kawali Ne 16

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

kawali Ne 16


*KAWALINE*

*Zahra Surbajo*

 

*Bissimillahirrahmanirrahim*

*wannan littafi nawa na kuÉ—ine 500,yazo da salo na musamman acikinsa dagajin sunan kuma kun san zeyi maana,sannan na É—auko wani ciwo dake damun mu ahalin yanzu na kawalci,so duk meso ya turo kuÉ—insa 500,in siya zakiyi kifitarmin karku siya,Sannan suk wanda yasayi wannan littafin AJEE DOWN kyauta zekarantashi*

*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*

*07044600044*

*KUSHA LABARI HAUSA NOVELS tashace akan youtube wacce zaku samu complete ɗin littafin KAWALINE akai dama wasu sauran littattafan masu ƙayatarwa da nishaɗantarwa gaku masu sauraro kuhanzarta zuwa dan ɗebe kewarku,KUSHA LABARI HAUSA NOVELS ƊAYA TAMKAR GOMA*

https://www.youtube.com/@kushalabarihausatv

*16*

 

Rayhana ta isa abuja cikin ƙoshin lafiya,inda tasamu kawun nata yazo ɗaukarta a jabi garage.

Koda yayi arba da ita da ciki a gaba kamar wacce zata haihu yanzu kukane ya kubce masa,dan farin sani yasan rayhana me tarbiyyace amma ga iftilain daya afka mata.

Itama hawaye take haka suka shiga taxi zuwa inda yake ayki,a mota suka gaisa daga haka ba wanda yasake cewa komai.

Koda rayhana taga katafaren gidan da zasu shiga cogewa tayi awaje takai dubanta gun kawun nata tace asanyaye”kawu nan gidanfa?”

Murmushi yayi yace”kinsan de ba yadda zaayi na mallaki wannan na baroku a Æ™auye kuna wahala,to nan gidan da nake gadi ne,ba nawa bane”ya bata amsar fuskarsa É—auke da murmushi.

Sunkuyar dakai tayi ƙasa tana muemushi,suka shiga cikin gidan.

Tsabar kyau da haɗuwar gidanne yasa rayhana kasa ɗaga ƙafarta har saida kawu ya taɓota tai firgigit ta bishi abaya.

É“angarenshi yamata masauki dan selfcontain ne,sosai gun yamata kyau,kan kujera ta zauna ta sauke ajiyar zuciya.

“ki zauna anan rayhana ni zan koma É—akin maigadi na bakin Æ™ofar shigowa, masu gidan na faÉ—a musu a Æ™auye kike kinzo nan ki haihune ki koma nasan baki da rawar kai dan Allah ki Æ™ara kiyayewa,”cewar kawu atausashe.

“insha Allahu kawu zan kiyaye.” ta faÉ—i atausashe.

Daga haka sallag ta fara yi sannan ya bata abinci taci tai godiya ga Allah sannan ta kimtsa É—akin da yake amatsayin mallakinta a halin yanzu.

********

Siyama jitayi gaba É—aya duniyar tai mata zafi,ta rasa inda zatasa kanta taji daÉ—i,ga wata irin mahaukaciyar soyayyar rayhan dakw É—awainiya da zuciyarta.hakanne yasa ta haÉ—a yanata yanata ta diro nigeria,cike da kunyar haÉ—uwa da innarta da rayhana.

Direct daga airport drop É—in mota ta É—auka zuwa garinsu cikin shigar badda kama ta yadda bame ganeta.

mama tasamu a tsakar gida tana wanke wanke bakinta É—auke da sallama ta shiga gidan.

Daga muryarta mama ta gane siyamace, jikinta har É“ari yake ta miÆ™e tana faÉ—in”siyama kece?”ta fashe da kuka.

Itama kukan tasaka ta tafi da gudu suka rungume juna,kuka suke sosai cikin kukan siyama ke faÉ—in “inna ki yafemin don Allah na tuba bazan Æ™ara barin gida ba”

“Siyama koda kike can ban taÉ“a kwana dake azuciyata ba kullum nema miki shiriya nake gurin ubangijin daya jarabceni dake”cewar mama cikin kuka

Sun jima a haka kamin su saki juna su samu guri su zauna tashi mama tayi takawo mata abinci,siyama tace”mama rayhana da naga bangantaba ko kin ayketane?”

Kuka inna tasa daga nan ta kwashe duk abinda ya faru ta sanar da siyamar.

Yanke jiki siyama tayi ta faɗi jin cewar ƙanwarta na ɗauke da cikin wanda takeso da burin yazama mijinta.

 

*Ku hanzarta siya 500 ne kawai dan vama ayi komaiba awannan labari*

COMPLETE ÆŠINSA NAKAN YOUTUBE KUJE KU SAURARA AKAN KUSHA LABARI TV,GA LINK CAN ASAMA.

*500 kacal zaku biya kusha karatu karku bari abaku labari*

Surbajo for life.

Post a Comment

0 Comments