Garin Dadi 49

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Garin Dadi 49


{49}

*Ina kuke manyan mata Æ´an Æ™walisa ma’abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haÉ—aÉ—É—un Lagos lace wanda zaku iya samun É—inkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaÉ“inki, gefe É—aya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUÆŠI GIDA…..*

~~~Cike da mamaki gami da hasashe kala kala da tunani iri iri nama kasa magana dan tambayoyin dake kai komo cunkushe cikin raina sun hanani lalubo ko kalma kwaya daya da zan tarbeta da ita, shin meya hadata da mijina? A ina ta samu no dinsa? Wanne dalili yasa ta kira no dinsa? To dama ta taɓa kiran sa ne ko kuma wannan ne karo na farko? Duka wadannan tambayoyin fa ina bukatar amsarsu sai dai a wurin wa zan samu?

“hello neighbor kina jina?” naji ta bukata daga cikin wayar, wani gwauron numfashi na sauke kafin na amsa mata a dakile,

“ina jinki, amma lafiya?”

“lafiya lau wallahi, ai kinga yau ban leko ba bana É—an jin dadine kuma wallahi na wuni ban iya cin komai ba shiyasa nace bari na kiraki ko zan samu wani abu in ci…..”

“ba zaki samu ba dan nima yau banyi girki ba” daga haka ban jira cewarta ba na katse wayar duk da haka ban hakura ba sai da naje na danna mata block sannan nayi delete no din shi dai yana zaune yana kallo na baice komai saboda shima din yayi mamakin yadda aka yi ta dauki no dinsa a wayar mijinta ta kirashi dan ko tantama ba yayi wannan ita kadai ce hanya daya da zata iya samun no dinsa,

“baby….” naji ya kirani yana wasa da zanen dake gaban rigata wanda aka rubuta _Hello Kitty_ shiru nayi masa ban amsa ba saboda matar nan ba Æ™aramin É“ata min rai tayi ba, ya za ayi ta wani kirawo mijina dan kawai tana nemana akan buÆ™atarta?

“Hello kitty…..” ya fada cikin tsokana, “what?” na bukata bayan nayi kicin kicin da fuska alamar ina sama,

“sweetheart nikuma menene laifi na? Me nayi?”

Shuru nan dinma nayi tunda idan zanyi masa adalci kam shi ai bashida da laifin komai tunda yana zaune ta kira shi, ban kai ga lalubo amsar da zan bashi ba sai ga wani kiran daga Felicia wannan kam kin ɗauka yayi kamar yadda ya saba ƙin ɗaga wayarta ita kuma gata da shegen naci nan ta kafa kira hakan ya sake kular dani,

“dan Allah ko ka É—aga kiran nan ko ka saka wayarka a silent dan wallahi nidai an dameni…..”

ÆŠaukar wayar tashi yayi yabar falon ya wuce cikin bedroom hakan ya sake tunzurani gashi ya tafi ya barni cikin tunani shin zai dauki wayar ne ko kuma me ya tafi yi cikin dakin? Wata zuciyar ce ta rinka zugani akan in bishi inga me yake yi, nan dai na kasa hakura na tashi na bishi, akan gado naga wayar tashi a ajiye shikuma ya shiga bathroom, to nikam yau dai ko inje in dauki wayar nan tashi ne inyi abinda ban taba yiba wato bincike? Kul wallahi ahir dinki Maimunata kina zaune da mijinki lafiya kuna kaffa kaffa da juna kar ki kuskura ki ganowa kanki abinda zai hana ki zaman lafiya da mijinki domin duk dadinka da miji to ka nisanci wayarshi,

Wannan shawarar ta daya zuciyar tawa nabi na koma falo jiki a sanyaye na nemi wuri na zauna duk kallon da nake yi ya fita daga kaina ma, amma fa ya zama dole in takawa wannan yarinyar samha burki kar ta kuskura ta sake kirar min wayar mijina duk da ma dai nayi blocking dinta,

Ina nan zaune ni ba kallon nake ba ban kuma tashi ba ya fito, “baby lets hang out…..”

“Awwwwn…..” na fada ina tashi tare da rungumeshi, a gurguje naje na shirya na saka bakar abaya na fito ba tare da nayi kwalliya ko na shafa turare ba, ba wani nisa muka yi sosai ba amma dai duk da haka fitar ta sakani farin ciki dan har video call muka yi da kawalli na nuna mata inda muka je, Irfan ta hasko min wanda yake kwance yana bacci yayi bulbul dashi kai bama shi kadai ba gaba dayansu sunyi bulbul dasu saboda yanzu suna wata na biyu ne,

“Æ™awalli dan Allah nima ki sakani acikin addu’a in samu cikin nan in haihu…..”

“oh Allah gaggawar me kike? Wato har kin manta ko? To kar kiyi mamakin yanzu haka ma kina dashi….”

“yanzun dai babu sai dai Allah ya kawo…..”

“Allah yakawo mai albarka kawata”

“amin” na fada a marairaice, daga nan muka yi sallama, zuwa 9 muka koma gida. Bayan kwana biyu da samha ta shigo ban sakar mata fuska ba kamar yadda na saba sakar mata dan har ga Allah ni na gaji da lamarinta so nake ta daina shigo min gida dan soki burutsunta yayi yawa sai tazo tana yi min wasu maganganu na rashin hankali wai dan Allah ina gamsuwa da mijina, ido na zuba mata fuskata babu walwala nace,

“samha wai meke damunki? Menene naki na yimin wannan maganar? Wannan fa sirrinane tsakanina da mijina idan har na fada miki wacce riba zaki samu?”

“ehh gaskiya sirrin ki ne kam amma abunne yake bani mamaki, ni wallahi mijina bana wani samun abunda nake so, kamar ba namiji ba dan tunda muka yi aure nidai banji abinda ake ta kozozozon ana ji ba….”

“to wannan ai kuma keda mijinki ya kamata ku zauna ku tattauna har ku samu mafita bawai ki zo kina fadawa duniya ba….”

“Wallahi sis abunne yake damuna shiyasa, kuma mafita nake nema shiyasa…..”

“ki samu mijinki ku tattauna shine mafita…..”

“ai bama lallai ya tsaya ya saurareni ba….”

“Allah ya kyauta” abinda nace kenan saboda bana son mu tsawaita maganar ma bare ta kaini gaba nan muka bar maganar duk da haka ban sake mata ba,

A halin yanzu dai ƴan mata biyu ke bibiyar samz bayan Felicia akwai wata wadda shima kansa bai san wacece ita ba sai dai yana mamakin ta yadda ta san abubuwa da dama game dashi ciki kuwa harda ni matarsa ta sani kuma tana ikirarin sai ya sakeni ya aureta bai taba fada min ba nima kuma ban bincika ba dan na san bin diddigin miji bai da amfani, ita Felicia kam dama na san da zamanta kuma na san zabin mahaifiyarsa ce shiyasa abin ban saka shi araina ba amma ita wannan dake bibiyarsa itace tashin hankali na a yanzu kuma na fuskanci hakanne a yau din nan da misalin ƙarfe 11 aka danna min doorbell har kusan sau biyar da yake na shiga wanka, ina fitowa da na buɗe banga kowa ba sai wata babbar paper bag fara nan na kinkima na shiga da ita ciki tunda banga kowa ba ta yuyu wanda ya kawo din shine ya ajiye bayan ya jira yaji shiru,

Zama nayi na soma fito da kayan ciki, wani ɗan ƙaramin box na fara cin karo dashi ina budewa naga zoben azurfa mai kyau, sannan sai wani turare oad na maza shima acikin gidansa sai agogo mai masifar kyau shima acikin gidansa sai kuma greeting cards guda biyu irin wanda masoya ke turawa masoyansu a lokacin bikin wani shagali dan tayasu murna, a jiki ba a rubuta komai ba amma an nuna ana taya shi murnar zagayowar ranar haihuwarshi,ai ji nayi kamar inyi me dan baƙin ciki kuma ban taba sanin inada zafin kishi ba sai yau dan wuni nayi cikin baƙin ciki da damuwa, yana ta kirana normal call da video call kamar yadda ya saba duk lokacin da yake office wuni muke muna waya indai bawai aiki ne yayi masa yawa ba amma yau naki ɗauka haka kuma babu abinda nayi a gidan sai aikin kuka da nasha wannan kam nayi na kara kamar babu gobe dan har sai da idanuwana suka kumbura, haka na wuni naki ci naki shan komai kamar wata mai azumi shi dai yana can baima san abinda yake faruwa ba duk tunaninsa bana tare da wayar ne ko kuma ina ta baccin nawa na sabo, sai da naji yunwa na neman illata ni sannan na hada tea na sha,

Ƙarfe 6 da yan wasu mintuna ya dawo kuma yana waya da mommy ya shigo kamar yadda hakan yazama al’adarsu yanzu, ban wani saurareshi ba yau babu hugging babu kisses babu magana haka na bude masa kofa ina budewa na juya na wuce cikin bedroom, bin bayana yayi da kallo ya zauna a falo a gajiye kuma a kasalance ya ajiye jakar laptop É—in shi dama yau bai shigo da komai ba saboda jiya ya sissiyo min duk wasu kayan tande tande da makulashe suna nan cike a fridge dina,

Sai da ya kammala wayar sannan ya lura da kayan dake gefensa kan kujera nan ya dudduba cike da mamaki dan ya san bani na siya masa ba da nice ba ta haka zan bashi ba to amma waye ya kawo? Ganin baida wanda zai bashi amsa yasa shi tashi yabini cikin bedroom,amma bani ba hatta shi yayi mamakin ta yadda aka yi koma wacece wannan ta san yau birthday dinshi kuma duk yadda akayi tayi bincike sosai akansa.

Ina kwance ina wani sabon kukan ya shigo, zama yayi gefena yana kamoni zuwa jikinsa, “baby meke faruwa? What’s wrong with you?”

Jajayen idanuwana na daga ina kallonsa raina a bace,

“baka ga kaya a falo ba?”

“na gani, waye ya kawo?”

“kafini sanin wanda ya kawo ai tunda ga dukkan alamu soyayya kake yi da ita saboda gashi nan har ta san yau birthday dinka ta aiko maka da gift har gida…..”

“Baby wai ya kike magana kamar irin na san komai dinnan…. I know nothing about what you are saying…… I don’t know who’s behind this….. Trust me….”

Ido na tsura masa ina son gano gaskiyar abinda yake fada min nan naga shima ya saka nasa cikin nawa hakan ya tabbatar min da duk abinda yake fada gaskiyane domin da ba gaskiya bane bazai iya hada idonsa da nawa ba, rungumeshi nayi ina kuka duk da hakan na kasa saukowa daga fushin da nayi, shikuma dama ya jima yana receiving massages na wata yarinya wai Suhaila amma bai taba daukar abin serious ba bare har ya kulata to ko itace ta aiko masa wannan kayan? Wannan shine tunanin da yaketa yi amma baya son in gane shiyasa yayi saurin katse tunanin, dakyar da rarrashi ya lallabani na sauko dan tsabar yana son in saki raina shine ya shiga kitchen ya dafa mana noodles duk da ni nake fada masa wasu abubuwan gudun kar ayi kwaba, ina zaune ina kallonsa ya gama dafawa ya soya kwai sannan muka koma falo. Tamkar wata baby koda yake yace ni din baby ce a gareshi haka ya zaunar dani ya rinka bani a baki duk da girkin nasa ya danyi yaji kadan amma haka na daure naci yau dai na sha soyayya kamar wata sabuwar amarya ni kaina na san nayi dacen samun miji mai sona sosai wanda baida wani buri sai na ganin farin cikina,

“baby ina ta sauri in dawo gida kuma shikenan sai in zo in sameki kinata kuka….”

“wancan kayan fa ka san yadda zaka yi dasu dan wallahi ba zasu zauna min a gida ba…”

“au ba zaki barni in saka ba…?” ya bukata cikin tsokana ai yunkurawa nayi zan tashi yayi saurin danneni da gefe daya na jikinshi, ina shirin fara yi masa tsiwa ya rufe min baki da nashi dan dole nayi shiru na hadiye maganganun da nayi niyyar fadi ada,

Washe gari ban san ya yayi da kayan ba na dai ga ya fita dasu kuma ni dai tun daga wannan lokacin hankalina yaki kwanciya dan na fahimci koma wacece wannan to da gaske take kuma a shiryenta tazo, duk da na yarda da irin soyayyar da mijina yake nuna min amma nidai ina tsoro ina tsoron kar yarinyar nan tayi tasiri acikin zuciyarsa har ya raba soyayyar da yake yimin ya sammata,wannan al’amari shi yake sake tayar min da hankali har yake É—arsar min da tsoro mai girma cikin zuciyata, gashi dan jaraba kullum sai ta turo masa massage ko gajiya bata yi, ita tana yi Felicia tana yi sun sakani a tsakiya suna kokarin kwatar min miji ta kowanne hali,

Anty na kira ina kuka na zayyane mata dukkan damuwata nan ta kwantar min da hankali kuma ta babbani shawarwari akan yanda zan rike mijina da kyau sannan in sake bada himma wurin kyautata shi da bashi farin ciki haka kuma in manta da duk wata mace dake kawo masa hari in rage wannan zafin kishin nawa in kula da mijina, haka kuma in kula da hakkinsa sosai na shimfida in daina wannan ragwantar dan na fada mata ni yanzu tunda na rabu da wannan cikin na daina daukar dawainiyarshi yadda ya kamata dan yanzu a sati baifi sau biyu ba nake iyawa shima dakyar sai da rarrashi da lallabawa amma lokacin da ina da ciki duk lokacin da yazo ina maraba, faÉ—a tayi min sosai tace in rinka daurewa kuma inyi hakuri a kowanne lokaci kowa haka yake hakuri, mun jima sosai da anty tana bani shawarwari kafin muka yi sallama, dan aikace aikace na nagama na kwanta dan in dan rage bacci kafin lokacin girki yayi, ina kwanciya naga ya kirani video call dauka nayi ina lumshe idanuwana……..

*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*

*_Ummi Shatu_*

Post a Comment

0 Comments