Garin Dadi 56

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Garin Dadi 56


{56}

*Ina kuke manyan mata Æ´an Æ™walisa ma’abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haÉ—aÉ—É—un Lagos lace wanda zaku iya samun É—inkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaÉ“inki, gefe É—aya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUÆŠI GIDA…..*

~~~Rasa yanda zatayi tayi dan gaba daya ta zama confused, ta san duk abinda Malika ta fada gaskiyane idan har tana son samz dagaske sannan tana son ta mallakeshi to ya zama dole ta iya hakurin rasa komai, ya zama wajibi ta shirya salwantar da duk wani abu wanda ta mallaka kamar yadda Malika ta faɗa, to amma gefe ɗaya tana ji acikin zuciyarta kamar bata kyauta ba kuma idan har hajiya ta san wannan labarin to mai rabasu sai Allah sai dai da yake abinda zuciya ke so nan ta yakice wannan tunanin a ranta kawai ta tashi taje ta sake debo bangles wannan karon guda hudu Malika ta karɓa sannan tayi mata sallama ta tafi tana sake jaddada mata cewa ta jira result mai kyau.
***

“Baby kiyi hakuri amma bana son ki sake repeating irin wannan laifin da kika yimin Kinji?” naji ya fada yana kallon fuskata yayin da hannuwana ke cikin nasa, kai na daga masa kuma har lokacin ban daina zubar da hawaye ba,

“ki daina kuka…. Ai ya wuce, mun shirya yanzu….”

Harararsa nayi cikin nuna so da kauna nace “ka bani wahala….”

“am very sorry my love, come here, zo muyi bacci” duk da na san ba baccin bane amma haka na biye masa nan muka fada duniyar ma’aurata wanda kowannenmu ya nuna bajinta karshe wurin samarwa da dan uwansa farin ciki,

Kasancewar zai je office a gurguje na shiga kitchen duk da yana cewa in bari kawai idan yaje office zai yi breakfast amma nace lalalalah nice nan zan hada masa ko yaci ko ya tafi dashi duk wanda yayi masa sai ya zaba aciki,

Ba wani abu mai wahala na yiba saboda lokaci ya tafi bread kadai nayi toasting bayan na soya ƙwai sai na dama custard, lokacin da na dauko kayan na fito daga cikin kitchen har ya fito falo yana kokarin balle botiran gaban rigarshi Kasancewar suit ya saka, ajiye kayan nayi na karasa gabansa ina balle masa gaba daya ya cika falon da kamshinsa,

“kin sa na makara baby” ya fada yana riko waist dina tare da shafa waist bits din dake daure kuguna,

“am very sorry, yanzu zaka tafi ai…. Zo kayi breakfast”

Kamar wani karamin yaro haka nayita cuccusa masa har ya koshi sannan na rakashi ya tafi bayan na sumbaci goshinsa da lips dinsa, ciki na koma ina jin a yanzu bani da wata sauran damuwa kuma. Ko 30 minutes bai fi ba da tafiya ya kirani video call, narke murya nayi na shagwabe nace,

“dama kuwa kamar ka san yanzu nake cewa zan kiraka in tambayi izinin fita….”

“ina zaki je?”

“kasuwa, ina son inje in iyo cefane in zo inyi maka girki”

“bana son ki fita baby, ki dafa min abinda yake available wanda kike bukata kuma babu just text me sai in taho miki dashi”

“ni dai dan Allah A’a, dan Allah ka barni inje in siyo wallahi bazan jima ba yanzu zan dawo”

“baby idan kika fita maza kallonki suke wasu ma tunani zasuyi ko baki da aure su fara sonki”

“wallahi zan saka mask in rufe fuska ta kuma shigar matan aure zanyi”

“ok to ki shirya in gani idan kinyi kyau da yawa you are not going anywhere”

Tashi nayi ina dariya na shirya cikin bakar doguwar riga na saka hijabi dogo sannan na saka face maks amma duk da haka rigima ya tayar da kyar na lallabashi ya yarda ya barni bayan ya kakkafa min dokoki nace ehh duk na yarda, kudin cefanen ya turo min dashi duk da nace masa da akwai amma sai da naga alert dinshi, rufe gidan nayi na fita. Kamar yadda na daukar masa alkawari iya abinda ya kai ni kadai nayi na dawo gida amma fa duk da haka nasha kira a waya sai kace wadda zata É“ata har sai da nace masa gani a gida na dawo sannan ya hakura ya tsagaita min da wannan kiran,

Kitchen na shiga na dora mana girki domin harma naso in makara, couscous da vegetables soup nayi sai fattoush salad A’a na hada gefe daya kuma na hada coconut milk shake, ina cikin aikin ban kai ga karasawa ba ya dawo, da gudu na tafi na tareshi tare da É—aleshi kamar zamu fadi, rikeni yayi gam yana shakar kamshin da jikina keyi dama sanye nake cikin wata farar riga armless amma na danyi kwalliya harda sarka da dan kunne nasa,

“baby kina wannan kamshin kika fita?”

“A’a boo, dazun nan fa nayi wanka na shafa turaren saboda kai…”

“thank you baby, I love you”

“love you too” Tare muka karasa girkin muka baje a falo muka ci, kamar yadda muka saba maraja’ar karatun da muka saba yi muka yi, wanda kuma bai gama fahimta ba na Æ™ara masa haske, bayan duk mun kammala na dube shi cikin taushin murya nace,

“sweet nazo da wata bukata amma ban sani ba ko zaka amince”

“baby dan Allah ki kwantar da hankalinki, baki da magana koda yaushe sai maganar ciki, dan Allah ki daina damun kanki Allah yana sane damu bai manta damu ba kuma zai bamu a lokacin da ya dace”

Murmushi nayi saboda jin abin da yace saboda shi duk tunaninshi maganar ciki zanyi kamar yadda na saba ko kuma maganar zuwa ganin Dr sai dai a wannan karon ba haka bane,

“sweet what do you think?”

“baby ai na san duk maganarki bata wuce ta ciki…”

Kumatunsa na ja kafin na bashi amsa da “wannan karon to baka canki daidai ba, É—azu da na fita kasuwa naga wani abu da ya burgeni shine nace zanyi shawara da kai idan har ka amince sai nima inyi joining….”

Jana jikinsa yayi ya rungume kafin yace “what’s it baby?”

“ÆŠazu naga wani shago na snacks leemat delicacies, wallahi abun ya burgeni idan zaka barni zanyi joining classes É—inta har nima in zama expert a wannan fannin….”

Ina wasa da hannunshi dake cikin nawa naji yace,

“baby shine kadai bukatarki?” kai na daga masa,

“indai hakan zai saka ki cikin farin ciki zanyi miki, zan barki kiyi joining classes din”

Rungumeshi nayi kam kam ina kissing dinshi tako ina,

“baby duk murnar ce wannan? Please i need more….”

Dariya nayi na cigaba da sumbatarsa dama na san zai yi wahala yaki amincewa dan ban taba son abu ya nuna yana kin abinba, duk abinda nake so shima yana so. Tun a daren ranar na soma bibiyar shafinta na Instagram har na samu contact dinta,

Washe gari bayan ya fita office na kirata na fada mata duk abubuwan da nake son koya kama tun daga harkar snacks har kalolin abinci na zamani nan ta faÉ—a min abinda zan biya, muna gama waya da ita da ya kirani nake faÉ—a masa yadda muka yi da ita yace babu matsala, a ranar ya saka min kudin na tura mata tace nan da kwana biyu zamu fara.

Gaba ɗaya waɗannan kwanakin na zama busy banda lokacin zaman banza bare har in samu in shiga damuwa duk da wani lokacin ina tunawa da damuwar tawa amma a cikin 100% yanzu 80% ya ragu, wuni nake ina karance karancen abubuwan da take turo min sannan gefe ɗaya ina rubuta duk wani abu wanda yake da muhimmanci, sai dai fa duk da wannan tarin ayyukan da nake yi baisa nayi wasa ko sakaci da kulawa da mijina ba, bashi lokaci na nake sosai indai yana gida sai idan ya tafi office ne sannan nake mayar da hankali wurin koyon duk wasu abubuwa da nake buri amma da zarar ya dawo sai in hakura haka kuma da weekend bana ma ko bi ta kai dan a lokacinne muke kasancewa da juna sosai mu shaƙata mu shana. Wannan weekend din na shirya gwada irin abubuwan da na koya shiyasa yana bacci na tashi na shiga kitchen na hau aiki kafin ya tashi nayi duk abinda zanyi kuma babu laifi komai yayi yadda ake so,

Ina kokarin tubewa in shiga wanka ya tashi lokacin 12 ta É—an gota, hararata naga yayi kafin yace,

“shine kika gudu ko?”

“to ai naga kana baccine sweet”

“to gashi na tashi”

“Barka da tashi my love love…”

Dariya yayi tare da miko min hannunshi na kama, tare muka yi wankan muna cike da nishadi da farin ciki, shiryawa muka yi na kai shi falo ina ce masa,

“yau ga jagwalgwalo na kaci kaji”

“baby girkin ki yafi karfin jagwalgwalo….. You are special”

Haka yake ta zugani yana sake bani ƙwarin gwiwa kuma shine yasa na sake mayar da hankali sosai kan fannin girke girke, idan na ɗanyi abuna babu yawa daga ni sai shi sai makota da nake bawa wani lokacin sai in dora akan shafi na da na bude nima wato chefweedat wadda yanzu har na soma samun followers sosai musamman ma da leemat ta ɗan tallata ni,

Ranar da na gwada yin birthday cake nayi masa nayi decorating a jiki na rubuta Happy birthday sweet nayi snapping na ajiye ban dora ba har sai da ya dawo daga office,

“baby which birthday again? Yau nawa date?”

Dariya nayi nai kissing dinsa kafin nace “Nifa bawai ina nufin birthday dinka bane kawai dai nayi maka ne,

” awwwwn…. Wow… When your wife is a baker” ya fada yana kissing dina shima,

“to yanzu zamu yanka cake din ko sai nayi shower?”

“go and shower first”

“no” yace dani yana kamoni ina kokarin guduwa, duk da bana so dole tare muka yi wankan sannan muka zo muka yanka cake muna ciyar da junanmu, duk sai da na mikawa neighbors dina da yake yana da girma step biyu nayishi, a daren na É—ora akan Instagram ai fa wurin mutum biyar suka yimin dm akan suna so,

Kallon samz nayi dake kwance bayana yana kokarin rufe system dinshi,

“sweet kaga wasu wai na so….”

“su yi order kiyi musu mana”

“Nifa gaba daya banma san yanda tsarin yake ba”

“you can contact your tutor”

“to shikenan”

Washe gari na kira leemat ta sanar dani yadda duk take abubuwanta da price dinta da komai, nan nima na dan fara da kadan kadan wani lokacin sai ayi order biyu ko uku, komai tare dashi muke yi ko girki idan na koya sai muyi tare da weekend shiyasa yanzu bani da matsalar girki duk ranar da sarautata ta motsa sai in hakimce ince yau girkinsa zan ci bawan Allah babu musu sai yaje ya girka mana. Tun zuwan da nayi Kano har yau ban koma ba kuma bana jin zan koma har sai bikin Bishra wanda aka saka nan da 6 months, nida kawalli muke hirar dazu da ta kirani nan take fada min wai zata yaye Irfan cikin week dinnan dan watanshi 11 yanzu,

“Haba kawalli ki barshi ya cika 12 months mana”

“kawalli ba zaki gane bane, barshi dai a yayeshi yanzun, babanshi ma ai da rigima yaketa yi wai ba za a yayeshi yanzu ba kaza da kaza to yanzu dai ya hakura dasu Annie suka saka baki”

“kawalli kararshi kika kai gida?”

“ya bazan kai ba yana neman ya jika min aiki”

Dariya muka yi gaba daya kuma sai lokacin na fahimci ciki gareta shiyasa zata yaye Irfan din, koda muka yi sallama jugum nayi araina inata tunani gashi kawalli zata yi na biyu amma ni ko na farkon ban samu ba take na fara hawaye damuwata ta sake dawowa sabuwa na gaza aikin komai a gidan na zauna sukuku a haka ya dawo ya sameni…….

*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*

_*Ummi Shatu*_

Post a Comment

0 Comments