Garin Dadi 42

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Garin Dadi 42


G*D

*Ina kuke manyan mata Æ´an Æ™walisa ma’abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haÉ—aÉ—É—un Lagos lace wanda zaku iya samun É—inkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaÉ“inki, gefe É—aya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUÆŠI GIDA…..*

{42}

~~~Lafiya lau na kwanta amma tun cikin dare nake jin ciwon kai da zazzabi sama sama yana rufeni banda uban tashin zuciya da ya sarƙafemin zuciya dan kadan kadan nake jin amai yana taso min amma dai ban tashi ba, juyawa nayi na kalleshi inda yake bayana a kwance sai dai amma ya kanainaye ni gaba ɗaya cikin jikinsa, a hankali na soma ƙoƙarin zamewa daga jikin nasa ina son tashi dan bakina ya soma cika da yawu,motsin hakan da yaji shine ya tashe shi daga baccin da yayi nisa aciki,

“Baby menene?”

Yamutsa fuska nayi kafin nace “babu komai ina son shiga toilet ne…”

“baby jikinki da zafi….. Fever ne?”

“ehh…. Harda ciwon kai”

“ayya sorry, muje idan kin dawo sai Kisha paracetamol”

Shine ya taimaka min na shiga bathroom din amma kuma na kasa yin aman sai yunkuri dai nake ta yi daga karshe dole haka ya daukoni ya dawo dani ya kwantar dani tare da lullubata dan sanyi nake ji sosai gashi kaina kamar zai fashe dan ciwo haka bakina jinsa nake kwata kwata babu dandano har wani É—aci É—aci yake yi. Da wannan zazzabin na kwana dan bai sakeni ba sai bayan asubah kuma sai lokacin na iya tashi nayi salla sannan na sake kwanciya shi kam sai faman sannu yake yi min yana tambayar ya nake ji,

“jiri nake ji sosai kamar zan fadi kuma bakina É—aci sannan duk jikina babu Æ™arfi”

“am sorry baby…. Allah ya baki lafiya,za muje hospital anjima” É—aga masa kai kawai nayi kafin na lumshe idanuwana, duk da a bukace yake dani amma sai ya hakura zuwa 11 muka shirya bayan ya kira abokinsa ahmad wanda shine yazo ya kai mu a motarshi, duk yanda nake ji da abubuwan dake damuna na zayyanewa Dr nan aka rubuta min drugs bayan tests da na yiyyi, tun a hanya nake fada masa abinda nake sha’awar ci wato alalan gwangwani kuma wanda aka saka manja ba man gyada ba, murmushi yayi yana rungume dani muna zaune abaya yace,

“baby yau kuma yar moimoi ce…. An bar maganar waina?” kai na É—aga masa ina sake shinshinarsa saboda dadin da turarensa ke yi min, hannuna daya dake cikin nasa ya murza yai kissing yace da Ahmad dan Allah ya fara biyawa restaurant kafin ya saukemu a gida, take away ya iyo min na alalan sannan ya dawo, daurewa nayi har muka isa gida sannan ya bude abincin ya bani naci sai da na gama sannan ya fita office, yana hanyar office din baima karasa ba naji yana kirana a waya, dakyar na daga saboda baccin da nake ji, ina ajiye wayarshi itama anty salaha ta kirani nan na daga bayan mun gaisa nace mata zan kirata an jima dan yanzu baccin dake idona bazai barni in fahimci komai.

Wuni nayi ina bacci dan ko sallar azahar ban yiba sai 3 da na tashi bayan na idar da salla wanka nayi duk da har lokacin bana jin karfin jikina sosai, cire wayata daga flight mood nayi na kira anty salaha muka gaisa muka dan taba hira sannan muka yi sallama, ahakan na daure na shiga kitchen saboda Dr yace in dan rinka motsa jikina,

White rice na dafa mana sai stew din kifi duk da na san ba wai lallai ni din inci ba, ina cikin kitchen Ina soya miyar ya dawo, ganina a kitchen Ina aiki ya sakashi É—an bata face ya kalleni yana hararata cikin wasa,

“baby bakya jin magana ko? Why all this?”

“sweet ba kana ji dr yace kar in rinka zama wuri daya ba, irinka yin aiki ko babu yawa ba….”

Matsowa yayi ta bayana ya rungume ni yana shafa cikina,

“to amma baby you should wait until you recovered….”

“no…. Na fada maka na gaji da ganinka kana cin abincin restaurant….”

“You no want peace baby….” yace dani yana kissing wuyana da kuncina,

Tare muka karasa girkin sannan muka tarkata muka koma falo kuma tun bayan dawowarsa bai sake fita ba muna tare manne da juna musamman ma ni dan yanda nake manne masa kamar wata cingam haka zan ta lafe masa a jiki kamar wata mage amma bawan Allah bai taɓa gajiyawa ba ko ya nuna alamar yana son in dan bashi space, Felicia kuwa duk da baya daukar kiran nata bata hakura ba maimakon haka ma ai sai canja no da tayi ta kirashi kwata kwata bai kawo cewa ita bace dan ko true caller bata nuna masa sunanta ba,

Ina kwance na bararraje a jikinsa ina kallon cartoon a MBC 3 ta kirashi, bana jiyo abinda take cewa amma shi ina jin amsar da yake bata, da farko ma kashewa yaso yayi amma sai ta tayi saurin fara rokonshi hakan yasa ya tsaya yana jiran yaji gudun ruwanta,

“Samz am very sorry for what I did…… Am very sorry pls, na san na É“ata maka rai kuma na batawa matarka but hakan bazai sake faruwa ba, I promise you”

“look Felicia, wannan kiran da kike yimin bana sonshi, kin san ina da mata, akan me zaki rinka kirana cikin dare? Duk abubuwan da kika yi abaya bai isheki ba? Kin yi niyyar batawa matata rayuwa, kin hadani da mahaifiyata tayaya kike expecting zan so ki?”

“Haba samz….. I said am sorry, please and please”

“Is ok, shikenan?”

“ina son ganinka…”

“wannan kuma bazan yi miki alkawari ba saboda bama zai yuyu ba”

“please samz…”

Jin magiyar bata ƙare ba yasa shi kashe wayar yana kallona, duk da ina jin duk abinda ya fada amma sai nayi kamar hankali na ba akan shi yake ba saboda karma ya zargi ko raina ya ɓaci,

“baby….”

“sweet….” na amsa ina sake shigewa cikin jikinsa tare da kokarin kai bakina kan nashi, karÉ“a yayi yana goga hancinsa kan nawa muna yiwa juna murmushi,

“hope dai ban bata miki rai ba….. Felicia ce take ta damuna da kir…..”

“dan Allah kabar wannan maganar ni raina bai baci ba…. Bama na son maganar please….” na fada ina lasar lips É—insa da harshena, shima biye min yayi yana ramawa idan na lasar masa lips shima sai ya lashi nawa, idan na cijeshi a lips dinsa na sama ko na kasa sai shima ya rama haka muka yita yi har sai da lokacin sallar ishah ya so kure mana dan dama duk lokacin da muke yin irin wasannin nan bama ji bare gani.

Tsawon kwanaki biyu na shafe ina fama da wannan nacaccen zazzabin mai nacin tsiya wanda kusan duk dare dashi nake kwana ga jiri da ciwon kai gefe daya kuma gaba daya bakina baba jin dandanon komai haka yake salam duk da ina fama da kwadayi kwadayi banda tashin zuciya da yake saka yawu yaita taruwar min a baki nida shi yanzu bamu da wani abunyi sai shafe shafen cikina ko fita zai yi ba zai yi min sallama ni kadai ba sai ya hada da cikin shima yayi masa tasa sallamar ta musamman ta hanyar shafa shi wani lokacin harda sunbatarsa yake yi,

Ni dai yau tun bayan fitarsa ma a kwance na wuni sai zuwa yamma bayan mun gama waya dasu mama naji babu abinda nake sha’awar ci irin wainar fulawa to amma matsalar idan ni nayi bafa lallai in iya ciba shiyasa na bari sai ya dawo, wurin Æ™arfe 5 da wani abu ya dawo ina zaune falo nasha kwalliyata cikin milk color din riga iya gwiwa mai siririn hannu marar kauri haka kuma ta É—an kamani kadan saboda kumarin da na kara yi,

“my love….” ya fada yana hadani da jikinsa,

“sannu da zuwa sweet….”

Ni da kaina na hada masa komai bayan na sanar dashi wainar fulawar da zai yi min, tare muka shiga kitchen din ina nuna masa yadda zai yi da haka dai ya soya wata ta dagargaje wata kuma tayi min yadda nake so, bayan ya gama muka dawo falo na haye cinyarsa muka ci tare,

“sweet ya maganar da muka yi na zuwanka Kaduna?”

“baby ai gani nayi baki da lafiya and kuma bana son tafiya ma na barki ke daya….”

“nifa naji sauki my love, goben dai kaje ko dan ka bawa mommy hakuri…”

Shuru ya É—anyi na wani lokaci kafin yace “baby ki bari ki kara samun lafiya sai inje”

“ni na samu lafiya, kaje tunda bawai kwana zaka yi ba”

“akan me ba zan kwana ba?” ya fada kamar gaske amma na san kawai tsokana ta yake yi,

“saboda muna bukatarka mana”

“ban yarda ba, bayan kwana biyu rowa kike yi min….”

“Nifa bani da lafiya” na fada cikin shagwaba ina turo masa baki,

“ina binki bashi ai, zaki biya one by one…”

Haka dai na samu na lallaɓashi washe gari yayi sammakon tafiya kadunan bayan na sha dogon hugging kamar babu gobe dan ya jima manne dani kafin ya hakura ya tafi ni dai ni kaina ban san wanne irin so muke yiwa juna nida mijina ba gashi sam bama gajiya da juna idan yana gida muna manne da juna idan baya nan muna manne awaya kuma tun ada ahaka muke har yanzu babu abinda ya canja maimakon ya ragu ma abin ƙara gaba yake.

Lokacin da ya isa Kaduna sun jima tare da daddy suna tattaunawa amma bawai akan mommy bane duk da dai daga baya daddyn sai da yayi complain akanta kamar yadda ya saba dan gaba daya zaman hakuri yake da ita gashi shi damuwarsa yaranta mata ne baya son ta É—orasu kan wannan halayyar tata suje gidan mazaje ana samun matsala amma ita sam taki fahimtarsa bare ta gyara, hakuri kawai samz yake bashi dan idan ba hakurin ba babu yadda za ayi da mommy, ina kitchen ya kirani ya hadani da daddy muka gaisa sannan muka yi sallama wannan karon babu kisses babu i love you saboda daddy yana nan, daga wurin daddy ciki yakarasa wurinsu mommy daga mommy sai mary saboda Hadiza ta koma school shima Abdallah haka, yanda mommyn ke fushi dashi suma su Mary haka wannan dalilin ne ma yasa ko gaishe shi bata yi ba tana zaune tana kallonsa abinda ya bata masa rai kenan har yayi mata kaca kaca yace kuma tsaf zai zaneta idan ta kawo masa raini hakuri ta bashi kafin ta tashi ta basu wuri, kujerar dake kallon mommy anan ya zauna ya gaidata ta amsa babu yabo babu fallasa dan duk da É“acin ran da take ciki da fushin da take yi dashi zuwansa yasa taji dan sauki har ta dan sauko,

“mommy na zo ne in baki hakuri akan abunda ya faru, kiyi hakuri ki yafe min sannan kiyi hakuri ki karbi matata a matsayin surukarki saboda wallahi bata da wata matsala, duk abinda ake nema wurin macen kwarai tana dashi…. Tana kyautata min tana kulawa da duk wasu hakkoki nawa….. ”

” kai din dai da kazo in yafe maka to na yafe maka amma kar ka sake sako min zancen matarka anan Samuel…. Bana kaunarta kuma bana jin zan Æ™aunace ta har abada, ai dama tun farko saida na gargadeka amma ka toshe kunnuwanka, kaje kayi gaban kanka, to wallahi mutukar kana son farin cikina da albarkata sai ka rabu da wannan yarinyar, ka saketa ta koma gidan iyayenta….. ”

” mommy wallahi bana son inji kina irin wannan maganar, saboda me zan saki matata? ”

” saboda bata dace da kai ba, ni na haifeka kuma ni nafi kowa sanin abinda ya dace da kai…..”

Duk yadda yaso ya fahimtar da mommy ta rufe idanuwanta taki fahimta ganin haka ya sanyashi tashi domin tafiya saboda yaga bambamin fadan da take ta faman yi ba mai karewa bane, cikin bacin rai tace,

” Samuel what are you trying to do? Ni mahaifiyarka ina yi maka magana zaka tashi ka fita? Nima har ta kai ta nuna maka bani da muhimmanci agareka?”

“mommy ba haka bane kawai naga maganar taki karewa ne kullum magana daya….” daga haka ya ajiye mata kudi yan dari biyar sabbi fil ya fita tana tsaye tana kallonsa cikin takaici, kafin ta koma ta zauna kan kujera cikin rashin sanin takamaimai abin yi……………

*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*

*_Ummi Shatu_*

Post a Comment

0 Comments