kawali Ne 17

Latest Posts

6/recent/ticker-posts

Ad Space

kawali Ne 17


*KAWALINE*

*Zahra Surbajo*

 

*Bissimillahirrahmanirrahim*

*wannan littafi nawa na kuÉ—ine 500,yazo da salo na musamman acikinsa dagajin sunan kuma kun san zeyi maana,sannan na É—auko wani ciwo dake damun mu ahalin yanzu na kawalci,so duk meso ya turo kuÉ—insa 500,in siya zakiyi kifitarmin karku siya,Sannan suk wanda yasayi wannan littafin AJEE DOWN kyauta zekarantashi*

*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*

*07044600044*

*KUSHA LABARI HAUSA NOVELS tashace akan youtube wacce zaku samu complete ɗin littafin KAWALINE akai dama wasu sauran littattafan masu ƙayatarwa da nishaɗantarwa gaku masu sauraro kuhanzarta zuwa dan ɗebe kewarku,KUSHA LABARI HAUSA NOVELS ƊAYA TAMKAR GOMA*

https://www.youtube.com/@kushalabarihausatv

*17*

 

Mama agigice take shafa mata ruwa afuskarta har ta dawo hayyacinta,ayki rungume maman tayi ra fashe da kuka.

Bata taɓa sani ko jin son satakewa rayhan yakai girman haka ba saida taji tanaso taga bayan cikin dake jikin ƴar uwartata dan samun damar mallakar masoyinta rayhan.

Daƙyar mama ta rarrasheta tai shuru dan ita da zatonta duk tausayin rayhanarne yasata suma da wannan kukan,batasan na tausayin kanta ba ne.

Miƙewa tayi jiki ba ƙwari ta shigar da kayanta ɗaki,sannan ta ƙarasawa inna wanke wanken,ta ɗora musu abinci.

A zuciyarta fana saƙa ta yadda zata ɓullowa lamarin dan ko mamace zata kawo mata cikas a cikar burinta na ganin ta auri rayhan zata iya taka mata burki.

*********

Rayhana acan abuja ko tana shiga gurin matar gidan wacce a haife ta haifeta mace me son mutane gashi faram faram take mata.

Yauma kamar kullum ta shigo falon na hajiya ta duÆ™a har Æ™asa ta gaidata sannan tace a ladabce”hajiya yau me zan tayaki dashi,a kitchen É—in?”.

Murmushi tayi ta dafa kanta tace”Allah miki albarka Æ´ata,yau zaÉ“inki zamuci agidannan,kinji ko,kidafa mana duk abinda ranki keso zamuci”

Murmushi tayi tai ƙasa da kai tana wasa da hannunta,sannann ta miƙe ta nufi hanyar kitchen ɗin,tana tafiya daƙyar sakamakon kumburin da ƙafafunta sukai mata.

Idanun hajiyar ne ya sauka akan Æ™afafun tace”zonan rayhana”

Dawowa tayi da sauri ta duÆ™a agaban hajiyar”gani hajiya”

“Kina zuwa awo kuwa acan rayhana jifa duk yadda Æ™afafunki suka kumbure?”

Ƙasa tai da kanta sakamakon hawayen da suka taru a idonta tace a sanyaye”ban taÉ“a zuwa ba hajiya”

“Subuhanallahi kuna aykin me,to maza kije ki shirya kizo in kaiki da kaina wannan ay sakaci da lafiya ne”cewar hajiya lokacim data miÆ™e tai hanyar É—akinta.

Badan ranta nasoba taje ta shirya ta faÉ—awa kawunta ta dawo hajiya ta fito suka shiga mota direba yaja suka nufi asibiti.

Da ike private sukaje yasa baay mata faɗa sosaiba,anan ne ana mata scarning akaga twins zata haifa duk maza kuma suna cikin ƙoshin lafiya.

Hajiya murna take sosai da batun haihuwar tagwayen yayinda irako rayhana kuka take wanda hajiya ra jiɓanta dana kunya ne.

Duk abinda yadace akai mata sannan suka baro asibitin.

Koda suka dawo É“angaran hajiya suka sauka,bayan sun hutane hajiya tace”rayhana likita yace damuwace tai miki yawa hawan jini na barazanar kamaki,inaso kisani mutuwar aure ba a kanki aka fara ba da Æ™ananun shekaru,ki kwantar da hankalinki ki haihu lafiya na miki alÆ™awarin riÆ™e miki Æ´aÆ´anki ki koma karatu ke kuma inde zaki iya zama dani”

Rasa bakin magana rayhana tayi godiya kawai takewa hajiyar tana kuka,hajiyar ta Æ™ara da cewa”kije ki kwaso kayanki ki dawo nan part É—in dan ancs adena barinki ke É—aya dan haka kidawo nan É—akin husna batanan yanzu taje germany raka Æ™anwata gun likitanta,zasu dawo next month”

Nanma godiya kawai ta iya yiwa hajiyar daga haka taje taiwa kawunta bayani kuma sosai yaji daÉ—i ta koma ta kwashe kayan nata ta koma part É—in na hajiya.

Tunda ta koma É“angaran hajiya take samun kulawa ta musamman tamkar tana gaban innarta,shiyasa in sukai waya da inna take bata labari.

Koda rayhana taji siyama ta dawo gida batai murna ba dan itace silar wannan mummunar ƙaddarar dake kanta.

Shiyasa ko awaya bata nemanta se in itace ra nemeta su gaisa shima sama sama.

 

 

*Ku hanzarta siya 500 ne kawai dan vama ayi komaiba awannan labari*

COMPLETE ÆŠINSA NAKAN YOUTUBE KUJE KU SAURARA AKAN KUSHA LABARI TV,GA LINK CAN ASAMA.

*500 kacal zaku biya kusha karatu karku bari abaku labari*

Surbajo for life.

Post a Comment

0 Comments