Garin Dadi 6

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

Garin Dadi 6


©️ *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*GARIN DAÆŠI……..!*

*_NA_*

*_UMMI A’ISHA_*

*Wattpad:ummishatu*

 

*6*

 

~~~Tagumi kawai ta rafka tana kallona batare da ta furta ko kalma É—aya ba har sai da na gama bata labarin komai sannan ta sauke ajiyar zuciya mai Æ™arfi ta janye tagumin da tayi ta kalleni fuskarta babu fara’a tace,

“maganar gaskiya widat banji daÉ—in wannan labarin naki ba sam….. Ta yaya za ki bari sheÉ—an yayi wasa da tunaninki, kinfa sani sarai cewar an yi miki miji sannan an bada ke, kin manta da maganar aurenku da yaya faisal ne? Wannan abun da kike yi kuskure ne kuma ya kamata ki farga, ko a shari’a babu kyau neman aure akan nema, tun wuri kiyi gaggawar fatattakar wannan mummunan lamarin tun kafin gida su sani nidai shine kawai shawararar da zan iya baki….. ”

” Æ™awalli da alama har yanzu baki fahimce ni ba…. Wallahi Allah shine shaida dama ban taÉ“a jin son yaya faisal acikin raina ba kuma kema kin sani saboda nasha faÉ—a miki, to yanzu Allah ya haÉ—ani da irin wanda nake so saboda ni dama na fi son na auri mutumin da ya kwanta min har cikin raina ba wai irin yaya faisal ba wanda daidai da rana É—aya ban taÉ“a jin sonsa ba…. ”

Jin abin da na faÉ—a ya sanya Maryam zuba min idanuwanta gaba É—aya tana kallona dan tama rasa abin da zata ce sai zuwa can tace dani,

” kiyi ta addu’a Æ™awalli…. Dama idan aure yazo sometimes irin haka na faruwa, shaiÉ—an sai yayita Æ™oÆ™arin shiga cikin lamarin dan ta wargaza komai yaga ba ayiba amma idan aka dage da addu’a sai kiga Allah ya daidaita komai….. Allah ya kyauta”

“amin Æ™awalli na gode, bari naje gida dan kofa wanka banyiba na fito dan na zo na sanar dake…”

Tare muka rankaya zuwa gidan mu har wurin 8 muna tare sai lokacin na rakata ta tafi bayan ta yi min gargaÉ—in wai kar na kuskura na bari yaya faisal ko gida su fahimci maganar nan, da to kawai na bita domin maganar gaskiya yaya faisal ya jima da fara fahimtar akwai abin da ke faruwa ina jin wannan dalilinne ma yasa ya É—an ja baya da kirana kuma da alama kamar fushi yayi dan yau kusan kwana shida kenan bai kirani a waya ba.

Zaune nake ina nazarin wani manual na na’ura mai Æ™waÆ™walwa bayan nayi shirin bacci cikin riga da wando masu santsi light blue, jin Æ™arar wayata ya sanya ni kallon agogon jikin wayar Æ™arfe 11:30 na dare abin da yayi mutuÆ™ar bani mamaki kenan saboda ganin kiran yaya faisal mutumin da ya shafe kusan wata bai nemeni ba nima ban nemeshi ba har yau É—innan da ya kirani, É—agawa nayi ina son jin da wacce yazo, cikin taushin murya naji sallamarsa nan na amsa bayan na kishingiÉ—a na kuma rufe jibgegen littafin dake gabana,

“widat a haÆ™iÆ™anin gaskiya na kasa gane abin da yake faruwa… Gaba É—aya kin sauya kuma kin canja daga yanda kike…. Dama da biyu kuma ina sane naÆ™i nemanki tsawon wannan lokacin saboda ina son gane gaskiyar abinda yake faruwa….. Widat meyasa kika daina so na? Nayi miki wani laifi ne ko kuma kinji wani mugun abu atare dani? ”

Shiru na É—anyi har sai da ya kira sunana dan tabbatar da cewa shin har yanzu ina kan layinne ko ta yanke, ajiyar zuciya nayi sannan cikin sanyin murya nace,

” yaya faisal duk abubuwan nan da ka faÉ—a babu ko É—aya aciki wanda ya faru, ni banji wani abu marar daÉ—i a kanka ba…. Kawai dai….” shiru nayi na kasa Æ™arasawa hakan yasa shi faÉ—in,

“ina jinki, ki faÉ—i duk abin da ke ranki widat kar kiji shakka….. Kawai dai me?”

Nauyin kalmar naji shiyasa na kasa faÉ—a, tayaya zance masa bana sonsa tun asali?

“yaya faisal a gaskiya dama tun can baya ni akwai wanda nake so kuma har yanzu muna tare dashi”

Shiru naji shima yayi na tsawon wasu mintuna kafin ya saki ajiyar zuciya,

“idan na fahimceki dai dama bakya so na har na turo gidanku? Anyway shikenan zan yi musu bayani yanda zasu fahimta, amma ki sani ni ina son ki kuma naso na rayu dake, da kin san irin girman sonki acikin zuciya ta da irin tanadin da nayi miki na kyakkyawar kulawa da Æ™auna wallahi widat da kin zaÉ“eni a matsayin miji amma babu matsala Allah ya cigaba da tabbatar mana da duk abin da yafi zama alkhairi, nagode saida safe…. ”

Ji nayi jikina yayi sanyi, sam banji daÉ—in yanayin da naji yaya faisal aciki ba wato yanayi na damuwa da É“acin rai amma babu yadda na iya saboda nima zuciya ta na can wani wuri daban, daren ranar sai da na jima banyi bacci ba kafin bacci É“arawo yayi nasarar É—aukata.

Washe gari ina tsaka da bacci naji muryar Annie tana tashina, da mamaki fal cikin zuciya ta na tashi saboda a iya sanina dai yau weekend ne bare ko ince saboda fita aiki take tashina dan kar in makara,

“zo abbanku yana kiran ki….” daga haka ta juya ta fita daga cikin É—akin, dogon hijabi na saka har Æ™asa akan kayan baccina na fita idanuwa cike fal da bacci sakamakon rashin isasshen baccin da ban samu ba jiya,

Ina shiga falon Abba na hangi mama zaune da yaya Abdul hakim kusa da ita sai Annie itama zaune ɗan nesa da abba kaɗan, ganin irin yanda naga fuskokinsu ya tabbatar min da cewa ba ƙalau ba musamman ma yaya Abdul hakim dake ta faman aikin watso min harara kamar zai tashi ya bugeni,

“abba ina kwana, mama ina kwana….”

“lafiya lau maimunatu…..” abba ya amsa yana zare farin gilashin dake idanuwansa, sunkuyar da kaina Æ™asa nayi saboda na fahimci ni mai laifi ce saboda yadda babu wanda ya amsa gaisuwa ta sai iya abba kaÉ—ai, tunani na ya katse sakamakon maganar abba da naji,

” maimunatu yaya kuka yi da faisal….?” tambayar da tayi mutuÆ™ar gigita tunani na da hankali na gaba É—aya dan ban san irin amsar da ya dace in bawa abba ba a wannan lokaci,

“maimunatu…..” abba ya sake kiran sunana, “na’am abba”

“nace yaya kuka yi da faisal? Ina son ji”

Shirun dai na sake yi saboda ban san abin da zance ba,

“abba ai bata da gaskiya dan haka babu abin da zata iya cewa, wulaÆ™anci ne da Æ™asÆ™anci ta gama yi wa faisal….. Ai ba zai yi mata Æ™arya ba, duk abin da ya faÉ—a hakane….” yaya Abdul hakim yafaÉ—a cikin fushi da É“acin rai,

“a’a ai akwai buÆ™atar muji daga bakin ta, gara ta faÉ—i koma menene da bakin ta”

“Mai shari’a babu batun aji daga bakin ta, mu muka haife ta ba ita ta haife mu ba, mu ne muke da iko da ita ba itace take da iko damu ba dan haka ya zama dole tayiwa dukkan dokar da muka shimfida biyayya, maganar auren ta da faisal ko tana so ko bata so sai an yi ta faÆ™at, idan kuwa bata amince ba to ta nemi wata uwar amma ba ni ba…. Nima ba ita kaÉ—ai na haifa ba bare baÆ™in cikin ta yayi ajali na ” Annie ta faÉ—a cikin fushi ta tashi ta fita, hawaye ne suka shiga wanke min kumatu babu Æ™aƙƙautawa take naji tsanar yaya faisal tsana mai tsanani domin ta dalilinsa gashi zan samu matsala da gidan mu a karo na farko cikin tarihin rayuwa ta, Karon farko da mahaifiyata tayi fushi dani tare da alwashin mummunan sakamako a gare ni, kifewa nayi awurin ina gunjin kuka wiwi.

Tsawar da yaya Abdul hakim ya daka min itace tayi sanadiyyar haÉ—iye kuka na,

“ke…. Idan baki yi wa mutane shiru ba sai na zo nayi ball dake, marar kunya, ana ganin ki kamar me hankali ashe ba haka bane…….”

Jin an ɗagoni yasanya ni ɗagowa ina kallon mama wadda ta riƙoni ta sani cikin jikin ta tana rarrashi, sai lokacin naji abba yayi gyaran murya alamar zai yi magana kuma maganar mai muhimmanci,

” maimunatu……. Kiyi haÆ™uri zan aura miki faisal wannan shine hukuncin da na yanke…..”

Jin abinda kunnuwa suka jiye min take na nemi jina da ganina na rasa na zama nidai gani nan ne dai kawai nakasa gane a wanne irin yanayi nake……….. ✍

*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*

*_Ummi Shatu_*

Post a Comment

0 Comments