kawali Ne 10

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

kawali Ne 10


*KAWALINE*

*Zahra Surbajo*

 

*Bissimillahirrahmanirrahim*

*wannan littafi nawa na kuÉ—ine 500,yazo da salo na musamman acikinsa dagajin sunan kuma kun san zeyi maana,sannan na É—auko wani ciwo dake damun mu ahalin yanzu na kawalci,so duk meso ya turo kuÉ—insa 500,in siya zakiyi kifitarmin karku siya,Sannan suk wanda yasayi wannan littafin AJEE DOWN kyauta zekarantashi*

*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*

*07044600044*

*KUSHA LABARI HAUSA NOVELS tashace akan youtube wacce zaku samu complete ɗin littafin KAWALINE akai dama wasu sauran littattafan masu ƙayatarwa da nishaɗantarwa gaku masu sauraro kuhanzarta zuwa dan ɗebe kewarku,KUSHA LABARI HAUSA NOVELS ƊAYA TAMKAR GOMA*

https://www.youtube.com/@kushalabarihausatv

*10*

 

Raihan motsin arziƙi yakasa yi bare yay yunƙurin hanata tafiya,so yake yayi magana bakinsa ya masa nauyi,haka ya zubawa sarautar Allah ido har ta fice.

Runtse idanunsa yayi wasu hawaye masu zafi na biyo kumatunsa,tunda yake yaune karona farko daya sadu da virgin,dan duk kasuwancinsa da lalatattu yake kuma ba wanda ya É“ata ba sauran wasu,yau gashi ya keta budurwa cikakkiya akaro na farko.

Kanshi ya riƙe dake faman sara masa ,ƙarar wayartane yasa ya firgita yakai dubansa gurin.

Ɗauko wayar yayi ƙirar camon A33 numbar dake kira,ansa mamana akai,tsintar kanshi yayi da ɗaga kiran ba tare dayasan yayi hakanba.

Dagacan ko mamansu ce ta fara magana da cewa”Rayhana ina kika shige har yamma baki dawo ba wlh duk atsoracs nake kar ki gujeni kamar Æ´ar uwarki siyama,”

Sosai yasake samun tabbaci kan cewa suÉ—in tagwayene,amma dan ya Æ™ara gamsuwa sai yace mata “ba ita bace ta yar da wayarne na tsinta”

“Iko se Allah É—an samari kataimakemu ka faÉ—i inda kake in ta dawo seta zo ta amsa”cewar mamam bakinta har rawa yake.

“ki faÉ—amin ku inda kuke se in kawo muku ni baÆ™one anan É—in”cewar rayhan asanyaye.

“Allah yamaka albarka yaro kaji,muna kaita,dakazo katambayi gidan liman babba marigayi zaa kawoka mungode yaro”cewar mama jikinta se É“ari yakemata.

kashe wayar yayi yabi screen É—in da kallo,hotunansu su biyun ne akan wayar sosai yake mamakin abun seyake ganin abun kamar almara.

Miƙewa yayi da ƙyar ya shiga yay wanka sannan yazo ya maida kayan jikinsa,ya ɗauki wayar tata ya fice zuwa mota saida ya shiga ta cika da mamakin banin ledar jijaban data ɗinko ma na cikin motar.

Shuru yayi yaja motar ya ɗauki hanyar takai zuciyarsa cike da saƙe saƙe.

**********

Itako mamansu tunda taji zancan an tsinci wayar rayhana hankalinta ya tashi fatanta Allah dawo da ita lafiya dan jikinta yafi bata ba lafiya lau ba.

Rayhana ko tunda ta fita agidan na rayhan tsoron tafiya ma take a mota koda ta hayace shiyasa bata hau motar ba taita tafiya aƙasa tana kuka gamida sharar majina.

Tayi tafiya me tsayi sannan ta saurari abun hawa ta hau ba tare da tana dako sisiba.

Shiko rayhan tuni ya isa gidan nasu,inda yasha mamakin ganin irin ruɓaɓen gidan da suke rayuwa aciki.

Har cikin gida mama tai masa ison shigowa,ba musu ya shiga ta shiɓfiɗa masa darduma ya zauna.

Bayam sun sake gaisuwar ne mamansu tace”bawam Allah ina kasamu waya da hijabanta”

“Mama a shagom abokina ta mance dashi telane shine da kika kira nazo kawo mata”cewar rayhan kanshi aÆ™asa.

Mama bin jikinshi tayi da kallo baki buɗe ko kaɗan beyi kala ma da masu gwagwarmaya akasuwa ba,yafi kala da masu rayuwa a ƙanƙara.

Nisawa tayi tace “to angode yaro Allah sa agama da duniya lafiya”cewar inna tana murmushi.

Shigowar rayhana yarkace yarkace tana kukane ya katse hirar tasu.

turus taja ta tsaya ganin rayhan agidan nasu,a gigice inna ta kamota ta riƙeta ganin hijabin jikinta da jini sosai ta tsorata dan tasan ba lokacin period ɗinta bane.

“me yasameki rayhana,wannan jinin na menene?”cewar inna afirgice.

Rayhan ƙasa yay da kanshi tausayin uwar da ƴar na azabtar da zuciyarshi wasu hawaye masu zafi nabin idonsa.

“mama wannan baÆ™in karan danazo nasameki dashi shine yayimin fyaÉ—e,bisa laifin da siyama tai masa”cewar rayhana cikin matsanancin kuka.

Luuuu mama tayi ta faɗi ƙasa,abunka dame hawan jini tuni alamun shanyewar ɓarin jiki ya bayyana atare da ita,ga kumfa dake futo mata a baki.

Dagashi har rayhanar da gudu sukai kanta,rayhana na jijjigata tana kiran sunan ta.

COMPLETE ÆŠINSA NAKAN YOUTUBE KUJE KU SAURARA AKAN KUSHA LABARI TV,GA LINK CAN ASAMA.

*500 kacal zaku biya kusha karatu karku bari abaku labari*

Surbajo for life.

Post a Comment

0 Comments