Garin Dadi 33

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Garin Dadi 33


©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
_(Home of experts & perfect Writers)_

 

*GARIN DAÆŠI….!*

_*NA*_

_*UMMI A’ISHA*_

*Wattpad:ummishatu*

{33}

PAID Book #500

*Ina kuke manyan mata Æ´an Æ™walisa ma’abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haÉ—aÉ—É—un Lagos lace wanda zaku iya samun É—inkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaÉ“inki, gefe É—aya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUÆŠI GIDA…..*

~~~Koda na koma ciki samu nayi wayata na rangajin neman É—auki na, cikin hanzari na É—auka nan naga shine yake kira, cikin bedroom É—ina na wuce ina É—aga wayar kuma har lokacin hawaye basu bar fita daga idanuwana ba,

“my baby…… Pls stop crying mana… Haba” ya faÉ—a cikin lanÆ™wasa murya, kwanciya nayi nai lamo ina sauraren tausashasshiyar muryarsa mai kama da zuma wurin zaÆ™i,

“uhmm na manta before in tafi…. Koda yake ma bari za muyi video call anjima”

“Allah ya kiyaye hanya, I love you”

“I love you too baby”

Sai da ya tabbatar da ya kwantar min da hankali na daina kuka sannan muka yi sallama lokacin har ya isa tasha ya samu mota, falo na koma wurin Bishra bayan na tura masa text massage kuma ina gama tura masa na kashe wayata dan tsokana nayi kuma na san zai kira.
***
Bayan sallar magriba ya isa gida, bai samu kowa a gidan ba sai iya daddy domin su mommy sun tafi church, zama yayi suka gaisa da daddy suka ɗan taɓa hira wadda mafi yawan hirar akan halayyar mommy ne wacce har yanzu ta kasa saduda kullum cikin rikici take da neman tashin hankali,

“Daddy dan Allah ka cigaba da haÆ™uri da halin mommy kar ka É—auki mataki akan ta…. Daddy bazan so a kaina mommy ta samu matsala da kai ba” Samz ya faÉ—a kansa a Æ™asa fuskarsa É—auke da damuwa,

“Ka kwantar da hankalinka babu abin da zai faru insha Allah, ai na saba da halin mahaifiyarku…… A gaskiya ba kuyi sa’ar uwa ba, ku yafe min ban samar muku uwa ta gari ba Muhammad”

Jin maganar daddy yayi batai masa daɗi ba duk da yasan mommy ba uwa ta gari bace amma da daddy ya kira ta da wannan sunan sai da yaji wani iri, har lokacin sallar ishah suna tare da daddy yana sake yi masa nasiha akan ya kula dani kuma ya riƙeni amana saboda iyayena dani kaina mun cancanci halacci, bayan sun dawo daga salla ya wuce ɗakinsa, wanka ya fara yi bayan ya fito ya kira wayata wadda nima ɗin tun ɗazu nake kiran sa dan inji ko ya sauka gida lafiya amma network bai barni na sameshi ba wai is not reachable,

Muna zaune a falo nida Bishra muna kallon wani Indian film a tashar zee world naga kiransa, tashi nayi na shige cikin bedroom sannan na É—auki kiran da yake video call ne,

“Baby…. What are you doing?”

Shagwaɓe fuska nayi kafin nace dashi,

“tun É—azu nake kiranka amma ban same ka ba, me ya faru?”

“sorry baby…. Nima i wanted to call you, muna tare da daddy ne”

“Ya ka samu mutanen gida?”

“Duk suna lafiya” ya faÉ—a cikin harshen hausa,

“ya jikin mommy?” na sake tambayarsa,

“Ta samu sauÆ™i sosai”

“A gaida ta”

“zata ji….., me kika ce É—azu?”

Fuskata na rufe ina dariya, dariyar shima yayi sannan naga ya gyara zamanshi ya jingina bayanshi da gado,

“Ki bari anjima zan kiraki muyi hira, yanzu zan je wurin su mommy…… Kin ci abinci ko?”

“Naci…. Shikenan ka gaishe su”

Katse kiran nayi na koma falo shi kuma ya ƙarasa shiryawarshi cikin kayan shan iska boxer da ƙaramar t shirt ya fita saboda yaji motsin dawowarsu mommy daga church,

Dukkansu suna zaune a falo banda Hadiza wacce ke cikin kitchen tana dafa musu abin da zasu ci, gaba ɗaya ƙannen nashi sunyi murna da ganin sa amma banda mommy wacce tayi kicin kicin da fuska tun bayan da taga shigowarshi, sama sama ma ta amsa gaisuwarshi wanda sam bai ma yi tunanin zata amsa ba, zama yayi cikin su duk da mommyn bata sakar masa fuska ba, abinci Hadiza ta kawo masa jalop ɗin taliya da ɗanyen kifi, da yake dama shi ba mai yawan magana bane har suka gama cin abincin bai yi magana ba,

“Samuel abin da kayi yayi daidai kenan ko? Ka kyauta abin da kayi ko? Ni mahaifiyarka ni ka juyawa baya ka zaÉ“i wasu fiye dani….” mommy tace dashi bayan su Mary sun fita daga falon ya rage daga ita sai shi,

“mommy wallahi ba juya miki baya nayi ba har yanzu kina nan matsayin ki na mahaifiyata wadda bani da wani sama dake….”

“shikenan” ta faÉ—a tana tashi daga inda take zaune zuwa cikin bedroom É—in ta, ta É—an ji sanyi kaÉ—an a ranta da jin abin da ya faÉ—a mata amma duk da haka wannan bazai canja mata Æ™udurin da ta jima dashi a cikin ranta ba, sam ba zata fasa ba daga abin da tayi niyya dan a yanzu ba musuluntar da yayi ne tashin hankalinta ba babban tashin hankalinta wannan auren da yayi wanda take ji ajikinta kamar shine zai raba ta da É—anta wanda ita kuma ba zata taÉ“a lamuntar hakan ba.
***
A ɓangaren Hashim kuwa abubuwa sun ci uban na da, fantamawa yake yi ba kaɗan ba shida hajiyarshi hajja Sharifa wadda ke sakar masa kuɗi ko ta ina, gaba ɗaya ya sallama gidan su tun daga ranar da Iya tayi masa korar kare bai sake waiwayar unguwar ba kai ko hanya bata bida shi haka ya bar su Iya cikin ƙuncin rayuwa da halin ƙaƙa na kayi shi bai taimaka musu ba bai kuma bar mai taimakonsu ya taimaka musu ba, ko bikina bai ji ba kuma bai san nayi ba dan shi yanzu ba ta ni yake yi ba ta hajja Sharifa yake yi wacce ta zamo fitilarsa acewarsa ta dalilin ta ne ya soma riƙe manyan kuɗaɗe, duk inda manyan yara suke to zaka samu da Hashim aciki, kullum yana hanyar zuwa party da sauran wuraren shaƙatawa ga uban tarin ƴanmata masu aji da marassa aji duk nasa ne, duniya tana gara masa fiye da yadda yake so, ni kuwa dama ya jima da mantawa dani acikin tarihin rayuwarsa,

Gidan hajja Sharifa yake zaune kuma anan yake tara abokai da ƴanmata suke sharholiyarsu babu mai kwaɓarsu.
***
Shirin bacci nayi cikin kayan bacci na masu taushi, ina kammalawa na haye gado araina ina cewa “Bishra uwar son kallo” dan tana can falo tana kallon wani film, wayata na É—auka da zummar kiran samz sai ga kiran shi ya shigo, murmushi nayi na É—auka,

“Hubbi baka yi bacci ba?” na faÉ—a cikin tsokana,

“Taya zanyi bacci banji voice dinki ba baby….”

“Ni bama zan iya bacci ba saboda baka nan…” na faÉ—a ina fashewa da kuka a hankali,

“Am soo sorry baby…. Bari kuka mana, ranar Friday zan dawo…… Ba É—azu kince min idan na dawo zaki bani maganina sau 3 a rana ba?”

“uhmm uhmm” na faÉ—a ina maÆ™ale kafaÉ—a kamar yana kallona, murmushi naji yayi kafin ya soma jero min kisses ta cikin wayar, É—an tsagaitawa yayi kafin yace,

“Idan na dawo ai za a bani ko?”

“Ni ko yanzu ka dawo ma….” na faÉ—a nima ina kissing É—in shi ta cikin wayar,

“I love you baby… I don’t know how to describe irin yanayin da na samu kaina that night….”

“Kai ba zaka iya describing ba amma ni zan iya” na bashi amsa ina turo baki kamar yana kallo na,

“ok, how did you feel? Tell me”

Gyara kwanciyata nayi sannan nayi gyaran murya nace,

“Zafi, raÉ—aÉ—i, zugi etc, sai da naji kamar ansa sabuwar razor blade an yanyaka wurin sannan aka kawo ruwan barkwano aka watsa a wurin, ta hakane kawai zan iya describing maka abin da naji ranar….”

“oh my God….” naji ya faÉ—a cikin murmushi,

“Ayya sorry baby, ni kuma ranar naji zaÆ™i fiye da sugar fiye da zuma, and naji zaÆ™i fiye da Maggi fiye da komai a duniyar nan…. Kuma tun daga ranar na samu nutsuwar da har yau ban sake jin buÆ™atar wata mace ba…. Thank you for that”

Turo baki na sake yi ina yi masa shagwaɓa shi kuma yana ta lallashi na a haka har na samu nayi bacci,asubar fari kuwa bayan na idar da salla da massage ɗin shi na fara cin karo,

_Mornings would be better if I woke up next to you. Good Morning my love_

Reply na tura masa ko 5 seconds ba ayiba sai ga kiran shi ya kirani video call, É—ayan bedroom É—in na koma nabar Bishra a É—ayan, saida na fara gasheshi sannan muka yi karatun Alqur’ani tare sannan na É—ora masa Al’azkar É—in da nake koya masa, ina faÉ—a yana faÉ—a da haka na koyar dashi addu’o’i guda biyar,

“Baby cire hijab É—in mana” naji yace bayan ya rufe littafin dake hannunsa ya ajiye kan bedside drawer,

“Saboda me?” na tambaye shi ina kallon fuskarshi,

“I want to see your chest please….” kunya naji ta kamani jin amsar da ya bani, cire hijabin nayi ina É“oÉ“É“oye fuskata,

“please cire night gown É—in mana”

Turo baki nayi inata noƙe noƙe amma saida na cire, kissing ɗina yake ta yi ta cikin wayar kamar zai cinye ni daga ƙarshe nace ya kwanta yayi bacci muka yi sallama, nima baccin na koma bayan na maida rigata kuma na kashe wayata. Yau dai wuni nayi ina yin baƙi, Anty Salma tazo ƙawar Anty wadda muka je training Lagos tare, bayan ta tafi su Annie suka zo ganin ɗaki su ɗinma basu wani jima ba, lokacin da zasu tafi kamar inbisu haka naji, har yamma inata baƙi washe gari kuma Anty ta kawo min yaranta su Islam suka wunar min saboda jibi zasu koma Abuja, a ranar shima Daddyn samz da uncle ɗinsa suka zo, girki nayi musu musamman duk da su ɗinma basu wani jima ba shi kansa samz ɗin bai san zasu zo ba bare ni, Albarka daddy yayi ta saka min sannan suka tafi,

Da daddare da ya kirani nake sanar dashi zuwansu daddy duk da yayi mamakin zuwan nasu amma yaji daɗi sosai saboda ko babu komai ai naga wani nasa yazo matsugunninmu, da yake yanayi ne na sanyi takure nake cikin bargo nasha uban kayan sanyi harda socks a ƙafata, kuka na fara yi masa babu gaira ba dalili shi kuma dandanan ya ruɗe,

“Baby menene?”

“Ni ka dawo haka”

“2 days remaining insha Allah baby…. But it seems like you are feeling cool ko?”

Kai na ɗaga masa ina ƙaƙalo hawayen shagwaɓa,

“Same here sweetheart nima sanyin nake ji amma na kusa dawowa kinji, ki daina kuka”

Ya jima yana kissing da rarrashi na kafin na yarda nayi bacci, kullum nida shi muna maÆ™ale akan waya inyita zuba masa shagwaÉ“a yana lallashina da haka har Friday tayi, ai ranar da farin ciki na tashi, tunda wuri na soma shirin karÉ“arsa, girki nayi masa sannan na gyara jikina dama tuni Bishra ta tafi dan tun safe ta tafi gida wai zata yi baÆ™i, kwalliya nayi cikin wata maroon É—in doguwar riga amma irin ta zaman gidan nance bata fita ba saboda bata da nauyi kuma shara shara ce sannan Æ™irjin rigar a buÉ—e yake, turare nasha kota ina sannan na zauna zaman jiransa ina game a system É—ina dan rage lokaci, Æ™arfe 3 daidai na yamma ya Æ™araso, tashi nayi naje na buÉ—e masa gate ya shigo yana sanye da baÆ™in jeans da green É—in t shirt an rubuta fresh agaban rigar da baÆ™in combos a Æ™afarshi yana goye da jakar shi kan shi da baÆ™ar p cap, sai baÆ™in glasses a idonshi kamar yadda ya saba yin shigar shi tun a lagos da na fara ganinshi, tsalle nayi na É—aleshi lokacin da ya shigo nan ya riÆ™e ni muna dariya………. ✍

 

*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*

 

_*Ummi Shatu *_

Post a Comment

0 Comments