Garin Dadi 30

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Garin Dadi 30


©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
_(Home of expert & perfect Writers)_

*GARIN DAÆŠI…..!*

*_NA_*

*_UMMI A’ISHA_*

PAID BOOK #500

*Wattpad:ummishatu*

30

*Ina kuke manyan mata Æ´an Æ™walisa ma’abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haÉ—aÉ—É—un Lagos lace wanda zaku iya samun É—inkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaÉ“inki, gefe É—aya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUÆŠI GIDA…..*

~~~Wani farin ciki ne ke faman É—awainiya dani ina jin rayuwata da gangar jikina kamar tana tafiya akan iska, da zarar na tuna cewa nida samz gobe zamu zama ma’aurata kuma mallakin juna sai inji Æ™afafuwana tamkar baza su iya É—aukana ba saboda tsantsar shauÆ™i da tsananin É—oki,

Hannayena na saka na sake maƙale shi bayan na ɗaga idanuwana ina kallon fuskarsa, zaune nake gefenshi amma ina cikin jikinsa nasa hannaye na zagaye shi kaina bisa kafaɗarsa, wata irin zazzafar soyayyarsa nake ji wadda ban taɓa jiba dan ji nake kamar zan koma cikin cikinsa dan so, kallo na shima yayi muka haɗa ido,

“ni kika yima rowa ko?” ya faÉ—a yana É—an cije lips É—in shi na Æ™asa, farrr nayi masa da idanuwa na kafin nayi masa gwalo, goshinsa ya haÉ—a da nawa sannan ya bani amsa da,

“zan rama ne…. Ki gama naki iya yau kaÉ—ai gareki…. Ni kuwa daga gobe nawa turn É—in zai fara….. Zaki yi bayani”

Shagwaɓe fuska nayi na sake narkewa acikin jikinsa,

“nidai a’a”

“nima a’a” ya faÉ—a cikin kwaikwayon muryata, dariya muka yi gaba É—aya daga ni har shi,

“É—an gyara min zip É—in rigata….” nace dashi jin alamun mun Æ™araso event center É—in,saida ya turo baki kamar yadda nake yi masa sannan ya zuge min zip É—in yana hararata cikin shauÆ™in so,Æ´ar pose É—ita ya buÉ—e ya Æ™ara min kuÉ—i Æ´an É—ari biyar biyar sabbi fil wanda ya ciro daga cikin aljihunsa.

A tare muka jera bayan mun fito daga cikin hall ɗin muna riƙe da hannun juna kuma tun daga nan aka fara haskamu da camera, haske kake gani ko ta ina an zagaye mu ana yimana hotuna,

“Masha Allah…. My favorite couple” Æ™awalli ta faÉ—a bayan ta tsaya kusa dani dan a É—auke mu tare, mun jima awaje kafin aka yi mana jagora zuwa ciki kuma har lokacin hannuna yana saÆ™ale cikin nasa, har wurin zaman mu aka rakamu sannan aka fara gabatar da abubuwan, addu’a aka fara yi daga nan aka yi jawabin maraba da É—an taÆ™aitaccen tarihin kowannenmu daga bisani aka fara cashewa bayan an kira amarya da ango,

Anci an sha an raƙashe haka kuma an zubar da kuɗi babu laifi, misalin ƙarfe 10:30 aka tashi, yanzu kam ba tare dashi zamu koma ba, ina katarin anty wanda hakan ba ƙaramin daɗi yayi min ba dan nasan wataƙila idan dashi zamu koma ya nemi yimin abun neman magana daga ƙarshe muyi faɗa idan na bijire,

Muna komawa gida nayi wanka nabi lafiyar gado duk da ina ɗan jin yunwa dan yanzu bana cin abinci sosai. Kasancewar na gaji bacci na nayi haiƙan har sai da gari ya waye sannan na tashi, tunda na tashi kuma da zarar na tuna yau za a ɗaura min aure a kaini gidan miji sai inji gabana ya tsinke ya faɗi haka dai nake ta daurewa nayi wanka aka yimin kwalliya nayi shiga ta cikin wani tsadadden leshi wanda anty ta ɗinka min dark purple, da yake yau ake wuni shiyasa gidan namu cike yake taf da ƴan uwa da abokan arziƙi a nata cashewa da masu kiɗan ƙwaryar da aka ɗauko, wayata a kashe take banma san inda take ba, anty ce ta sakani a ɗaki ta bani wani farfesun kaza kuma ta sakani a gaba sai na cinye, idan ban manta ba irin wannan naman naci yafi sau uku kuma duk babu daɗi dan har ji na nake kamar zan amayo dashi, abubuwan da anty ta ɗura min acikin cikin nan nawa sun fi gaban lissafawa duk da sunan maganin infection da na gyaran jiki, haka dai na rinƙa yaga ina ci ina yatsine fuska da haka har na cinye sannan ta haɗa min maltina da madara na sha ƙawalli sai gwalo take yimin idan ta faki idon anty, bayan na gama ci mun fito muka ji alamun dawowar ƴan ɗaurin aure nan na sake jin jikina yayi sanyi shikenan aure ya ɗauru, ban sake gaskata hakan ba sai da yayuna suka shigo suna bada labarin an ɗaura akan sadaki naira dubu ɗari, kamar zanyi kuka amma anty tace idan na kuskura nayi hawaye nida ita ne, sake shiryani aka yi muka fita wurin angwaye, ya sha farar shadda ƙal da baƙin glasses a idonshi yayi kyau har ya gaji, hotuna aka yiyyi mana sannan suka tafi mu kuma muka koma gida kafin kace me har anfara maganar tafiya kaini, ji nayi kamar in gudu wani wurin in ɓoye amma babu dama domin duk inda nayi ƙawalli na biye dani, ita ta rakani wurin Abba ma yayi min nasiha irinta uba da ƴa sannan su mama, faɗan da suka yimin shine ya saka ni kuka kamar zanyi hauka, itama Anty nata faɗan tayi min kamar haka,

“To widat gashi dai Allah ya kawo mu ya nuna mana, rana bata Æ™arya, yau zaki tafi gidan mijin ki, to wallahi kar naji labarin Æ™azanta da rashin gyara, sannan banda raina miji banda rashin kunya, haka Æ´an uwansa kisa aranki baza su taÉ“a sonki ba… Hakan shi zai sa ki zauna lafiya kuma zuciyar ki ta huta, dan duk tsanar da zasu nuna miki dama kin san hakan zai biyo baya, amma idan kika sawa ranki dole sai sun soki to zaki tabbata cikin damuwa dan baza su soki ba saboda kullum kallon wadda ta raba su da É—an uwansu ta fitar dashi daga addininsu zasu yi ta yi miki amma Hakan kar ya hanaki kyautata musu idan sun zo gareki, kiyi musu dukkan wani nau’i na kyautatawa musamman ma mahaifiyarsa karki yarda ki wulakantata dan ta nuna bata sonki, ki tuna itace ta kawo mijin ki duniya tayi É—awainiya dashi har ya zama abin da ya zama yanzu, kiyi mata biyayya iya iyawarki kuma ki girmama ta ki bata matsayin uwa…. Allah ya baku zaman lafiya ”

Duk faɗan da iyaye suka yi min na anty ne yafi tsaya min arai da naji tayi maganar ƴan uwan samz ba zasu soni ba, tabbas nima na fahimci hakan domin babu wadda ya taɓa nemana acikin ƴan uwansa ko danginsa, anty Amina ce kaɗai matar uncle ɗinsa da wasu dangin su ke fafutukar zuwa neman aure na dan yanzun ma sune suka zo ɗaukar amarya,

A can gidan su samz kuwa mahaifiyarsa bata san abin da ke gudana ba dan daddy baya shiga shirginta kuma baya sanar da ita komai akan batun auren mu da Samz, sai yau ta sani da taga Abdullahi ƙaninsa yayi shiga da manyan kaya nan take tambayarsa ina zai je? Amsa ya bata da wai ɗaurin auren Samz ai tunda taji haka ta yanke jiki ta faɗi bata sake sanin inda kanta yake ba saboda dama tana da lalurar hawan jini, asibiti aka kai ta aka bata gado amma samz kwata kwata bai san hakan yana faruwa ba dan babu wanda ya faɗa masa kuma ko auren nasa ma daddy ne ya gargaɗeshi akan ya ɓoye mata karya kuskura ya sanar da ita idan ba haka ba hanawa zata yi zata bi bokaye a ɓata lamarin wannan dalilin ne yasa bai sanar da ita ba.

Bayan sallar magriba aka kaini gidana dake unguwar hotoro, kuma ana kaini kowa ya kama gabansa aka watse aka barni inata shaƙar kuka na, ƙawalli kuwa saida ta gama yimin rashin mutuncinta kafin ta tafi daga baya kuma itama kukan tayi sannan ta tafi, ganin zaman shiru yana neman damuna yasa nayi alwala nayi sallolin dake kaina wato magriba da isha, bayan na idar na koma kan gado na takure ina kallon uban dukiyar da aka kashe min acikin ɗakina wanda komai silver colour, shi kuwa ango bai shigo ba sai bayan sallar ishah kuma shi kaɗai babu ɗan rakiya dama iya Ahmad ne abokin nasa to shi kuma tun bayan ɗaurin aure ya koma Abuja,

A kusa dani ya zauna yana ƙoƙarin buɗe fuskata,

“Kuka kike yi ne?” ya buÆ™ata cikin tsokana, shiru nayi na sunkuyar da kaina,

“Ahmad yace akwai salla da zamuyi ta nafila raka’a biyu ko? Muyi sai ki ci abinci ki kwanta…. Zan bar ki ki huta yau”

Shiru nayi nai tsit kamar ruwa ya cinye ni, hannuna ya kama cikin nashi,

“Kin jima kina tambayar wacce irin rashin lafiya nake yi idan banda lafiya amma bana faÉ—a miki ko? To yau zan faÉ—a miki dan kece maganin…. Ciwon ciki ne kuma Dr ya tabbatar min da maganin yana wurin ki soo sau nawa zaki rinÆ™a bani? Da safe da yamma, ko da safe da rana da yamma da kuma dare? ” ai ban san lokacin da na kalleshi ba a tsorace, shi É—inma ni yake kallo, murmushi naga yayi ya miÆ™e tsaye, nikam ji nayi kunyar duniya ta taru ta lulluÉ“eni kamar Æ™asa ta buÉ—e in shige, gaskiya sai yau na yarda namiji bai da kunya, alwala ya É—auro muka yi salla raka’a biyu muka karanta abin da ya sawwaÆ™a cikin Littafi mai tsarki muka yi addu’a, abin da ya shigo dashi ya É—auko mana, gasasshiyar kaza ce sai fresh milk da fruits, kan cinyarsa ya É—ora ni yayi ta yimin É—ura har sai da ya cika min ciki dan wai ya fahimci ban ci abinci ba, wanka yace in je inyi nace nayi, bai takura min ba shi ya rage kayan jikinsa ya shiga daga shi sai boxer, sai bayan da ya shiga sannan nayi hanzarin saka kayan bacci riga da wando na shige cikin bargo, shima bai wani jima sosai ba ya fito É—aure da towel, leÆ™ensa nake yi ta yadda ba zai gane ba ina kallonsa ya shafa turare yasa kayan baccin sa baccin sa wando iya rabin cinyarsa da riga armless, kan gadon ya nufo nan nayi gaggawar rufe idanuwa na, gaba É—aya a sanyaye yake sakamakon wayar da Æ™anwarshi Mary tayi masa É—azu É—azun nan tana sanar dashi rashin lafiyar mommy wadda ke kwance a asibiti wannan abun da yaji shine musabbabin tashin hankalinsa kawai yana dannewa ne yana nuna min he’s ok. A hankali ya hawo kan gadon ya kwanta gefena wanda hakan sai da naji gabana ya faÉ—i, wayarshi ya kashe sannan ya ajiyeta kan bedside drawer kusa da tawa,

“Baby…. Yau rowa ta Æ™are ko?” yace dani yana Æ™oÆ™arin jawoni jikinsa da hannayensa masu taushi, ban Æ™iba na shige cikin jikinsa nayi pillow da Æ™irjinsa,

“kina jin bacci?”

“uhmm” na bashi amsa,

“yau baki ya mutu Babu magana? “Ya faÉ—a yana shafa gadon bayana a hankali zuwa can naji yana É“alle botiran jikin rigar tawa,

“zaki fi jin daÉ—in bacci a haka” ya raÉ—a min bayan ya saÉ“ule rigar daga jikina, manna ni yayi a jikinsa bayan shima ya cire tashi rigar, duk da ina cikin kiÉ—ima tare da É—imuwa hakan bai hanani jin daÉ—in É—umin jikinsa ba dan kamar me zazzabi haka naji jikinsa,

“baka da lafiya ne?” na tambayeshi bayan na É—aga kaina na kalleshi acikin duhun da muke kwance,

“a’a lafiya nake….. Me ya faru?”

“naji jikin ka ne kamar da zafi”

“a’a haka temperature É—in jikina yake normally…..”

“kuma kaje hospital?”

“me zai kaini hospital alhali lafiya ta Æ™alau”

Murmushi nayi na mayar da kaina na kwantar araina ina tunanin dalilin da yasa ya iya barina daren yau, tuno tsokanar da Ƙawalli ta rinÆ™a yimin É—azu kafin ta tafi nayi, sake maÆ™aleshi nayi tsam ina shaÆ™ar Æ™amshin jikinsa, ina jinsa hannunsa yaÆ™i tsayawa wuri guda a jikina ya taÉ“a can ya taÉ“a can da haka har ya isa inda ya jima yana kwaÉ—ayin zuwa, na san dalilinsa na auna Æ™irjina saboda dab da lokacin bikin mu yake cemin wai matar uncle É—insa ta haÉ—o lefenmu yaje gani wai yaga ta saka manyan braziers wanda ko haihuwa nayi ba lallai su yi min daidai ba nikuma nace wallahi in dai wanda na ganine zasu yimin amma yace Æ™arya nake wai ni É—in nawa nake shi so yake ma ya samomin cream in rinÆ™a shafawa ko zan ciko, tsokana iri iri babu wadda bai yimin ba sai rabuwa nayi dashi, sai da yagama ganin Æ™waÆ™waf É—in shi sannan muka yi addu’a tare, wani bacci mai daÉ—i ne yayi awon gaba dani jina a alÆ™ayyar da ban taÉ“a samun kaina aciki ba………….✍

Asuba ta gari Widsamz

*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*

 

*_Ummi Shatu_*

Post a Comment

0 Comments