Garin Dadi 55

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Garin Dadi 55


{55}

 

*Ina kuke manyan mata Æ´an Æ™walisa ma’abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haÉ—aÉ—É—un Lagos lace wanda zaku iya samun É—inkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaÉ“inki, gefe É—aya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUÆŠI GIDA…..*

~~~Ina haÉ—a kayana ina share hawayen da yake sauka kan kuncina a haka ya shigo ya sameni wanda dawowarsa kenan daga masallaci tun bayan da ya fita sallar asubah, tsayawa yayi yana kallona kafin naji yace,

“wannan kayan fa??”

“Kano zanje…” na bashi amsa ba tare da na kalleshi ba,

“yaushe kika dawo daga Kanon da har zaki sake komawa? Ko wani abu ya faru a gida?”

Dakatawa nayi daga abinda nake yi dama tuni hawaye sun wanke min fuska ga wasu sabbi suna zarya da sintiri bisa kuncina,

“Babu abinda ya faru a gida, kawai naga kamar ka gaji da zama dani ne shiyasa zan bar maka gidan dan wannan kora da halin da kake yimin ya isa haka….. Yau 3 days baka kulani baka yimin magana”

Zama yayi kusa dani yajani jikinsa ya rungume ai kamar jira dama nake take na fashe da kuka,

“baby Kin bata min rai ne da yawa, ta yaya wata zata zo ta fada miki magana akaina and you start misbehaving instead of you to explain everything to me….. Am very sorry ni ban gaji da zama dake ba, shikenan ya wuce, don’t go anywhere please….. Kinga idan kika tafi gida relatives dinki zasu iya rabani dake suce ba zaki dawo ba tunda bana kulawa dake ina takura miki, am soo sorry please, forgive me ”
Har lokacin ban daina kukan da nake yi ba na shagwaba tabbas abinda ya fada gaskiya ne banyi aiki da hankali ba bare tunani bayan ya bani dukkan dama kowacce iri da zan zauna inyi magana dashi amma maimakon haka sai kishi ya rufe min idanu kawai na hau dokin zuciya naƙi yarda muyi magana ta fahimta kuma na fuskanci hakan shine ya bata masa rai fiye da maganganun da na fada,

“stop crying baby, kiyi hakuri”

Kai na daga masa amma har lokacin kukan nake yi haka yaci gaba da rarrashi na har nayi shiru daga karshe shine ya dauki kayan ya mayar dasu inda na ciro su ya sake dawowa wurina ya kama hannuwana ya rike yana kallona.
***

Tun bayan da suka bar wurin samz suke faman tunanin abin yi ko kuma hanyar da za su bullowa lamarin amma sun gagara samun mafita domin sun jarraba duk wata hanya da dabara wurin ganin ya amshi tayin soyayyar da Shalele tayi masa amma abin ya faskara ko kuma yaci tura,

Idanuwanta jajur take kallon Malika ranta kuma a cunkushe,

“Malika na rasa yadda zanyi….. Baki da wata dabara ne wadda kike ganin idan munbi watakila in samu karbuwa awurinsa?”

“Hmmmm sai yanzu hankalina ya kai kan wata dabara wadda tun afarko ita ya kamata ace mun fara bi kuma ta yuyu da tuni yanzu wani zancen ake yi ba wannan ba Shalele amma sai dai ban san yanda zaki karÉ“i maganar ba….”

“yaya kuwa zan karbeta matsawar burina zai kai ga cika?”

Gyara zama Malika tayi kafin tayi kasa kasa da murya kamar tana gudun kada wani yajisu,

“Tunda munyi duk iyakar kokarinmu mun kasa shawo kansa mun gwada duk wata dabara tamu amma abun ya faskara to yanzu ina ganin Lokaci yayi da zamu juya tunaninsa, lokaci yayi da zamu mallakeshi ta wata hanyar koda kuwa baya so kuma koda hakan na nufin wata zata rasa shi ke kuma zaki mallakeshi….. ”

” am Malika ban fahimceki ba, ban fahimci abinda kike nufi ba…. ” Shalele ta bukata cikin rashin fahimta,

” ina nufin zamu je mu hadashi da malamai….. ”

ÆŠan shiru Shalele tayi kamar wadda take nazarin maganar da ta fada kafin ta dubeta tace,

” amma kina ganin hakan babu matsala? Nifa bana son kauce hanya akan abin duniya, kar kaje ka rasa lahirarka akan duniya ”

” Haba Haba, haba Shalele ke kanki kin san ai bazan yi haka ba, tayaya zanje wurin wadanda suke shirka, wannan fa kawai normal malami ne zamu je mu nemi taimako ya taya mu da addu’a kan Allah ya karkato da hankalin wannan bawan Allahn zuwa gareki, ai ko a cikin musulunci sunna ce ta rayuwa ka nemi dan uwanka ya tayaka da addu’a akan wata bukata taka ko wani buri naka, to mu dinma hakan zamuyi…. ”
Jin abinda Malika tace sai ta dan yamutsa fuska tayi murmushi tace,

“to shikenan hakane kuma na fahimceki yanzu yaushe kike ganin yadace muje?”

“wa? Ai da zafi zafi ake dukan karfe hajiya, a yanzu ba sai anjima ba zamuje ayi duk abinda yadace”

“kema kin san hajiya ba zata taba barina in fita yanzu ba”

“to ai babu matsala ni ba sai in wakilceki ba? Ni sai inje inyi masa bayanin dukkan damuwarki da bukatarki da kuma abinda muke so ya rokar mana….”

“shikenan hakan yayi, nagode Æ™awata, Allah yabar mu tare yabar zumunci”

“amin, ai babu komai kawata kema kin san Kinfi karfin haka awurina kuma zan iya yin komai dan ganin kin samu farin ciki kin samu abinda kike so, yanzu me kike ganin zamu bashi domin sadaka tunda kin san aikin ki babban aikine kawata amma babu matsala kome kika bashi baki fadi ba saboda zaki samu biyan bukata ”

Tsamm Shalele tayi ta tsaya tana kallon ta kafin tace” Malika wai yaushe kika san malamai ne da har kike ta rattabo jawabi a kansu haka? ”

” wallahi bawai sanin su nayi ba, kin san anty Rabi’a kanwar maman mu wadda ta jima bata haihu dinnan ba to itace fa aka hada ta da shi taje ta bukaci ya taimaka mata da addu’a kuma yana yimata ko shekara ba ayiba ta samu ciki yanzu kinga yaran ta biyar…. Ajere a jere ”

” masha Allah, to me zan bashi matsayin sadaka…. ”

” ni ina ganin kar muyi approaching dinshi da kudi, mu bashi abinda idan ya gani zai dage ya mayar da hankali yayi mana aiki ”

” kamar me kenan? ”

” Gold…… A cikin gold dinki ki bada guda daya akai masa ”

” kai Malika, gold fa kika ce, so kike hajiya tayi bandata”

“Ranar biyan bukata wallahi rai ba a bakin komai yake ba, ni da ace nice idan har bukatata zata biya to ko rayuwata ce zan iya badawa, haba Shalele ni sai nake ganin kamar baki damu da ki mallaki wannan guy dinba, kamar duk abubuwan da kike fada a kansa karya ne, kamar duk girman son da kike ikirarin kinayi duk wasa ne…. ”

” kema kanki kin san ina sonsa kuma ina son in mallakeshi… ”

” to idan kuwa hakane sai ki shirya rasa komai dan mallakarsa ciki kuwa har da abubuwan da kika mallaka masu tsada ”

” hakane, to yanzu wanne zan baki daga ciki?”

“acikin bangles dinki ki bada koda guda biyu ne mukai masa mu gani”

“ok tom ina zuwa”

Da ga haka ta nufi wurin tangamemiyar wardrobe É—in ta bayan ta bude ta dauko wani dan karamin box wanda saida ta saka wasu pin kafin ya bude, nan ta ciro awarwaraye daka daka kirar India sai sheki suke da daukar ido, guda shida ne iri daya sai wasu suma guda shidan daban kirar Dubai, guda biyu ta debo da ciki ta mayar akwatin ta rufe ta sakashi cikin ma’adanarshi ta rufe ta dawo wurin Malika wacce ke zaune tana latsa wayar ta,

“kawata gashi….. Wannan ai sunyi ko?”

“ehh to sai dai naje sannan zanji daga gareshi, kin san kamar yadda na fada miki tun farko aikin naki babba ne na san sai anyi yanka an zubar da jinin shanu ko rakuma dan ayi sadaka banda sauran abubuwa, babu damuwa dai kuma na san Insha Allah ba zata gagara ba, amma fa maganar nan ta zama sirri tsakaninmu kawata karki yi gangancin fadawa kowa ciki harda hajiya dan aiki zai iya lalacewa ”

” hauka nake zan fadawa hajiya?? Hajiya taji na bada bangles dinnan ai na shiga uku…..Allah dai yasa mu dace ”

” Insha Allah, Insha Allah zamu dace kuma zaki ce na fada miki, bari ma ki gani in tashi inje”

“to shikenan nagode kawata, duk yadda ake ciki zamuyi waya”

Tare suka fita ta rakata har harabar gidan wanda yake makeke sannan tangamemen gaske, samarin gidan suna nan sai buga kwallon kwando suke yi tare da abokansu gefe daya kuma wasu suna buga table tennis, ita dai Malika yau ko hajiya bata shiga ta yiwa sallama ba gudun kada hajiyan ta gane. Ita kuwa shalele bayan ta raka Malika shiga cikin su Jalil tayi suka cigaba da buga table tennis domin ta iya sosai kuma ta kware a wannan fannin, wasan da ya kaisu har magriba kafin su shiga cikin gida, koda wasa bata sanar da hajiya abinda ya faru ba duk da kuwa hajiyan nata tambayarta yaushe Malika ta tafi bata yi mata sallama ba? Yadda Malikan ta gargadeta akan ta iya bakinta haka tayi koda wasa bata sanarwa da kowa ba,

Da daddare tana shirin kwanciya bacci taji kiran Malika cikin zakuwa da son jin abinda ke tafiya ta dauki wayar,

“kawata ya ake ciki ne?”

“alhamdulillah, albishirinki…”

“goro….” ta fada cikin shagwaba tana kokarin kwanciya,

“mun gama da matsalar ki Insha Allah domin malam ya bani tabbacin insha Allah wannan guy din zai kiraki da kansa daga nan zuwa gobe, idan kuma har hakan bata faru ba zuwa 1 week malam yace in sake komawa zai sake sabon wani aikin na musamman”

Hamadala shalele tayi kafin ta sake gyara kwanciyar ta cikin tsantsar farin ciki,

“Alhamdulillah…. Kai gaskiya amma naji dadin jin wannan labarin kawata, yanzu kenan in jira call dinsa?”

“Enhem…..”

“thank you soo much kawata, Allah yabar zumuncinmu”

“amin kawata, don’t mention it”

Sallama suka yi ta katse wayar ai tun daga wannan lokaci ta fara zaman jiran kiran samz amma har karfe 1 na dare shuru daga karshe ma bata san lokacin da bacci ya dauketa ba,

Washe gari tana farkawa da wayarta ta fara dan itace abu na farko da ta fara janyowa ta duba wai ko zata ga miss calls dinsa amma babu ko daya haka ta sauka daga kan gadon duk ranta babu dadi ta shiga bathroom, gaba daya a yan kwanakin wuni take da waya atare da ita tana jiran kiran samz amma ko alamun hakan babu, idan ta kira Malika tayi mata complain sai tace ta kara hakuri kuma kar ta sake ta kirashi ko ta tura masa text malam yace da kansa zai nemeta a haka har kwana bakwai din ta cika nan Malika ta sake dawowa,

“Gaskiya na fara sarewa da lamarin nan Malika…. Anya kuwa kina ganin guy dinnan zan samu kansa?”

“ki kwantar da hankalinki kawata zaki samo kansa very soon kawai dai muci gaba da bin umarnin malam, dama yace idan 7 days tayi bai nemeki ba to in sake komawa kuma yanzun nan zan koma”

“yawwa dan Allah tashi ki koma maza maza, faka faka kawata….”

“akwai bukatar mu sake kai masa wani abu hakan kadai zai sa yayi mana aikin da yadace”

“me kuma zamu sake kai masa Malika?”

“Gold, matsawar kina son burin ki ya cika to fa yazama wajibi ki bude hannuwanki shalele….”

Shiru shalele tayi ta gagara koda motsi bata son ta rasa hanyar mallakar samz haka kuma bata son tayi abinda daga baya zata zo tana cizan yatsa dan idan hajiya ta gane abinda suke kullawa a bayan fage tabbas kashin ta yagama bushewa……

 

*Sakkwatawa, zamfarawa, mazauna Kebbi kuna ina? Wannan garabasar taku ce kuyi maza maza ku garzayo ku kwashi garabasar kayayyaki cikin farashi mai sauƙi, siyan daya ko sari, dan more wannan garabasar masa ku garzaya ku shiga wannan link domin kasancewa cikin gidan sauki*

https://chat.whatsapp.com/E5Q6ce8rZhY25J32dauHRu

_*Ummi Shatu*_

Post a Comment

0 Comments