Garin Dadi 38

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Garin Dadi 38


©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
_(Home of experts & perfect Writers)_

 

*GARIN DAÆŠI……!*

*_NA_*

*_UMMI A’ISHA_*

*Wattpad:ummishatu*

End of book 1(end of free pages)

PAID BOOK #500

{38}

*Ina kuke manyan mata Æ´an Æ™walisa ma’abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haÉ—aÉ—É—un Lagos lace wanda zaku iya samun É—inkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaÉ“inki, gefe É—aya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUÆŠI GIDA…..*

~~~Cike da kasala na soma ware kitson kaina amma ko biyar ban tsefe ba naji na gaji ba zan iya cigaba da tsifar ba babu shiri na haƙura sakamakon wani bacci da naji yana fisgata, tashi nayi na rufe ko ina na dawo na kwanta nan kan kujera ko minti goma banyi da kwanciya ba bacci yayi gaba dani, bacci nayi mai shegen daɗi cikin kwanciyar hankali da nutsuwa wanda bani na farka ba sai misalin ƙarfe ɗaya da rabi na rana,

Wanka na shiga nayi a raina ina cewa har yanzu wannan bawan Allahn bai dawo ba daga zuwa siyan waina, shiryawa nayi cikin riga da skirt ƴan kanti masu santsi na shan iska, ni kaina mamakin kaina da kaina nake saboda irin yanda na ɗan yi kumari, ƙirjina ya cika dam ya ninka da, bra ɗin da samz ke yimin ɗan biki a kai yake cewa wai tayi min yawa to yanzu tama yi min kaɗan shiyasa ko sawa bana yi, salla nayi bayan na feshe jikina da turaruka masu sanyin ƙamshi, ƙarar wayata ne ya sani miƙewa na nufi falo inda take, ganin samz ne ya sani yin murmushi kafin na ɗaga na zauna kan kujera,

“Baby…. Are you still sleeping?”

“No, na tashi, salla nayi…”

“ok, buÉ—e min na dawo”

Ajiye wayar nayi na fita na buÉ—e masa, shigowa ciki yayi yana kallo na fuskar sa cike da so da kulawa,

“Sannu da zuwa…” nace dashi ina É—an hugging É—insa,

“Thank you baby….”

Ciki muka shiga ya miƙo min ledar da yazo da ita karɓa nayi na buɗe, ai ina buɗewa naji yawuna ya tsinke tashi nayi na ɗauko jug da filet na juye wainar da kunun dan duk a cikin leda aka zubo, ƙuliƙulin na kunce na juye a kai na fara ci kamar na shekara hanci komai ba, tsayawa kawai yayi yana kallona amma ban san yana yiba har sai da naji cikina ya ɗauka sannan na ajiye guntuwar wainar na ɗauki kunun nasha, ba ƙaramin daɗi wainar tayi min ba ko kuma dan ina kwaɗayinta ne naji daɗinta oho,

“Kaifa? Ka ci abinci?”

“Naci…… Baby your chest is now full……” ya faÉ—a yana kai hannunsa wurin,lumshe idanuwana nayi na shige cikin jikinsa ina jin wani irin shauÆ™in son kasancewa da shi, ada mijina bai wani dameni ba asalima har faÉ—uwar gaba nake ji duk lokacin da na fuskanci zai raya sunnah dani amma yanzu ni da kaina na bashi gudummawar faruwar hakan ban san dalili ba yanzu sam bana Æ™osawa dashi. Soyayya muka shayar da junanmu sannan muka tsarkake jikinmu muka yi sallar la’asar wacce har mun so ma mu makara, muna manne da juna har dare, ni ina narke jikinsa kamar wata kyanwa bayan munyi sallar ishah muka fita tare na rakashi restaurant yaci abinci ina waje ina jiransa domin ni bana son jin koda Æ™amshin abincinne, ina tsaye a waje ina jiran fitowarsa wasu samari guda biyu suka zo wucewa har sun wuce sai suka dawo da baya, bakina cike fal da yawu saboda tashin zuciyar da nake ji haka kawai,

“Æ´an mata barka da hutawa….” suka ce dani atare lokaci guda, da kallo na bisu na san a haife ba zasu wuce sa’anni na ba, ban tanka musu ba har sai da suka sake maimaitawa sannan na É—an matsa na zubar da yawun da ya cika min baki nace,

“lafiya?”

“lafiya lau…. Idan ba zaki damu ba muje mana”

Kaina na kalla ina sanye da hijabina har ƙasa, bance musu uffan ba dan na hango samz yana ƙoƙarin fitowa, har ya ƙaraso suna tsaye gabana suna yimin magiyar inbisu mu shiga cikin restaurant ɗin amma ban tanka ba,

“Hey… Me ke faruwa?”

Kallon kallo suka fara yi a junansu,

“So suke wai inbisu mu shiga ciki….” na bashi amsa ina kama hannunsa,

“Wannan matar aure ce to….. She’s mine”

Daga haka muka yi gaba yana riƙe dani, sai bayan da muka fita daga cikin harabar restaurant ɗin sannan naji yace,

“Ba zan sake zuwa dake ba ko ina….”

“why?” na buÆ™ata fuskata a shagwaÉ“e,

“to ba ga irinta nan ba, mates É—inki sun fara kawo miki hari…..”

“To ai ban kulasu ba, ni inada miji”

“A ina?”

“Anan mana…” na faÉ—a ina sake shiga jikinsa, murmushi yayi ya riÆ™eni shima,

Muna komawa gida da wannan wainar da kunun tsamiya na fara kafin nayi shirin bacci dan yanzu da wuri bacci yake cika min ido ina rigashi kwanciya ma. Tun ƙarfe 9 nayi bacci kuma ban farka ba sai 3, kwance na ganshi kusa dani da laptop akan cikinsa yana faman danne danne,

“Ba kayi bacci ba?”

Kallona yayi bayan ya juyo da haske laptop É—in saitin fuskata,

“Yanzu nake son yi…. Na gama”

“ok, kayi bacci lafiya…”

“Na gode my sweet baby”

Lumshe idona nayi bayan na gyara kwanciya ta kuma ban sake farkawa ba sai asubah, yau kam da wuri ya tashi yatafi siyo min waina da kunu, ina kwance a ɗaki muna waya da ƙawalli tana bani labarin irin wahalar da take sha sakamakon juna biyun da take ɗauke dashi,

“ayya Æ™awalli sorry….. Allah ya rabaku lafiya, sai kiyita kula dai ki rage yawan aiki tunda asibiti sun hanaki…”

“ehh dama yanzu babu abin da nake yi tunda an samo min mai aiki…… Ke fa wata nawa ne cikin?”

“kin jiki, ni É—in ciki gare ni?”

“To raina min hankali, ai ko ki faÉ—a ko kar ki faÉ—a nidai na san warhaka an samu rabo”

“to nidai bani da komai, ai samz bawan Allah ne”

Dariya naji tayi kafin tace, “Naga alama ai…. Ai makwancin kowa ma daban keda shi”

“kamar kuwa kin sani…” na bata amsa nima ina dariya,

“Hmmmm Widat kenan…. Allah dai ya raba lafiya”

Hira muka yi sosai dan har saida cajin wayata ya ɗauke sannan muka haƙura na jona wayar a jikin caji na sake kwanciya a haka ya dawo ya sameni da yake yau ya fita da keys.
***

“What? Matarsa ta bishi Abuja yanzu haka tana tare dashi? Abun da ba zai taÉ“a yuyuwa ba kenan….. ” Maman Mary tayi maganar cikin Æ™araji,

” calm down kawata, zauna kiji, ki kwantar da hankalinki ” Madam comfort ta faÉ—a cikin alamun rarrashi, taÉ“e baki Felicia tayi ta sake gyara zama bayan mom É—inta tayi mata alama da ido,

” mommy sai haÆ™uri fa, but to be honest an gama miki da yaro wallahi, wannan Æ´ar yarinyar sai yanda tayi dashi, duk ya susuce a kanta, komai ta saka shi yi yake, baki ga wulakancin da ta sakashi yayi min ba jikinsa yana rawa….. Harda ce min wai ko uwar sa bata isa komai ba bare ni, gaskiya naji tausayin samz dan tabbas ba haka suka bar shi ba, ya zama wani bita zai zai Æ´ar Æ™aramar yarinya tana commanding É—insa…. ”

Wani Sabon tashin hankali da É“acin rai ne ya ziyarci mommy jin abubuwan da Felicia ta faÉ—a game da gudan jininta, lallai biri yayi kama da mutum dan yanzu kam taga samz yaja baya da zuwa Kaduna ashe yana can tare da wadda ta fita muhimmanci a wurinsa, dafe goshinta tayi cikin damuwa tace,

“Na rasa yaya zan yi da wannan yarinyar, na rasa ta yadda zan rabata da É—ana…. Maman Felicia dan Allah menene mafita? Ki bani shawara pls”

Kallon Felicia madam comfort tayi kafin tace ta basu wuri, bayan fitar ta ta kama kunnen mommy tayi mata raÉ—a tsawon mintuna sannan tace,

“Ina ganin wannan shine kaÉ—ai mafita”

Tashi mommy tayi ta tafi tana mai yin amanna da shawarar madam comfort.

Mu kam sam ba mu san abin da ke gudana ba dan kawai rayuwarmu muke yi anan cikin so da ƙulafucin juna, samz shi ke yimin komai har wankin inner wears dan ni babu abin da nake yi, rabon da in ɗora tukunya kuwa da sunan girki har na manta dan tun zuwana yanzu kimanin watanni biyu kenan mun shiga na uku, kullum restaurant yake zuwa yaci kuma bai taɓa complain ba, ni kuma wainar gero da kunun tsamiya sune suka zama abinci na har gobe su nake iya ci dan har an zaunar min da kwano a gidan matar da take yi kullum samz zaije ya karɓo min ita zanci da safe da rana da daddare, na sake yin fresh na murje nayi kyau abina bani da matsalar komai dan muna zaune da mijina lafiya sannan yana nuna min so kamar zai cinyeni, ni kaina na san irin son da samz yake yimin dole idan mahaifiyarsa ko ƙannensa suka gani suji wani abu aransu saboda jikinsa har rawa yake yi wurin yimin ko samar min abin da nake so sam baya ƙaunar yaga raina ya ɓaci,duk wanda yaga irin kyautata min ɗin da yake yi zai tsammaci ko na shanyeshi ne amma Allah shine shaida ya san ban taɓa yin wani abu wanda ya kauce hanya wai da sunan in mallake mijina ba ko wani abu mai kama da haka.

Yau sai da ya gama tsefe min kitson kaina sannan ya fita office, ina zaune a falo bayan na yi wanka sanye da ƙaramar doguwar riga, mun gama waya da samz kenan naji bugun ƙofa, tashi nayi naje na buɗe bayan na saka hijabina har ƙasa, wata mummunar faɗuwar gaba ce ta ziyarceni sakamakon waɗanda na gani, mahaifiyar samz da ƙannenshi guda biyu sai Felicia, duk da ban taɓa ganinsu ba amma na gane cewa sune domin na gansu ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba a hoto, murmushin yaƙe na ƙaƙalo wanda a zahiri yafi dariya ciwo,

“Sannunku da zuwa…. Mommy sannu da zuwa” na faÉ—a jikina na rawa sakamakon irin kallon tsana da Æ™in jini da na gani a fuskokinsu su duka,

Mommy ce ta fara wucewa batare da ta kulani ba bare ta amsa sannu da zuwan da nake yi mata kamar zan zube a ƙasa, duk cikin su babu wanda ya amsa sai Felicia kaɗai itace ta kula sannan ta wuce ciki, ƙofar na mayar na rufe nabi bayansu cikin sanyin jiki, duk ɗinsu ɗauke suke da manyan jakunkuna kamar zasu shekara a gidan,

Ruwa naje na ɗebo roba huɗu na haɗo da lemon jarka, ni tunda nazo gidan ma ban sha lemon ba saboda bana so haka shima samz ba sha yake ba dan naga kamar bai dameshi ba, babu wanda ya tanka min nan na durƙusa gaban mommy na soma gaidata amma bata amsa ba haka naci gaba da tsugunno har sai da naji ƙafata na ƙokarin ƙagewa sannan na zame na zauna, babu wanda ya kulani cikin ƙannenshi face sabgar gabansu da suke yi duk sun yi rashe rashe kan kujera kowacce tana latsa wayarta, ina ji lokacin da mommy tayi masa waya tace sun ƙaraso, kuma da alama ko shima bai san da zuwan su ba na san da ace ya sani da zai sanar dani,

Muna nan zaune har ya ƙaraso, ya sissiyo musu abinci da kayan marmari saboda ya san ni ba iya girki nake yiba bare in dafa musu, tashi nayi zan karɓi kayan hannunsa naji mommy ta daka masa tsawa,

“Kai…., idan ka kuskura ka bata abin da zan ci ta taÉ“a wallahi sai ranka ya É“aci”

Fasa karɓa nayi na wuce kitchen naje na dauko musu flates da spoons da cups, duk yanayin samz babu daɗi saboda abin da mommy tayi min ni kuwa ban nuna komai ko akan fuskata ba, jin suna gaisawa tana yi masa maganar da su ta shafa ya sani wucewa bedroom, zama nayi na ɗauki wayata ina duba saƙonnin da aka turo min ta manhajar WhatsApp, can ƙasan raina kuwa damuwa da tashin hankaline kwance amma dai nayi namijin ƙoƙari wurin dannewa,

Can falo kuwa bayan fita ta mommy ke sanar dashi dalilin zuwansu wai daddy baya nan yaje Imo noma kamar yadda ya saba dan yana da wata babbar gona a can ƙauyensu wanda yake noman doya aciki ganin baya nan shiyasa suma suka taho nan zasu yi kwana biyu sun bar Abdullahi agida, shiru samz ya ɗanyi daga baya yace,

“To mommy zan kaiku Guests house ne ko kuma mune zamu koma hotel mu bar muku gidan saboda naga kamar yayi mana kaÉ—an ko?”

“Babu inda zamu je, zamu zauna tare da matarka… Kai kuma sai kaje gidan Ahmad kayi manage kafin mu tafi, har yaushe zaka yi asarar kuÉ—i ka kama mana hotel…. Ban yarda ba”

Shi kansa ya san zaman takura zanyi shiyasa bai so haka ba to amma babu yadda ya iya, É—aki ya biyoni bayan sun gama gaisawa dasu mommy, a kusa dani ya zauna ya jani jikinsa, da murmushi na kalleshi kamar babu abin da ke damuna,

“baby…. Kiyi hakuri mommy sun zo, zasu yi 2 days”

“To kuma menene, ai babu wani abu… Tunda kai baka kaini ba ai gashi su sunzo”

“Nagode baby… I love you”

“I love you too” na faÉ—a Ina kwanciya a jikinsa, har magriba muna tare dashi a falo suna hira da mommy nikuma ina can gefe É—aya ina jinsu, bayan sallar ishah yayi mana sallama ya tafi bayan ya sake rarrashina amma na nuna masa babu komai, acikin bedroom É—in suka kwana nikuma a falo, washe gari na tashi na É—an Æ™oÆ™arta na gyara gidan, ban shiga É—akin ba saida suka fito na gaida mommy amma bata amsa ba su kuwa Æ™annenshi babu wadda yace min ko ci kanki tun zuwansu, bedroom É—in na shiga domin inyi wanka Felicia na gani baje saman gado, koda ta ganni sai ta kwaye rigar baccin da ke jikin ta, É—auke kaina nayi na shiga toilet, sai da nasa key na datse sannan na rage kayan jikina,

Lokacin da na fito kuwa da zan shirya ai gani nayi ta jiyo gaba ɗaya ta zuba min idanuwa kamar zata cinyeni, ƙirjinta duk awaje, bathroom na koma na saka kayana sannan na fito na shafa mai na fita, iske mommy nayi tana ta zazzagawa samz faɗa a waya wai ba za a dafa musu breakfast bane, ban dai ji me yace ba naji ta haushi da faɗa tana cewa ita ba zata juri cin abincin restaurants ba idan ba zai sa agidansa a girka musu ba shikenan, duk da inada lalura haka na daure na shiga kitchen dan komai akwai, dankali na fere na ɗora musu sannan nayi sos amma duk saida na daure hancina sannan nayi, ina gamawa ina fito musu dashi yana shigowa,

Kitchen ya biyoni, yana yimin sannu, kai na ɗaga masa saboda bakina cike yake da yawu ga amai da nake ji, bedroom na wuce na shiga bathroom yana biye dani, amai na fara sheƙawa kamar zan amayar da kayan cikina gaba ɗaya riƙeni yayi yana yimin sannu, bayan na gama ya ɗaukoni yazo ya kwantar dani akan gado, ban muna masa komai ba har naji komai ya lafa min sannan na dubeshi nace,

“Ina abinci na? Ko baka karÉ“o min ba?”

“Zan kawo miki yanzu, sannu baby”

Tun daga wannan lokacin na zama kamar baiwa nice shara wanke wanken flates ɗin da suka ci abinci, nice girki duk da ba ci zanyi ba asalima idan nayi na gama sai nayi amai kamar zan mutu, gasu su yi ta ɓata wuri da gangan amma bai mai gyarawa sai ni, kuma duk ciki babu mai yimin magana ko kulani a cikin su dama dama Felicia ma wani lokacin har girki take tayani amma abin da yake baƙanta min rai da ita daga taga zan shiga wanka sai tabini bedroom ta sakani a gaba da kallo kamar wata mayya gashi sai tayi ta buɗe jiki especially ƙirjinta sai dai in ɗauke kaina, duk waɗannan abubuwan ban taɓa faɗawa samz komai ba na ƙuduri niyyar yin haƙuri dasu har su gama zamansu su tafi tunda bawai zamu zauna dasu anan for life bane. Sati biyu da zuwansu yau kuma a yadda naji suna faɗa nan da 5 days zasu tafi domin daddy zai dawo kuma Hadiza zasu koma makaranta Uni-jos, yau tun 3 duk suka fita suka tafi ko church ko ganin garine ni dai ban sani ba, bayan tafiyarsu da kamar 40 minutes sai naji knocking budewa naje nayi nan ga Felicia ce ta dawo ita kaɗai, kamar na san wani abu zai faru sai ban rufe ƙofar ba kawai na barta a buɗe na dai turata, dama girki na gama, na gama amai kenan zanyi wanka naji knocking din, ganinta sai na fasa wankan, bedroom ɗin na shiga da zummar ɗauko wayata, ina shiga na ganta tsaye zindir haihuwar uwarta dama da alama jiran shigowata take,

“Beautiful girl…..” tace dani tana Æ™oÆ™arin riÆ™o hannuna, cikin sauri na kauce,

“Wallahi ina son ki widat….. Ba zan iya rayuwa ba idan ban same ki ba”

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un” na faÉ—a cikin ruÉ—ewa domin jin maganarta nayi kamar saukar aradu wai tana sona abin ko daÉ—in ji babu, me ya haÉ—a mace da sona ni Maimunatu? Ai ko daga bakin namiji wanda ba samz ba bana fatan jin wannan kalmar ta so bare a bakin mace Æ´ar uwata kuma jinsina, kafin na farga na dawo hayyacina kawai jin bakin ta nayi a wuyana ashe har tayi fatali da hijabina ni ban sani ba, ban san lokacin da na kai mata wani wawan mari ba, abin ka da wadda tafini Æ™arfi nan ta matse ni jikin bango muka fara kokawa har ta samu nasarar murÆ™usheni saman gado, rigata ta keta gida biyu tana kaiwa Æ™irjina kiss kota ina………….. ✍

*TIRƘASHI shin Felicia zata yi nasara? Wai shin ina labarin HASHIM? Ina makomarsa? Ya zaman widat da samz zai kasance shin soyayyarsu zata ɗore ko kuma ɗaya daga ciki zai juya baya? Wanne irin ƙalubale ke zaman jiran fuskantarsu a gaba? Mahaifiyarsa da danginsa zasu karɓi widat? Zasuyi nasarar rabasu ko kuma yaya zata kasance?, dukka amsoshin waɗannan tambayoyi dama wasu suna ƙunshe cikin cigaban labarin domin yanzu fa aka fara, tabbas akwai sauran rina akaba dan tsugunne bata ƙare ba, ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*

 

_*Ummi Shatu*_

Post a Comment

0 Comments