Garin Dadi 44

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Garin Dadi 44


{44}

*Ina kuke manyan mata Æ´an Æ™walisa ma’abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haÉ—aÉ—É—un Lagos lace wanda zaku iya samun É—inkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaÉ“inki, gefe É—aya muna da GHT product, zaku samu*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUÆŠI GIDA…..*

~~~Tagumi mommy ta rafka tana son samo mafita dan ba karamin aiki madam comfort ta haÉ—ata dashi ba, tayaya yanzu ita zata samu damar aiwatar da wannan aikin?

“No way….” ta fada a hankali bayan ta yi É—an karamin tsaki,

“mommy what’s wrong with you?” shine abinda taji Hadiza tace wadda shigowarta kenan cikin falon tana kokarin zama kusa da ita,

“Hadiza ina son inje inga halin da brother dinku yake ciki shida matarsa….”

“ahhh mommy ba kwanan nan yazo ba? Me kuma ya sake faruwa?”

“babu abinda ya faru kawai yanzu hankali na da tunanina yakoma gareshi ne ina son ganin halin da yake ciki”

“to shikenan mommy you can go tunda kince haka”

So take ta san ta inda yadace ta sanar da daddy maganar zuwanta Abuja amma ta rasa ta ina yadace ta fara, daurewa tayi tai ta maza tayi kundunbala yana shigowa taje ta sameshi da maganar,

Yana zaune ya ajiye dan ƙunshin da ya shigo dashi yana jira ta zo ya bata taje ta kafsata musu, yaji tace,

“yawwa baban Mary dama ina so ka shigo in fada maka ina son zanje Abuja cikin week dinnan….”

“lafiya?”

“lafiya lau, ina son inje inga halin da yarona yake ciki da matarsa”

“a wanne dalili? Naga bai dade da zuwa ba kuma ku dinma baku wani jima da dawowa ba, duk wannan zaman da kuka je kuka yi bai isa ya nuna miki irin halin da suke ciki ba har sai kin sake komawa yanzu?”

Cikin faÉ—a da hargagi kamar yadda ta saba ta dube shi tace” to koma can na koma na tare ai gidan É—anane ko? Sai me dan ban jima da dawowa ba na koma ”

” kinga ki bude kunnenki da kyau kiji abinda zan fada miki, tabbas gidan yaronki ne idan kin koma can kin tare babu wani aibu sai dai ni baza ayi wannan badakalar dani ba dan haka babu inda zakije ko menene ki kirashi a waya kiji, idan kuma ba haka ba kika kuskura kika sa kafa kika bar gidan nan to sai dai ki nemi wani gidan amma banda wannan dan na gaji kuma bazan dauki wannan ba… ” jin yadda yayi maganar cikin kakkausar murya yasata shan jinin jikinta dan bai taba yi mata haka ba sai yau saboda shi mutum ne mai mutukar hakuri sannan yana da kawaici ta san tunda taji yace ya gaji to ya gaji dinne kuma da alama tura ta fara kaiwa bango shiyasa ta shiga taitayinta duk da bakinta baiyi shiru ba amma ta cire maganar tafiyar daga ranta sai dai ta nemi wata hayar,haka dai taci gaba da mita shi dai yana jinta bai kara cemata komai ba dan dama ya riga da ya saba da wannan fadan nata na yau da kullum sai dai yafara gajiya lokaci yayi da yake ganin ya dace ya nuna mata karfin ikonsa shima a matsayinsa na mai gida wanda take karkashinsa,

Hakura tayi ta kira samz din ta buƙaci wasu kudade kamar yadda ta saba, bai tambayi dalilin bukatar kudin ko ya jira wani karin bayani ba ya tura mata kudin kamar yadda ya saba dan bata taba tambayarsa yace baida shi ba koda kuwa bashi dashi din saboda ya san duk abinda ya bata ko yayi mata bai faɗi ba haka kuma nasararsa tana da alaka da ita,takanas ta shirya ta je gidan maman Felicia ta sanar da ita halin da ake ciki na cewa daddy fa ya kafa ya tsare ya hanata zuwa ko ina kuma yace zai dauki tsattsauran mataki akanta idan har ta kuskura taje, bayan sun gama jajantawa daga karshe suka tsayar da matsaya guda daya na cewa madam comfort zata koma inda ta karbo maganin inyaso sai a canja dabara.

***

Yau tunda asuba da na hau online naga yaya Abdul hakim ya turo pic din baby ta WhatsApp group din yan gidanmu wai ƙawalli ta haihu misalin ƙarfe 2:30 na dare dama jiya tace min edd dinta ya cika har ta dan gota da kwana biyu kuma har yanzu bata jin ciwo ko alamun komai, wani tsalle naso in tashi in daka amma sai dai babu dama duk da haka ban kasa nuna farin cikina ta wata hanyar ba, samz dake kusa dani kam shagwabe fuska yafara yi saboda zan tafi Kano in barshi, dariya nake ta yi masa harda gwalo, hoton babyn naketa kallo wanda kana gani kasan yan gidanmu ya iyo sambalele dashi,

“baby idan kika je kwana nawa zaki yi?” Ya bukata yana kallona fuskarshi ta nuna alamun wai in tausaya masa, dariya nayi na rungumeshi sosai cikin kirjina nace,

“duk yanda kace my love…
Idanma kace kar naje ai haka zan hakura”

“a’a zaki je but bana son ki tafi ki barni” ya faÉ—a yana shafa cikina,

“kaima ai zaka je, bazan tafi in barka ba my love….”

“kwana nawa zakiyi?”

“duk yadda kace sweet”

“2 days yayi?”

Murmushi nayi na É—aga masa kai duk kuwa da nasan kwana biyu yayi min kaÉ—an tunda harme ma nayi akwana biyu na dawo? Ni ai da gani nake ma sai nafi 2 weeks dan rabona da Kanon anjima,

“yayi miki kaÉ—an ko?”

“uhmmmm” nace ina É—aga masa kai, hannuwana ya riÆ™e duka biyu cikin nasa yana matsawa a hankali,

“to ki faÉ—a da kanki yanda kike so”

“ni idan yadda nake so ne kawai dai sai ka ganni fa saboda babu rana”

Dariya naga yayi kafin ya girgiza kansa “Haba baby guduwa zakiyi ki barni? I need you”

“to ai kaga na jima fa banga Æ´an gida ba”

“Tom shikenan…. Amma keda kika ce da ba zaki je ba sai kin haihu”

“tab dane ai, yanzu na fasa zan je”

“kin zama marar kunya dai yanzu”

Dariya nayi dan ji nake tamkar inyi fuffuke in tashi in ganni acikin Kano, tun daga ranar na fara hada kayana sai kace idan na tafi na tafi kenan shi kansa sai da yace “baby wannan kayan ai yayi yawa ko ba zaki dawo bane?” hakan da naji sai kawai na ajiye kayan sai iya abinda zan buÆ™ata acan kawai na É—auka sai kuma kayan baby da na diddiba dama kusan komai guda biyu nake siya saboda ita, shi kam kudi yasaka min a account É—ina wai idan naje na Æ™ara siyama baby kaya before yazo,

Sai da aka yi haihuwar da kwana biyu za a shiga na uku sannan ya sama min ticket saboda yanzu ba a fiya zirga zirga sosai ba saboda canje canje da aka samu na yanayin rayuwa, kullum sai munyi video call da ƙawalli naga babyn wanda har anyi masa huɗuba da sunan Abbanmu amma za a ringa kiran shi da Irfan wannan sunan dama tun kafin ƙawalli tayi aure take riƙe dashi a ranta wai shi zata sakawa ɗanta shiyasa tana faɗa min nace to Alhamdulillah su ƙawalli buri ya cika,

Tamkar idan na tafi bazan dawo ba haka samz ya zame min duk yabi ya hanani sukuni sai jagwalgwala ni yake saboda gobe jirgin safe zan bi kusan bai barni nayi baccin kirki ba yanzu naga wani tashen jaraba yake koda yake dama tun farko kusan hakan yake kuma da haka ya horani nima, yau dai sai da ya gama tara min gajiya sannan ya barni shiyasa da bacci a idona sosai na isa Kano,

Kai tsaye gidana na wuce na sauka ai kam gida kamar na shekara bana nan dan ko ina ya haÉ—a datti ya fita kamanninsa, mai gadi na yana nan yana kula da duk inda ya kamata kuma duk karshen wata samz yana biyansa albashinsa, iya inda zan iya gyarawa kawai na dan karkade na goge sauran na bari sai an nutsu, wayata na kunna na kirashi video call,

“baby, i miss you…”

“I miss you too my love, kaga gidana yadda yayi datti?”

“haka zaki zauna cikin datti?”

“a’a zanje gidan Æ™awalli acan zan kwana sai bayan suna sai in koma gida inyi kwana biyu sannan sai in dawo kaga kafin lokacin na turo an gyara min…”

“to shikenan baby…. Allah ya kiyaye, i love you”

“I love you too….”

Sallama muka yi na tashi na tattara duk abinda zan tattara cikin madaidaicin akwati sannan na kai motata wadda ke rufe sai yanzu nasa aka bude min aka gyara, gidan ƙawalli na nufa batare na sanar mata ba nafi son kawai sai dai ta ganni, ai kuwa lokacin da na isa gidan cike yake da dangi yan gidanmu da yan gidansu wai har su bishra da suka fini nisa sun rigani zuwa ganina yasa gidan ya rude da murna kowa sai tsiya yake yimin saboda ba kowa ya san inada ciki ba. Ai tsokana na shata awurin yan gidanmu dan har maza ba iya mata ba shi yaya Abdul hakim lokacin da ya ganni ma cewa yayi wai,

“wa nake gani wannan kamar zata fashe?” kowa sai da yayi dariya banda ni wacce ta turo baki kamar zanyi kuka, bamu samu keÉ“ewa da Æ™awalli ba sai bayan sallar ishah lokacin kusan kowa ya tafi sai iya bishra da kanwar Æ™awalli Kubrah sai kakarsu gwaggo, nidai ina É—akin mai jego acan na sauka sai lokacin take bani labarin haihuwa duk sai na ji na tsure dan tace min anyi mata É—inki yafi a Æ™irga shiyasa naga tana ta tafiya daÆ™yar, har 9 ta wuce hirar da muketa yi kenan wato ita mace dai komai sai ta sha wahala ko an haihu lafiya rainon É—an ma babu sauÆ™i sai dai Allah yasa mu dace kawai, kasancewar akwai bacci a idona wanka nayi nazo na saka rigar bacci ina shirin kwanciya kiran samz yana shigowa dariya naji Æ™awalli tana yi tare da faÉ—in “ashe dai har yanzu kuna nan da wannan shegen Æ™ulafucin junan keda wannan mijin naki”

Ban kulata ba na É—auki wayar ina ce masa “am sorry Bae ban manta da kai ba yanzu nake son in kiraka nima, bacci nake ji…”

“bacci tun yanzu baby….”

“ba jiya ka hanani bacci ba….” na fada ina turo baki, dariya naji yayi kafin ya fara rarrashi na nikam na samu abinda nake so nan nayita zuba masa shagwaba bayan na hadasu da Æ™awalli sun gaisa yayi mata barka ita kuma tayi godiyar kayayyakin da muka kawo, wallahi dakyar na iya bacci daren yau saboda na saba koda yaushe sai yayi min tausa ya matsa min jikina kafin nayi bacci……….

*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*

*_Ummi Shatu_*

Post a Comment

0 Comments