Garin Dadi 39

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Garin Dadi 39


GD

*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*

{39}

*Ina kuke manyan mata Æ´an Æ™walisa ma’abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haÉ—aÉ—É—un Lagos lace wanda zaku iya samun É—inkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaÉ“inki, gefe É—aya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUÆŠI GIDA…..*

~~~Tamkar mafaraucin da ya jima yana farautar abinda zai kai bakinsa tsawon lokuta marassa adadi kuma cikin sa’a kayansa suka tsinke gindin kaba yayi gam da katar da farautar da ya jima yana nema haka Felicia ta zama a gareni duk da har lokacin ni É—in ban daina fafutuka tare da kokawar kokarin kwatar kaina ba, dambe fa muke yi sosai sai dai amma dama ni kaina na san tafi Æ™arfina dan bama za a haÉ—a Æ™irata da tata ba wadda adirenta take ga tsayi ga Æ™iba haka kuma ko ta É“angaren shekaru ma nata sun ninka nawa amma duk da hakan ban sare ba dan abin azuci yake, tunawa da nayi da Æ™udurinta a kaina na son shiga gonar Samz wadda ya zame min wajibi in kare masa kaina da duk wani abu nawa wadda ya zama mallakina ai take wani gagarumin Æ™arfi yazo min na shaÆ™e mata wuya gam ina tura ta, har lokacin bata saduda ba kuma ban ga alamar zata sadudan ba shiyasa nima ban yi giving up ba naci gaba da shaÆ™eta gashi duk ta yayyakusheni da dogayen faratanta masu shegen tsini,

Bayan mun jima muna wannan kokawar daga ƙarshe na samu nasarar jefata ƙasa nan ta faɗa bayanta har yana buguwa da bango, ganin haka ai ban jira komai ba haka banyi wata wata ba na ruga da gudu na fita dama kuma kofa a bude take, duk da rigar jikina yage take amma hakan bai dakatar dani ba domin akwai hijabi a hannuna, ina kokarin fita naji munci karo da mutum amma jin kamshin da ya bugi hancina take ya tabbatar min da cewa abin begena ne Allah ya kawo min shi a daidai lokacin da nake da buƙatar hakan, rungumeshi kawai nayi ina fashewa da kuka, cikin ruɗewa da tashin hankali yake kallona bayan ya ɗagoni yana tambayata,

“Baby….. What’s going on? Stop crying and tell me…… What’s happening? Pls answer me….. Baby…”

Cikin kuka nake nuna masa cikin bedroom É—in inda Felicia ke ciki, bai kai ga fahimtar abinda nake son faÉ—a masa saboda na kasa magana jikina in banda rawa babu abinda yake yi kuma kallo É—aya zaka yimin ka gane acikin firgici da tashin hankali nake, fitowar Felicia a guje itace ta dakatar dani daga amsar da naketa son bashi da hannuna, cikin sauri na sake É“oyewa cikin jikinsa ina kuka, ai nan take ya fahimta kawai sai ji nayi ya fincikeni daga jikinsa ya nufeta,

“Felicia what are you trying to do……?”

Wasu tagwayen maruka guda biyu naji ya bata a jere wanda sautinsu sai da ya tsoratar dani, da gudu ta juya ciki ya rufa mata baya idanuwansa cike da kishi tsantsa, ganin haka ya sani nima bin bayan su dan na fahimci kishi ya rufe masa idanu dan haka zai iya aikata komai,

Jibgarta na samu yana yi kamar Allah ne ya aiko shi ga jini ta bakinta da hancinta sakamakon marikan da yayi mata masu zafi, ai ganin zai iya lahantata ya sani saurin zuwa na rikeshi ina roƙonsa,

“Sweet dan Allah ka rabu da ita….. Pls and pls….. Dan Allah….”

Da ƙyar ya saurare ni har na samu nasarar janyoshi muka fito falo, kallona ya shiga yi tun daga sama har ƙasa kafin ya sake komawa cikin bedroom ɗin nan na sake bin bayansa, tarar dashi nayi yana zuba mini kayana cikin bag sai huci yake, nidai ina tsaye ina kallon ikon Allah banyi magana ba har ya kammala ya rufe ya janyo jakar ya damƙi hannuna ya janyo ni fuuuuhhhh, muna fitowa falo su mommy na shigowa, tsayawa duk suka yi suna kallonmu musamman mommy,

“Samuel….. Lafiya kake? Ina zaka je?” mommy ta watso masa wannan tambayar tana bina da kallon tsana saboda har lokacin hannunsa riÆ™e yake da nawa,

“mommy zamu bar muku wannan gidan har zuwa lokacin da zaku tafi saboda bazan iya barin Matata ta cigaba da zama anan ba tare daku, wannan yarinyar amana ce a wurina, amana iyayenta suka bani ita and duk abinda ya sameta sai Allah ya tambayeni saboda yanzu nine komai nata bata da kowa anan sai ni….. ”

” Samuel…… Samuel… Wai kana hauka ne? Baka da wata magana a koda yaushe sai ta matarka? Ita kaÉ—ai ce damuwar ka da matsalarka? Nida yan uwanka ba damuwarka bane ko? Kai iya matarka kawai ka sani saboda da gold akayi ta…. ”

Fitowar Felicia tana kuka shine sanadiyyar da gaba É—aya hankula suka koma kanta, da gudu ta tafi ta faÉ—a jikin mommy tana kuka tare da sanar da ita irin uban jibgar da samz yayi mata,

” mommy ki daina sauraren wannan makirar yarinyar dan duk abinda zata faÉ—a miki ba gaskiya bane, ta yaya zata zo ta rinka kokarin sai ta afkawa Matata? Akan me? To gaskiya na gaji i will not take this……. Zan tafi da matata in kula da ita tunda duk wahalar da take yi muku bakwa gani ”

” Kaine babban makaryaci Samuel….. Saboda matarka ka zabi ka É“ata da kowa ko? Matarka tafi maka kowa, duk abinda ta faÉ—a maka komai girmansa kanka É—auka yake, yanzu ta zo ta shirya maka karya akan Felicia amma ka yarda…. Naga alama nan gaba ni kaina sai ta rabani da kai…..”

“mommy……”

Dakatar dashi cikin tsawa tayi tare da É—aga masa hannu alamar bata son jin komai, ni dai tuni na jima da soma zubar da hawaye saboda bakin ciki da bacin rai domin kiri kiri su mommy suka goyi bayan Felicia suka ce wai sharri nake yi mata dan kawai ina bakin cikin zaman su atare dani kuma ina son raba samz da yan uwansa,

“mommy babu maganar karya fa cikin wannan maganar saboda ki dubi jikin ta duk yakushi ne sannan har kayanta dake jikinta ta yaga, shima wannan din sharri ne ko set up kamar yadda kika fada?”

“kai samz ni matarka bata isa tayi wasa da tunani na ba kamar yadda tayi wasa da naka, in your stupidity duk abinda matarka ta fada hakane ko? Wannan karya ne, karya take yiwa Felicia dama ni na san tunda ka auri yarinyar nan to sai ta rabaka da kowa naka, she’s a bad luck to our family…… Shiyasa tun farko ban goyi bayan ka aureta ba amma ka Æ™i, to babu inda zaka je da ita, dole taci gaba da zama tare damu har zuwa lokacin da zamu tafi….. ”

” mommy wannan ne bazai taba yuyuwa ba, bazan bari ku kashe yarinyar mutane ba, tunda ku dai kun zaÉ“i zama anan to ga gidan nan mun bar muku, duk wani evidence da zai iya satisfying dinki kan abinda yarinyar nan ta fada gashi nan na nuna miki amma kin rufe idonki kin ki gani saboda kiyayyar da kike yi mata, gaskiya wannan kiyayyar tayi yawa, bazan iya cigaba da barin ta tare da ku ba….. ”

Daga haka ya fizgi hannuna nikuma na soma kokarin turjewa saboda bana son in bishi inja masa fushin mahaifiya amma wani kallo da yayi min ni kaina sai da na san yau ran Æ´an mazan ya É“aci duk da haka ban bishi ta sauki ba amma haka ya figeni bayan ya dauki wayata yasa cikin aljihu ya tisani a gaba har bakin titi inda ya tare mana abin hawa, har ga Allah bana cikin farin ciki da abinda yayiwa mahaifiyarsa dan ko babu komai itace sama da komai a gareshi a duniya amma sai dai na fahimci shima yau ransa ya baci ne,

Kuka nake yi amma bai saurare ni ba har muka je lodge É—in da yace mai taxi ya kai mu, fito da kayan yayi ya biyashi sannan ya sake tisani a gaba zuwa ciki, apartments ne masu kyau da tsari na yan gayu wanda aka gina musamman da ma’aurata, mafi yawa masu honeymoon ke zuwa wurin su yi hutunsu dan kai ba zakace a Æ™asa Nigeria kake ba, Allah kaÉ—ai ya san yawan kudin da ya biya sai shi,

Kama hannuna yayi muka bi bayan É—aya daga cikin ma’aikatan har zuwa apartment din da aka bamu, komai yaji tamkar a Æ™asar turai sai dai sam bana farin ciki da hakan, da ace zuwan daÉ—i muka yi na san da zamu sha soyayya har mu gaji saboda yanayin wurin ma kadai ya isa jefaka cikin shauki da begen masoyinka sai dai amma kash wannan zuwan zuwane na bacin rai da takaici.

Ganin cikin matsanancin bacin rai yake shiyasa banyi masa magana ba na zuba masa ido, alwala ya shiga yayi domin lokacin salla ya yi wannan shine É—aya daga cikin abinda ke kara burgeni dashi sam baya wasa da salla kuma baya sakaci da ita, duk abinda yake yi da zarar lokaci yayi zai bari yaje yayi salla, nima alwalar na shiga nayi bayan na yi wanka dagaske Felicia ta yayyakusheni dan har su kirjina da saman fuskata shiyasa sai da nayi mata Allah ya isa babu adadi, lokacin da na fito daure da towel yana kwance gefen gado har ya idar da salla amma kallo É—aya zaka yi masa ka gane cikin damuwa yake, kayana na bude sai lokacin naga ashe harda nashi ya debo,wata farar doguwar riga marar nauyi na dauko na saka bayan na shafa turare, hijabi na saka naje nayi sallar nima, na jima cikin sujjadata ina kaiwa Allah kuka na idanuwana suna zubar da hawaye saboda ahalin yanzu nidai banda wata matsala da ta wuce ta dangin miji ban rasa komai ba sai soyayyar uwar miji da danginsa, wallahi sai yanzu na yarda idan mace zata yi addu’a akan aure is good ta hada harda uwar miji da dangin miji tare da abokan miji bawai iya miji nagari kadai zata roka ba dan ko mijin ya kasance na gari idan danginsa da mahaifiyarsa ba na gari bane to is another challenge, babu masifar da ta wuce ace dangin miji sun tsaneka especially ma mahaifiyarsa dan zaman bazai taba yi maka dadi ba komai soyayyarka da miji tunda ni kaina shaida ce, wasu addu’o’in na sake yi bayan na idar da sallar sannan na mike na nufi inda yake kwance gefen gado cikin damuwa, ni kaina acikin damuwar nake wadda kusan zan iya cewa tafi tashi domin babu dadi ace a kanka a samu sabani tsakanin uwa da É—a wallahi a duk lokacin da na tuna hakan ina tsintar kaina cikin tsananin damuwa da bakin ciki marar misaltuwa duk da nasan har awurin Allah ban da laifi to amma na kasa samun sukuni acikin zuciyata, jikina a sanyaye na zauna gefensa tare da kamo hannayensa masu taushi na rike cikin nawa ina murzawa………

Post a Comment

0 Comments