wadanda suka zo ganin kaya dan har yau ba agama zuwa kallo ba, ni dai ko ta kan kayan ban bi ba sai wadanda aka dinko min su na dudduba ciki harda wanda zanyi fitar biki dasu na kamu da dinner, Æ™awalli ke tsara yanda shigar tawa zata kasance, ni dai duk jikina yayi la’asar da ganin dagaske gidan zan bari in tafi gidan samz ada babu abin da nake so irin maganar aure na dashi amma ahalin yanzu idan Æ™awalli tayi min faÉ—a ma muke yi ita kuma tunda ta gane shikenan bata da aiki sai tsokana ta, gaba É—aya ji nake auren ya fice min arai kamar a sake Æ™ara watanni amma na san hakan ba zata taÉ“a faruwa ba, Æ™awalli na kalla dake ta haÉ—a min kaya na wuri É—aya ina daure da towel da hijabi a jikina fitowata kenan daga wanka,

“yaushe angon zai shigo ne?”

“oho masa ni na sani ne” na bata amsa ina Æ™okarin zama gefen gado, dariya naji ta fashe da ita,

“ohh Allah me iko wai ashe dama zanga widat haka? Ashe wannan ranar zata zo da zata rinÆ™a jin tsoron Samz”

“Wallahi ji nake inama a É—aga…..” na faÉ—a Æ™walla na taruwa acikin idanuwa na dan duk da ina sonsa yanzu ji nake bana son haÉ—uwarmu kwana kusa balle har mu zauna inuwa É—aya,

“ai idan aka É—aga ina jin sai an baki gado a asibiti…. Mutumin da kike ta jinya a kansa yanzu kuma kice wai so kike a É—aga….”

Ban sake tanka mata ba kawai na fara kuka, lallashi na ta fara tana cemin to kuma menene abin kuka har itama ta fara a haka anty ta shigo ta same mu,

” kin jimin yara da shashanci kunzo kun zauna kun Æ™ule a É—aki kuna kuka kamar waÉ—anda aka yiwa mutuwa…. Dan Allah ni karku É“ata min lokaci ungo ku zaÉ“a…..”

Wayarta ta miÆ™o mana, decorations ne kala kala take son mu zaÉ“i kalar wanda za ayi, Æ™awalli ce ta zaÉ“i wani kamar na gargajiya gargajiya amma yayi bala’in kyau, karÉ“a anty tayi tana cewa,

” Ranar kamun wanne kaya ma zata saka? Ungo ku zaÉ“i na dinner ”

“Golden ne Anty” Æ™awalli ta bata amsa, sake zaÉ“ar na dinner É—in tayi ta miÆ™a mata wayarta ta fice ta barmu kamar yadda tazo ta same mu, kafin kace mi har magriba tayi wanda hakan ke sake tada min da hankali,

Bayan tafiyar Æ™awalli É—akin mama naje muka zauna tana ta haÉ—a kan kayan da ta siyo na amfanin kitchen wanda za a tafi dasu jere gobe laraba ranar Alhamis za ayi kamu juma’a dinner asabar kuma za a É—aura aure ayi yini akai amarya É—akinta, duk ji nake kamar inyita kuka har sai an fasa bikin nan yanzu Ala basshi nan gaba sai ayi, shi kansa samz É—in yanzu bana doguwar hira dashi dan gaba É—aya haushinsa nake ji daga ya kirani zan tambayi menene sannan ina gama bashi amsa zan kashe wayata, ba wai laifi yayi min ko daina sonshi nayi ba a’a haka kawai nake jin bana son kusancinmu dashi, duk da hakan da nake yi masa shi baya zuciya ya kan kirani kamar yadda ya saba, dan ko yanzu da na zo kwanciya saida ya kirani amma nace bacci nake ji, cewa yayi to shikenan in kwanta in yi, kashe wayar nayi gaba É—aya ina ta juye juye nama kasa baccin gaba É—aya, daga Æ™arshe hijabi na nasa na fita, sashen Annie na shiga na buÉ—e É—akin bishra wacce ke kwance tana bacci sakamakon zirga zirgar da itama tasha yau, kusa da ita naje na kwanta naja bargo na lulluÉ“a sai hawaye, na jima ina zubar da hawaye kafin bacci ya É—auke ni wanda bani na tashi ba sai bayan asuba irin Æ™arfe 6 É—in nan wannan É—inma anty ce ta shigo da ban san ranar tashin mu ba daga ni har Bishran, É—akina na koma nayi wanka a gurguje bayan nayi salla, sama sama nayi breakfast sannan na tafi gidan Æ™unshi nida Anty wadda tayi dropping É—ina sannan ta wuce kasuwa ta can kuma zata wuce gidana, sai bayan da aka gama min Æ™unshin sannan Æ™awalli ta sameni a gidan,

“RangaÉ—i…. Amarya komai naki na dabanne… Gidanki mai kyau wallahi….”

Shiru nayi mata dan bana son jin zancen gidan nan hankalina tashi yake idan naji an ambaceshi, Æ™unshin aka yi mata itama amma iya baÆ™i saÉ“anin nawa da aka haÉ—a harda ja na seletif, bayan azahar muka bar gidan Æ™unshin muka koma gida yau dai nafi ganin gudun yinin fiye da na kowacce rana dan kafin Æ™iftawa da bismillah har magriba sunyi kuma sai lokacin Æ´an jere suka dawo kowa yana santin gidana, daren ranar kasa bacci nayi dan haka na tashi na koma cikin su Anty waÉ—anda ke falon mama suna aiki, kan dugowar kujera na kwanta anan nai bacci dandanan kuma naji gari ya waye kuma a ranar aka fara gudanar da biki, shi dai ango bai zo ba yace sai ranar Juma’a zai dira wanda ni hakan ma yafi min.

Tunda garin Allah ya waye bayan na dawo daga gyaran gashi ake kwaskware ni ana sake kwatalle ni dan wata me gyaran jiki ta musamman Anty ta kirawo wacce tazo ta sake gyara min fatata gyaran da yafi na baya sannan ta turare min jikina da wani turare wanda ya sha haÉ—i na musamman nan take fatata ta kama Æ™amshin gam ta riÆ™e sai zuwa yamma na samu kaina hannun matar nan bayan ta sakani nayi wanka da wani ruwan turare, me kwalliya ce ta zo itama ta fara nata aikin babu jimawa kamanni na suka canja na tashi daga widat É—in da aka sani na koma kamar wata balarabiya ko Æ´ar India, kayana milk colour ne amma an sirka da golden haka takalmi da yar jakar da na riÆ™e da gwaggoro na duk golden, sai bayan da aka gama É—aukata hotuna sannan aka sakani a mota muka nufi wurin kamu dan Anty sai waya take iyowa wai mutane suna jirana, faÉ—in irin kyawun da nayi da irin kuÉ—in da aka kashe É“ata bakine da É“ata lokaci, anci an sha haka kuma an sha hotuna, dangin ango suma sun zo matar uncle É—inshi Anty Amina da wasu mata su biyar sai bayan da aka gama kamu sannan suka tafi, duk na gama gajiya da zaman nan da tashi, bamu muka bar hall É—innan ba sai 8 saura shiyasa a mutuÆ™ar gajiye na koma gida, ranar kam da wuri nayi bacci. Washe gari ango ya baÆ™unci Kano dan tun 1 ya kirani yake sanar dani ya sauka shida abokinsa Ahmad dan anan ma suka yi sallar juma’a, kamar jiya yauma wuni aka yi ana hidimtawa fatata har tsawon wani lokaci ga uban Æ™amshi da ake manna mata babu Æ™aƙƙautawa, tun kafin magriba na isa gidan kwalliya nida Æ™awalli amma can ta tafi ta barni, har bayan ishah aka kai ana yimin kwalliya salla ce kaÉ—ai ke tadani, kwalliyar yau ai har tafi ta jiya kyau da matsayi domin yau ne na fito a asalin bride, Æ™amshi kuwa ai ba a ma magana dan ta ko ina tashi yake, misalin Æ™arfe 8 daidai suka zo É—aukata, babu kowa atare dasu daga shi sai abokinsa, komai nawa blue sai É—an ratsin silver kaÉ—an saboda takalmi na da pose É—ina duk silver colour ne da sarka da earrings harda zobuna da agogo duk silver, a hankali nake tafiya saboda tsinin takalmin Æ™afata gashi rigar ta baya tana jan Æ™asa, ganin ina Æ™oÆ™arin fitowa ya buÉ—e motar ya fito sai lokacin na ganshi bayan tsawon kwanaki rabona da shi, shima blue É—in shadda ya saka mai kyau da tsada harda hula itama blue dama ba Æ™aramin kyau manyan kayan ke yi masa ba to kyawun yau har yafi na kullum,

“Baby….” yace dani bayan ya Æ™araso kusa dani,

“zo ka riÆ™e min rigata ta baya dan Allah”

Matsowa yayi dab dani nan muka shaƙi ƙamshin juna,

“why not in É—auke ki maimakon riÆ™e miki riga ai kamar zai fi ko….”

Tun kafin in bashi amsa naji ya tarairaye ni ya ɗaukenin zuwa inda motar su take, bani da zaɓi illa in lafe cikin jikinsa,

“Ya biki? Kin gaji ko?”

Kai na ɗaga masa cikin shagwaɓa ina ɓata fuska kamar zanyi kuka,

“Ayya… Am soo sorry baby”

“Ahmad buÉ—e mana Æ™ofar nan pls”

Sai lokacin naji kunya ta kama ni da naga abokin shi ya fito ya buɗe mana ƙofar baya, ji nayi kamar inye me dan kunya, sakani yayi ya rufe ƙofar sannan ya zagayo ta ɗaya ɓarin shima ya shigo, hannuwana ya kamo cikin nasa masu mutuƙar ɗumi da laushi wannan dalilinne yasa sau tari idan ya riƙe hannuna bana iya ƙwacewa hannunshi is very soft and warm, jana jikinshi yayi yana raɗa min,

“matso muyi sirri kar Ahmad yaji mu…”

Banyi magana ba illa kallon fuskar shi da nayi wadda tasha gyara tun daga sajenshi zuwa gemunsa, rungume ni yayi sosai a jikinsa yana yimin raÉ—a,

“kinyi kyau baby…. You look… Just amazing….. Let me snap u” ya faÉ—a yana ciro iPhone É—inshi daga aljihu ya É—aukeni sannan yayi mana nida shi,

“kaima kayi kyau” na faÉ—a murya ta na rawa, hannunnshi É—aya na riÆ™e da nawa É—ayan kuma na gadon bayana yana wasa da zip É—in rigata cikin wayo da dabara yake sauke zip É—in bai san duk ina ankare dashi ba, wuya na zai yiwa kiss na yi saurin toshe bakin sa da hannu na, da ido yake tambaya ta wai why? RaÉ—a masa nayi,

“Zaka karya alÆ™awarinmu…. We promised ourselves sai bayan munyi aure”

Kanshi ya ɗaga sama sannan ya ƙwace bakin sa daga tsohewar da hannu na yayi masa,

“amma ai ba zaki hanani wannan ba….” ya faÉ—a yana sauke zip É—in rigata a hankali ta yadda Ahmad ba zai ji mu ba,

“ni dai a’a wallahi… Is part of our promised” na faÉ—a ina riÆ™e hannunsa,

“Oh my God…” ya faÉ—a yana kallo na da shanyanyun idanuwansa wanda yau suka fi kullum shanyewa, saukar da nawa nayi Æ™asa daga cikin nasa, gadon baya na yake shafawa yana faÉ—in,

“please baby…..”

“NaÆ™i wayon” na faÉ—a cikin raina ina maÆ™ale masa kafaÉ—a, duk yadda yaso ya min wayo Æ™in yarda nayi sai wani marairaicewa yake yi yana lumshe min ido amma naÆ™i furr tunda har yanzu ba a É—aura mana aure ba sai zuwa gobe, Æ™yaleni yayi kuma yayi shiru ya daina roÆ™o na may be fushi yayi wanda sam hakan bai É—aÉ—ani da Æ™asa ba, kuma duk da ya daina kulani hakan bai sa na bar jikinsa ba dan kamar mage haka nake idan na samu jikinsa, kaina kan kafaÉ—arsa na zagayeshi da hannuwana duka biyu na maÆ™ale, bai Æ™ara kulani ba sai hirarsu da suke yi shida abokinsa da kuma waya da yake amsawa jifa jifa a haka har muka Æ™arasa event center É—in da dandazon Æ´an uwa da abokan arziÆ™i keta dakon zuwan mu……….✍

*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*

_*Ummi Shatu*_

Post a Comment

0 Comments