Garin Dadi 50

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Garin Dadi 50


{50}

*Ina kuke manyan mata Æ´an Æ™walisa ma’abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haÉ—aÉ—É—un Lagos lace wanda zaku iya samun É—inkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaÉ“inki, gefe É—aya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUÆŠI GIDA…..*

~~Shima lumshe idanuwan yayi kamar yadda ya ga nayi sannan cikin sanyin murya yace,

“Hey baby…..”

“hey boo…..Ya aiki?”

“we thank God, am just wanna check you…. Yakike”

“awwwwn….. Ina lafiya but am missing you”

“zan dawo soon, me za a bani idan na dawo anything for me?”

Idanuwana na sake lumshe masa sannan na shagwabe murya,

“I kept something special for you darling……”

“are you serious?”

“yes dear….”

“ok zan zo da wuri baby, i love you”

“I love you too”

Sallama muka yi na ajiye wayar ina dariya saboda maganar da ya fada ta karshe wadda cikin raÉ—a ya fada kamar baya son kowa yaji,

Ina cikin baccina mai daɗi naji wani ƙaddararren bugun kofa wanda ya tadani dan dole, nan na zira hijabi na fita fuskata babu yabo babu fallasa tunda daga bacci na tashi, lokacin da na bude wasu fararen yanmata na gani guda biyu amma daya tafi daya tsayi dukkansu sun sha abaya sai kamshi suke, sannu da zuwa nayi musu kafi na basu hanya suka shiga ciki nikuma na tsaya a kitchen na dauko musu ruwa da lemo nabi bayan su dashi,

“Ina yini…” suka ce dani atare fuskokinsu duk dauke da murmushi,

“lafiya lau, yagida”

“lafiya lau….” suka sake amsawa a tare,

ÆŠan shiru falon yayi kafin na katse shirun ta hanyar cewa “kusha ruwa mana sannan ban gane ku ba….”

“ehh gaskiya ba zaki ganemu ba saboda baki sanmu ba in fact ma baki taba ganinmu ba”

“ehh hakane gaskiya” na fada ina sake kallon su daya bayan daya dan na kasa ganewa shin Æ™awaye ne ko kuma yaya da Æ™anwa ne,

“ni dai sunana Malika wannan kuma kawata ce sunanta Suhaila…..”

“ayya Allah sarki” na fada ina murmushi dan wacce tayi maganar itace babbar wato doguwar ciki,

“Maimunatu kamar yadda Malika ta sanar dake sunana Suhaila kuma nazo wurinki ne da wata babbar buÆ™ata wadda Æ™arama ce ta wani bangaren bata da girma….. Amma dan Allah ki fahimceni”

Gyara zamana nayi sosai ina fuskantarsu dan jin meke tafe dasu,

“ina sauraronki….”

“Da farko dai ina yi miki albishir da cewa mun zo miki da alkhairi har gadon barcinki…. Kamar yadda na fada miki wata yar bukata ce ba mai girma ba sai dai amma ta yuyu ke ki dauketa da girma, Maimunatu idan har kin amince da bukatata to zan mallaka miki abubuwa da yawa na more rayuwa, haka kuma zan fitar dake duk Kasar da kike so banda sauran kayan alatun rayuwa da zan mallaka miki…. ”

” baiwar Allah har yanzu baki fadi bukatar taki ba sai wasu maganganu kike yi daban…. ”

” calm down…. Zan fada miki amma ina so muyi yarjejeniya ne ta yadda ni dake zamu saka hannu da shaidu da komai…. Tun ranar da Allah yasa idanuwana suka sauka kan mijin ki naji bani da wani abu da nake so sama dashi, ban farga da cewa yana da aure ba har sai bayan da na nutsa cikin kogin sonshi, nabi duk wata hanya da ta dace dan ganin nasamu attention É—insa but all in vain, daga Æ™arshe naga bani da wata hanya wacce zan iya bi har ta kai ni ga nasara face ke… Ke kadai ce zaki iya taimaka min wurin samun soyayyar mijin ki domin a yanda labari yazo min bashida wani abu da yake mutuntawa da martabawa sama dake, ke kaÉ—aice MACE GUDA ÆŠAYA TILO dake mulkin birnin zuciyarsa, dan haka shiyasa nazo da Æ™oÆ™on barata duk da nasan KISHI KUMALLON MATA ba lallai ya bari zuciyarki ta amince da bukatata ba….. ”

Ai gaba daya daskarewa nayi awurin ina jina tamkar cikin mafarki wannan kuma wacce irin masifa ce take sake tunkaro ni? Sai yanzu na gane ta ashe itace wadda taketa bibiyar mijina babu dare babu rana yanzu kuma dan rashin kunya shine zata zo har gida ta ruÉ—eni da abin duniya ta shiga tsakanina da mijina, to ai ba abin duniya ba ko ita duniyar zata bani akan in siyar mata soyayyar mijina bana jin zata yi nasara domin nafi sonsa fiye da komai, kuma zan iya yadda in rasa komai da na mallaka dan kawai in cigaba da zama tare dashi,

“Maimunatu baki ce komai ba…..” inji kawarta Malika,

Ajiyar zuciya na sauke sannan na kallesu nace “duk naji abubuwan da kuka zo dasu sai dai ina so in tunatar daku abu daya da kuka manta, bani ke iko da zuciyarsa ba haka kuma ba nice zan zaba masa dukkan abinda yake so ba shiyasa sai nake ganin kamar zuwanku wurina baida wani alfanu tunda nidai bazan sa ba kuma bazan hana ba…. ”

” kamar baki fahimci abin da nake nufi ba…… ” inji Suhaila, hannu na É—aga mata alamar dakatarwa,

” ya isa haka dan Allah, idan har wannan ne ya kawoku to dan Allah kuna iya tashi ku tafi domin bazan taba fahimtarku ba….. ”

” nazo har gidan ki da bukatata amma kin wulakanta ni ba tare da kin san koni wacece ba, to shikenan zan nuna miki indai kudi da mulki suna siyan soyayya sai na siyi soyayyar mijinki…..

Mikewa tsaye nayi kamar yadda naga sun mike tana zubar da hawaye” wallahi karya kike, ko wacece ke baki isa kin siyi soyayyar mijina ba kuma mijina yafi karfinki……. ”

Bata sake tankawa ba kawarta ta jata suka fita tana kuka, suna fita Samha tana shigowa duk da bana wani sake mata amma hakan bai hanata shigowa ba a duk sanda taga damar hakan ta samu,

” widat wadanne bakine wadannan kika yi suka fita da kuka? ”

” nima ban san su ba, wani gida suke nema sai aka kwatanta musu nan….”

“ayya to ubangiji Allah ya rufa asiri”

“amin”

Sama sama nake amsa mata dan ni gaba daya zuciyata zafi take yi da zata taimaka min ma da ta kwashi kafafuwanta ta kara gaba dan bana bukatar wannan zaman nata, fahimtar hakan ina jin tayi shiyasa ta tashi ta tafi,

Nidai gaba daya na rasa abinda yake yimin dadi ji nake kamar idan yazo in bayyana masa amma wata zuciyar kuma tana cemin bai kamata in sanar dashi ba kawai in bar abin a raina ni daya, tunawa nayi da shawarwarin anty nan na danni zuciyata duk da abin yana damuna amma haka na daure na maida komai kamar ba komai ba, ganin yamma tana kokarin yi yasani fara dukkan aikace aikacen da na saba gabatarwa kafin ya dawo daga karshe nayi wanka na caba ado ina zaman jiransa. Koda ya dawo kokarin danne abinda ke raina nayi ban bari ya gane ba bare har yazo yana explaining, sakar masa fuska nayi da jiki muka sha soyayya kamar yadda muka saba sai dai fa lamarin suhaila sam yaki bacewa daga cikin zuciyata dan mutane yanzu ba abin yarda bane especially ma ita da har ALWASHI tayi akan mijina, daga karshe dai kin fadawa kowa nayi na barwa Allah yayi min maganin koma menene da kansa domin shine masani akan komai,

Kwana biyu dai baya samun zama yadda ya kamata saboda bikin abokinsa Ahmad da ya sako kai, yadda ahmad ya tsaya tsayin daka lokacin bikinmu shiyasa shima yanzu yake son ramawa kura aniyarta dan shine a sahun gaba akan komai, kasancewar a Kano za ayi bikin shiyasa da satin bikin yazo muka tattara muka tafi amma wannan karon agidanmu muka sauka kuma tare zamu dawo ranar da za a raka amarya, wannan zuwan banyi yawo ba sosai dan wasu ma basu san nazo ba gidan ƙawalli kawai na leka naga Irfan sai ko gidanmu da naje shima ban ko wuni ba, daga nan na dan shiga kasuwa itama sama sama, nayi attending duka events din kuma tun anan muka yi sabo da amaryar mai suna Nihal haka koda aka rakota Abuja ni na zauna tare da ita har zuwa lokacin da angwaye suka karaso sannan muka yi musu sallama muka tafi, tun muna hanya yake cemin wai yau bikin Ahmad ya tuna masa namu bikin muma,

“me ka tuna daga ciki?” na bukata ina kwanciya a gefen jikinshi,

“everything baby….. Babu abinda na manta”

“wow…..” na fada cikin tsokana, “ke baki tuna komai ba”

‘na tuna mana… ”

” me kika tuna? ”

” ranar dinner….. ”

Dariya yayi ya ja hancina saboda ya san tunda na fadi haka to kuma tsokanace zata biyo baya, har muka je gida maganar muke yi,

A falo na barshi suna waya da mommy nikuma na wuce bedroom waist bit din da na siyo na É—aura da niyyar burgeshi dama normal one din na siya ba mai hadi ba kamar yadda naji masu siyarwar suna tambayata lokacin da naje siya wai mai hadi ko marar hadi nace marar hadi dan bana son garin burge miji inje kuma in sabawa Mahalicci na, riga na saka iya cibiya da mini skirt wadda mazaunai na kadai ta rufe na fito, ai tun yana wayar da ya hango ni daga nesa naga ya tashi zaune daga kishingiden da yake yana miko min hannu amma sai na makale kafada naki zuwa, nafi son har sai ya gama yadda zamu fi sakewa da juna amma yanzu idan na kusanceshi ai akwai matsala, kasa hakuri yayi yace ma mommy bari yana zuwa zai kirata back ya ajiye wayar ya juyo yana kallona sosai,

“zo mana baby….” a hankali nake takowa zuwa inda yake, ina karasowa ya damÆ™i waist dina yana cewa,

“baby what’s this?”

“kwalliya nayi maka”

“I see, yayi kyau saura nan…..” ya fada yana taÉ“a cibiyata,

“kana so?”

“yes baby…..”

Tunda ya samu jigidar nan ai ya samu abin yi lallai ada nayi sake da ban saka tunda wuri ba sai yanzu ashe bawan Allah yana so kuma yana ra’ayi kuma da yake mai different colors na saka sai hakan yafi daukar hankalinsa tunda na gane haka nima yanzu sai na daina saka kayan da zasu rufe ta, koda yaushe kananun riguna nake sakawa iya cibiya inyita juyi yana kallo na wani lokacin ma har a bani tukwici.
*** *** ***

Shalele shine sunan da kowa na gidan ke kiranta dashi saboda tsabar shagwaba da gata kasancewarta mace guda daya a cikin gidan, duk sauran yan uwanta maza ne sannan kuma itace yar auta, wannan dalilin yasa kowa ya tashi abu Shalele duk wata kulawa tana samu gashi ta fito daga tsatson mulki da masu gidan rana saboda mahaifinta mai fada aji ne ne gaba da baya, duk abinda take so shi ake yi mata haka wanda bata so kuma an barshi har abada. Cikakken sunanta Suhaila Umar Lemu, mahaifinta ɗaya daga cikin ƙososhin gwamnatin tarayya ne suna zaune garin Abuja amma asalinsu yan jihar Bauchi ne,

Tana kan hanyarta ta zuwa airport da sanyin safiyar Laraba idanuwanta suka yi tozali gami da arba da samz wanda ke hanyarsa ta zuwa office, masha Allah kawai take furtawa acikin ranta saboda tsabar haduwarsa komai nashi yaja hankalinta nan tayi ta binsa har zuwa office É—in su,

Parking tayi ta kira daya daga cikin securities din office din, karon farko wasu sabbin kudi yan dubu ta zaro guda goma ciss ta mika kafin ta fara tambayarsa,

“dan Allah taimako zaka yimin, naga wani guy baÆ™i giant ya shiga nan yanzu shi nake so ka bani phone no dinsa….”

Dan jimm security din yayi kafin yace “ehh madam na gane shi amma sai dai bani da no dinsa….”

“babu matsala na baka assignment kaje ka nemo min komai da ya shafe shi please and am going to pay….”

“ok ma, i shall…”

Exchanging contacts suka yi sannan ta juya kan motarta ta fita tana jan dan siririn tsaki sakamakon kiran da Jalil keta faman yi mata dan ya jima da sauka………..

*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*

_*Ummi Shatu*_

Post a Comment

0 Comments