Garin Dadi 40

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Garin Dadi 40


G*D

*Ina kuke manyan mata Æ´an Æ™walisa ma’abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haÉ—aÉ—É—un Lagos lace wanda zaku iya samun É—inkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaÉ“inki, gefe É—aya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUÆŠI GIDA…..*

 

{40}

 

~~~Idanuwansa masu kyau da jan hankali ya buÉ—e ya zuba min yana kallona kamar yadda nima nake kallonsa da nawa koÉ—aÉ—É—un idanuwan,

“Boo….. Dan Allah ina neman alfarma, abubuwan da kayi baka kyauta ba bai kamata ka zama mai yin musayar yawu da mommy ba…..” kstseni yayi ta hanyar faÉ—in,

“is ok baby…… Bana son wannan maganar yanzu, dan Allah ki rabu dani inji da abu daya, wacce irin biyayya ce ban yiwa mommy ba? Wacce biyayya ce bana yi mata tun daga lokacin da na mallaki hankalin kaina har zuwa yanzu? Amma duk da haka mommy bata gani, bata appreciating duk wani effort nawa…. ”

” duk da haka uwa uwace bae, ba a taÉ“a yin fushi da ita….. ”

” kinga dan Allah kar ki dameni….. ” daga haka ya zare hannunsa daga cikin nawa ya juya tare da gyara kwanciyarsa, na san abinda ya faru ne yake yi masa zafi sannan gefe É—aya ga kishin abinda Felicia tayi wadannan dalilan nasan ko bai faÉ—a min ba sune ke hana zuciyarsa sukuni a wannan lokacin amma koma dai menene zan bashi lokaci har ya huce sannan bazan Æ™osa ba bare gajiyawa zan cigaba da nuna masa muhimmanci mommy a gareshi koda kuwa yankan naman jikinsa take yi.
***
Tun bayan tafiyar mu mommy ke ɓaɓatu su Felicia na sake zugata suna cewa ai na riga da na gama tsafe samz sai abinda na saka shi yake yi, duk wani abu wanda na hanashi tofa bai isa yayi ba yanzu gashi nan harda ita mahaifiyarshi na rabasu,

“Mommy ki duba kiga irin wulakancin da samz ke yi min duk wannan bai isheshi ba har sai da matarshi tayi min Æ™arya da sharrin abinda banyi ba shikuma ya yarda, yanzu gashi ya tafi ya barki saboda ita bayan kina matsayin mahaifiyarshi…… This is very unfortunate…… Mtsww” Felicia ta fada cikin zuga tare da makirci, wani dogon tsaki Mary ta ja kafin ta kalli mommy cikin zafin zuciya tace,

“mommy….. Ki rabu dasu kawai ki saka musu ido, dole wata rana zai neme mu da kansa tunda mune dolensa, duk lokacin da matar tashi ta gama cinye masa kudin nashi ta gudu ta barshi ai dole wurinmu zai dawo….”

“Wannan ba magana bace, akan me za asaka musu ido abarta har tayi nasara akanshi? Mommy kiyi duk abinda zaki iya ki rabashi da ita koba komai ke mahaifiyarshi ce kece kika sha wahalarshi har ya girma ya zama wani abu ta ganshi ta aura, babu maganar abar mata shi har ta kai shi Æ™asa….. Mtswww ni ina mamakin ma yadda wannan yar yarinyar take juyashi kamar wata babbar mace ” Hadiza ta faÉ—a cikin É“acin rai, ita dai duk mommy tana zaune tana saurarensu bata sake magana ba saboda É“acin rai amma a cikin ranta ta É—aukarwa kanta alwashin ba zata taÉ“a bari nida samz mu kasance ba saboda gani take kamar nazo in rabata da gudan jininta ne,

“ai kamar ma gani nayi tana da ciki….. Inahhh bazan taÉ“a haÉ—a zuri’a da waÉ—annan mutanen ba, wallahi bazan taÉ“a bari a haifi wannan cikin ba….. Bazai taÉ“a yuyuwa ba har abada” duk cikin zuciyarta take waÉ—annan maganganun bata bari wani daga cikin yaran nata yaji ba wannan dalilin ne yasa taji tana alla alla gari ya waye su koma Kaduna taje ta fara neman mafita.
***
Kamar yadda yace in rabu dashi ƙyaleshi nayi domin na san irin yadda yake ji a cikin ransa, har muka yi sallar ishah sai bayan da aka kawo mana abinci sannan ya tuna da batun abincina wato waina da kunu kamar yadda shi kadai nake iya ci a halin yanzu, cikin damuwa ya matso gareni ya rike hannuwana fuskar sa ƙunshe da tausayi na yace,

“baby…. Abincinki ya za ayi? Ko inje in fita yanzu ko zan samo miki?”

Girgiza masa kai nayi ina shafa fuskarsa nace,

“A’a sweet bana jin yunwa ai, a Æ™oshe nake”

“no baby, ko ke bakya jin yunwa it may be babynmu yana bukatar abinci”

Murmushi nayi na girgiza masa kai nace,

“to zan ci wannan wanda aka kawo”

“tnx baby but Allah yasa ya zauna a cikinki i prayed”

“Insha Allah darling” na fada ina murmushi, abincin ya dauko kacokan ya kawo gabana ya soma budewa, tuwon semo ne miyar ogu sai snacks danginsu meat pie spring rolls etc, snacks din naci sosai dan kusan ma duk ni na cinye shi iya tuwon kadai yaci, shirin bacci muka yi bayan mun kammala, har lokacin ba a daidai yake ba akwai sauran fushi atare dashi, ni dai kasa bacci nayi inata sake sake acikin raina, na rasa wa yadace in tunkara da wannan matsalar tawa domin bana son ta shafi kowa dake kusa dani tunda kowa na duniya da ka gani yana da tashi kalar matsalar shiyasa babu bukatar ka kara masa damuwa da taka gara ka barshi shima yaji da tasa damuwar, na jima idanuwana biyu duk da bana danasanin auren samz domin bani da wata matsala dashi amma ina takaicin auren nan da uwar miji bata kaunata da wannan tunane tunanen bacci yayi gaba dani ina kwance killace cikin kirjinsa.

Da safe ya rigani tashi dan lokacin da na farka ma gani nayi baya cikin dakin kuma na san duk yadda akayi ya tafi ya samo min abinda zan cine,

Wanka na shiga nayi na fito har lokacin zuciyata babu dadi banyi wata doguwar kwalliya ba duk da na san shi uban gayyar yana son ganina cikin kwalliyar, atamfa na saka dinkin riga da skirt wanda ahalin yanzu har sun fara kamani, turare nasha ta ko ina sannan na fita falo, wurin fa ya hadu komai da akwai harda su kitchen idan kana da bukatar girka wani abu komai dai zamzam tamkar agidanka, kallo na É—an kunna dan in dan debe kewa, wayata na É—auka na kira anty,

“amarya….”

Cikin jin kunya nace “Haba anty har yanzu a amarya nake?”

“ehh mana, ko kin tsufa?”

Dariya kawai nayi nace “anty yagida ya aiki? Ina su fawaz?”

“duk suna nan lafiya…. Gashi can wurin bishra”

Hadani dasu tayi duk muka gaggaisa sannan muka yi sallama bayan ta dan kara bani shawarwarin yanda zan kula da gidana da mijina harda danginsa gaba daya duk da ban fada mata matsalata ba, su Annie na kira suma muka gaisa gaba daya sannan muka yi sallama, ina shirin kiran kawalli sai gashi ta kirani video call dariya nayi nace Æ´ar halak acikin raina kafin na daga kiran.

“amarsu ya ake ciki?” nace da ita bayan na daga kiran ina kallonta tana kwance cikin bedroom dinta,

“Ranki ya dade…..wow kawalli wanna falon fa Ina kuka je?”

Dariya nayi na fara haska mata ko ina na cikin falon zuwa bedroom da kitchen ina bata labarin zuwanmu apartment din amma kuma na É“oye mata ainihin dalilin da yasa muka baro inda samz yake muka dawo nan da naji ta matsa da tambaya ma sai kawai nace mata hutawa muka zo yi, dariya tayi kafin tace,

“lallai kina shagalinki Æ™awalli….”

“to ba dole ba” na bata amsa ina dariya tare da kallonta sosai dan cikinta har ya dan fito, mun jima muna hira kamar yadda muka saba kafin muka yi sallama na ajiye wayar, sake daukar wayar tawa nayi dan kiran samz amma kuma wayarshi a kashe nan na hakura na tashi na jona tv na fara kallon tashar mbc Drama, ina kallo ina gyangyadi da haka har ya dawo ya sameni, zama yayi gefena bayan na taro shi ta hanyar rungumeshi,

“Kin tashi daga baccin?” yace dani yana sakani gefen jikinsa,

“uhmmm…. Ina kwana?”

“lafiya lau my love, hope kin tashi lafiya?”

Kai na daga masa ina jinsa yana shafar wuyana da fuskata inda Felicia ta yayyakusheni jiya,

“Ga abincinki…..” murmushi nayi yawuna yana tsinkewa, sake maÆ™aleshi nayi kafin nayi masa kiss akan lips É—insa,

“Thank you honey…. Kai kuma me zaka ci?”

“nayi order za a kawo min yanzu…”

Sake sunbatarshi nayi a fuska nace “that’s my boo…”

Murmushi yayi ya sake kusantani da jikinsa ya soma bani abincin ina ci har sai da na ƙoshi,ban jima da kammala cin nawa ba shima aka kawo masa nashi ya fita ya karbo, nice nan na ciyar dashi kamar yadda yayi min,

“baby anjima zamu koma gida…..”

Jin abin da yace ya sani kallon shi fuskata dauke da alamar son jin karin bayani, idanuwana ya hure min da iskar bakinshi yana kallona, lumshe idon nayi na bude naci gaba da kallonsa ina zaune rashe rashe kan cinyarsa,

“me ya faru zamu koma anjima?”

“su mommy sun tafi Kaduna yau”

“ya akayi ka sani? Kaje kunyi sallama ne?”

Girgiza min kai yayi yana wasa da yan yatsun hannuna,

“naje wurin ahmad da safe”

“amma shine ka kasa karasawa wurin su??”

Zuba min ido yayi ba tare da ya bani amsa ba, ganin dagaske dai bazai amsa min ba ya sani soma tsokanarshi ta hanyar yi masa cakulkuli, rike duka hannuwana yayi yana dariya yana cemin,

“baby you are asking for trouble…… You know how i get when you touched me like this….”

Dariya nayi na yunƙura zan tashi in gudu ya rikeni yana cewa ban isa ba sake cakulkularsa nayi kafin na gudu ya tashi ya biyoni, sunkuyawa yayi na haye bayansa muka cigaba da zagaye falon har zuwa wani lokaci.

Kamar yadda yace a ranar muka bar wannan apartment din muka koma gidansa, ahmad yayiwa waya yazo ya bude mana gidan domin dama shine ya rufe bayan su mommy sun tafi, kamar yadda na tsammata komai kaca kaca kamar irin nayi shekara bana gidan, tare da taimakonsa muka gyara ko ina, Turaren tsinke na kunna bayan na gama kintsa É—akin na sake shimfida wani bedsheet din na cire wancan,

Sai da na tabbatar da yana cikin farin ciki sosai bayan mun gama shan soyayyarmu sannan na kwantar da murya na soma yi masa magana cikin jan hankali da shagwaɓa ina shafa sumar kansa wanda ke kwance saman kirji na,

“Boo…. Dan Allah ina son kayi min wani abu”

Shi duk a zatonshi wata bukata nake da ita ta kudi or something like that shiyasa yayi saurin cewa,

“Baby don’t beg me please, duk abinda na mallaka naki ne, am here for you….”

“Nagode darling but ba maganar abinda ka mallaka bane….. So nake idan mommy ta dan huta kamar nan da 5 days kaje har gida ka bata hakuri akan abinda ya faru”

“saboda me?” ya bukata yana makale hannuna guda daya cikin nasa,

“saboda ta yuyu tana fushi da kai nikuma bana son hakan, bae ka san duk duniya babu wani fushi sama da na iyaye domin annabi yace fushin Allah yana daga cikin fushin iyaye…. Duk wadda iyayen sa ke fushi dashi to Allah ma fushi yake yi dashi, dan Allah kar kace A’a kayi hakuri kaje ka bata hakuri, yin hakan ba wai yana nuna Kaine mai laifi ba a’a kawai yana nuna kai mai biyayya ne agareta da gujewa fushinta…. ”

Shiru naji ya É—anyi na É—an wasu sakanni kafin yayi kissing chest dina ya sake a karo na biyu,

“thank you baby…. Thanks for your love and care…. I love you soo much, goshinsa nayi kissing nima ina murmushi zuciyata dauke da farin cikin nasarar da nayi har ya amince da abinda nake so, ” I love you too darling…. ” na fada ina sake hugging dinsa……

*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*

 

*_Ummi Shatour_*✍

Post a Comment

0 Comments