Garin Dadi 48

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Garin Dadi 48


{48}

*Ina kuke manyan mata Æ´an Æ™walisa ma’abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haÉ—aÉ—É—un Lagos lace wanda zaku iya samun É—inkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaÉ“inki, gefe É—aya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUÆŠI GIDA…..*

~~~Yau da wuri na tashi na shiga kitchen na shiryawa samz breakfast saboda shima da wuri zai fita office domin acewarsa akwai baƙi da zasu zo musu saboda wani gagarumin aiki da zasuyi,

Duk da yana sauri dankali na soya masa sannan nayi masa sos din kwai na haÉ—a masa tea na kai masa lokacin har ya fito daga wanka yana shiryawa, kayan breakfast din na ajiye sannan na karasa na taimaka masa ya gama shiryawa na dauki turare na fesa masa ina kallonsa cikin yaba shigarsa ta yau domin suit ya saka blue black amma rigar ta ciki fara ce sai necktie da ya saka,

“kayi kyau sosai sweet…. Kamar in hanaka fita” na karasa maganar cikin shagwaba,

“tnx darling but kar ki hanani fita i beg….”

“to zauna kayi breakfast sai ka tafi….”

“duk yadda kika ce haka za ayi my love”

Sosai yaci abincin kafin yayi min sallama ya tafi wanda sai da na raka shi har ƙofa sannan na dawo na kwanta bayan na rufe ko ina saboda bacci nake son in koma in dan yi,

Ban fi 20 minutes da kwanciya ba naji knocking, jin knocking din ba mai karewa bane ya sani tashi ina mamakin waye kuma yanzu? To ko shine yayi mantuwa ya dawo? Da waÉ—annan tunane tunanen dai na karasa, ina budewa naga Samha matar Kabir, murmushi nayi nace,

“Hajiya Samha kece, sannu da zuwa”

“yawwa sannu, ga baÆ™uwar sassafe” ta faÉ—a tana kokarin shigowa nan na bata hanya ta shiga nabi bayanta, daga ita sai rigar bacci sai hijabi, hira muka dan fara yi tun 9 da tazo har kusan azahar nan kuma naji abin yafara damuna domin inada aikace aikace na da nake son inyi, ina son in gyara gidana in wankewa mijina inner wears dinsa da kayan baccinsa kuma ina son in danyi bacci kafin ya dawo ko dan in bashi lakacina sosai amma taki fahimtar hakan bare ta tafi nikuma bana son in fito in fada mata ko in shiga ciki in barta taga kamar kora da hali nake yi mata amma duk mace mai hankali tunda kika zo tun safe anan kika karya ai ya dace ki tafi gidan ki kuma tun ana marmarinki ba afito ance ki tafi ba,

“Hajiya Samha naga azahar ta kusa bari na tashi akwai yan ayyukana suna nan jingim banyi ba suna jirana….”

“har wani aiki gareki widat? Aikin nawa yake? Ni kin ganni nan wallahi tunda na tashi ko tsinke ban dauke ba daga gidana na fito, ke ko gadon da muka kwana ma haka na fito na barshi kuma bana jin zan iya gyarawa”

“to ai ke amarya ce, har yanzu kina cikin dokin amarci nikuwa fa?”

“a’a wallahi kawai dai abinda na lura dashi shi namiji zuma ne sai da wuta dan daga lokacin da ka nuna masa kai wahalalle ne tofa a wahala zaka kare amma idan ka nuna masa kai ma dan hau ne sai kiga kun daidaita….. Wasu matan fa dan wahala har wanki suke yiwa miji wai, ni hauka nake zan yiwa namiji wanki, wallahi sai dai kar yasaka kayan ”

Tunda naji irin kalamanta sai na sha jinin jikina bance komai ba sai murmushi da nayi nan taci gaba da mitarta akan wai ita ba zata zauna ta bautawa namiji ba bata son wahala bla blah blah daga karshe dai ta tashi ta fita kuma shi dinma da tayi min sallmar ba gidanta ta shigaba ina hangota ta window din bedroom dinmu lokacin da na shiga ina tattara kayan da zan wanke, can kasa ta sauka ta shiga wani apartment din, nidai ko kadan kalamanta basuyi tasiri a gareni ba domin kowa da irin fahimtar sa da kuma tarbiyarsa har gobe mazan gidanmu sune suke kaiwa Abbanmu wanki su biya kuma before su fara aiki su yi aure sune suke yi masa wanki tas yayin da sukuma su Annie sune suke wanke masa kananan kaya kuma har gobe basu daina ba shiyasa ni a ganina wannan ba wai wahala bace kyautatawa ce, nima kuma tunda nayi aure nake wannan hidimar amma dukka kayana samz ke hadawa da nashi ya bayar wanki,

Ina kokarin shiga bathroom inyi wankin naji yana kirana a waya nan yake sanar dani sun gama meeting din may be ma yau da wuri zai dawo gida, sallama muka yi na shiga nayi aikina na gama na wanke toilet din nazo na gyara gidan sannan nayi wanka na dora girki,zuwa Æ™arfe uku na fita na É—an shiga maÆ™ota kamar yadda naga dacewar hakan kowanne gida na shiga kuma dukkansu ba wasu manya bane wasu zasuyi sa’anni na wasu kuma koda zasu girmeni to da kadan ne dan dukkansu babu wadda tayi haihuwa uku daga biyu sai mai É—aya, mace daya ce na ganta da dan girmanta dan yaran ta ma sun kai biyar kuma duk ciki tafi nutsuwa ko dan dama bama za a hada hankalinta da na sauran ba tunda tafisu shekaru kuma a gidanta ma na dan fi jimawa saboda tana ta bani shawarwarin in iya takuna kuma in iya bakina a compound dinnan domin akwai matsala, idan har baka iya bakinka ba yanzu zaka ji sirrin ka da duk wani abu da ya shafeka awaje haka kuma inyi takatsantsan, to ni dai ta barni a duhu dan bata fito fili ta fayyace min meyake faruwa acikin compound dinba amma duk da haka na dan fahimci wani abu kadan, sallama nayi mata na tafi inata mamaki da tunani kala kala saboda tace min duk ciki itace ta fara zuwa kowa anan yazo ya sameta ita asali daga jihar Borno suka dawo ita da mai gidanta wanda ya samu canjin aiki ana kiran ta da Hajja Gana,amma wannan hannunka mai sandar da tayi min yasa naji bana sha’awar yin mu’amala da kowa a cikin compound din sai dai kawai hakkin musulunci amma bazan shiga jikin kowa ba kuma bazan bari kowa ya shiga jikina ba zan zauna da kowa nesa nesa dan naga kamar dukkansu kansu yana rawa ciki harda Samha. Ina komawa sallar la’ asar nayi na sake gyare jikina na sauya shigata daga wacce naje da ita unguwa nasake wata sabuwa inda na saka wata fitinanniyar riga three quarter purple color mai Æ™aramin hannu, wuyan rigar a bude yake gaba É—aya shiyasa kusan rabin Æ™irjina awaje yake, sarka da dan kunne na saka masu jan hankali domin sarkar ta shige har tsakiyar Æ™irjina da yake doguwa ce haka dan kunnayen sun sauko har kan kafaduna suma, turarena wanda nake amfani dashi musamman idan ina gida shi nabi na shasshafa har cikin cibiyata da bayan kunnena da sauransu fuska ta ban yi mata wani havy makeup ba light nayi yanda zan fi daukar hankalinsa, Æ™arfe shida daidai ya dawo, ina falo ina kallo dama aikin kenan kallon series sai ko karatun novel, kiransa da ya shigo cikin wayata shine ya katse min kallon da nake yi na dauka ina yanga tamkar yana kallona,

“Sweet ya….?”

“Baby am back…..”

“Awwwwn…. Am coming dear”

Da gudu naje na buɗe ƙofar ina budewa na koma ciki na labe yana shigowa bayan ya rufe ƙofar na ɗale shi duk kuwa da cewa yana riƙe da jakar computer ɗin shi da baƙar leda wadda ban san me ya siyo mana ba aciki,

“Baby…..” na ji ya kirani cikin shagwaba alamar a gajiye yake, kayan na karba muka karasa ciki yana ta aikin kallona kamar yau yafara ganina, ai muna zuwa ya janyoni jikinsa ya soma sinsinata yana wasa da sarkar da nasa,

“wow… baby kinyi kyau, come closer please…..”

“nayi kyau a hakan?” na bukata cikin shagwaba,

“yes nah…” ya bani amsa yana murmushi, yana ta santin kwalliyata na samu na rage masa kayan jikinsa na cire masa socks da rigar jikinsa daidai lokacin kuma kiran mahaifiyarsa ya shigo ya É—auka ina jin alamun itace na kwashi kayan na basu wuri na wuce bedroom na kai sannan nazo na wuce kitchen naje na kwaso warmers É—in abinci na kawo, ledar da ya shigo mana da ita na dauka fruits ne aciki sai kilishi duk da shi baya ci amma ya kan siyo min saboda ya fahimci ina so,

Fruits din na yanyanka na hada masa komai yadda ya dace kafin na koma bedroom din na wuce bathroom na hada masa ruwan wanka na fito na nemi wuri na zauna ina jiran sa yagama ya shigo dan bana son in zauna inji abinda suke tattaunawa tunda kowa da muhallinsa. A can falo kuwa samz ya sake sosai yana shan hira da mommy domin yau ta sigar da tazo masa daban babu fada babu complain babu komai sai bincikar lafiyarsa da kuma halin da yake ciki nan ya zauna yake sanar da ita dukkan abubuwan dake faruwa a office da kuma canjin gidan da muka yi amma bai sanar da ita dalili ba nan take ce masa to ya kamata dai ya dage yayi saving kudinsa har yasamu ya mallaki gida a Abuja ya huta wannan gidan hayar, hira suka yi mai dadi sosai wacce rabon da su yi irin ta har ya manta yau ya sake yayi hira da mahaifiyarsa wacce yajima bai samu wannan damar ba, har aka kira salla aka idar yana kan waya nidai har na kosa na gaji da saurarensa har nayi salla na idar na zauna dan karanta alqur’ani, sai can naji shigowarsa, karasa rage masa kayan jikin nasa nayi ya shiga wanka nikuma na fito masa da kananun kaya wanda zai sha iska babu takura, jiransa nayi har ya fito ya shirya sannan muka koma falo bayan yayi salla, ina kwance jikinsa yana tambaya ta yau me da me nayi nake bashi labarin zuwan matar abokinsa wato abokin aikin sa Kabir, dariya yayita yimin jin nace ita ta hanani bacci dan muna tare har azahar. Hmm kamar da wasa sai Samha ta mayar da zuwa gidana kamar wani ibada dan kullum sai tazo sannan gashi bata la’akari da ko mijina yana nan ko baya nan, idan yana nan sai dai ya koma bedroom yabar mana falo sannan kuma hakan bazai sa ta tafi da wuri ba, koda cikin weekend ne haka take zuwar mana ta baro nata mijin ni wannan abu yana daure min kai kuma yana bani haushi dan gaskiya ni wannan zuwan nata yana takura min kuma ma sai naga kamar tafi zuwa idan samz yana nan wannan dalilin yasa na fara gajiya na daina bude mata Æ™ofa koda yaushe amma hakan fa baisa ta daina zuwa ba,

Yau muna baje falo muna kallo nayi É—ai É—ai kan jikinsa kamar yadda na saba kwanciya jikinsa kamar wata mage, wayar shi ce tayi kara ya dauka, ji nayi yace,

“ehh muna tare gata…” kara min wayar yayi a kunne ni wallahi duk tunanina ma ko acikin yan gidanmu ne wani ya kira wayata bai samu ba shine ya kira wayar sa amma me ina magana naji muryar makociyata Samha………..

*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*

*_Ummi Shatu_*

Post a Comment

0 Comments